Monday, 11 July 2016

YA ZAMU KOYAWA 'YA'YAN MU SALLAH?



YA ZAMU KOYAWA 'YA'YAN MU SALLAH?
*************************************

'Ya ta Shekaranta 12 amma sallah ta zamar mata kamar wasu kaya a ka (domin duk yanda nayi da ita bata yin Sallah).

Wata Rana na Umurce ta da taje tayi Sallah. Na tsura mata ido har ta tafi taje ta dau sallaya ta shiga 'daki bata yi wani dogon dadewa ba ta fito a zuwan tayi sallah din amma ni na san bata yi sallar ba.

Na tambayeta ko ta gabatar da Sallar ta kuwa? Ta amsa min da "Eh", amma ni na san bata yi sallar ba. Cikin tsananin fushi na wanke ta da mari har sai da ta kife a kasa.

Daga baya kuma sai tausayin ta ya kamani, amma ba yanda zanyi domin saboda na gaji da halinta (na rashin yin Sallah). Nayi nadamar marinta da nayi na dauki alkawarin ba zan kara marin ta haka ba.Domin na san wannan ba zai amfani 'yata da komai ba.

Wata rana wata Qawata ta gaya min Cewa, takai ziyara wajen wata Qawarta, kuma Qawarta ta ba wata mai kula da addini ba ce sosai, amma a duk lokacin da aka kira sallah takan lura da 'ya'yan Qawartata sukan yi sauri su ta shi suje Sallah ba tare da an tsawatar musu ko tunatar musu ba.

Qawar tawa taci gaba da gayamin cewa, tayi mamaki kwarai a lokacin da ta ga yanda yaran nan ke lura tare da kula da Sallah. Sai ta tabbayi Qawartata Cewa, "Ko me yasa na ga yaranki daga zarar an kirayi sallah suke tashi ba tare da ke tsawatar musu ba?"

"Sirrin abin tun kafin Inyi aure na kasance Ina karanta Wannan addu'ar kowace rana kuma har yau ban daina karantawa ba". Haka ta gayawa Qawata.

Qawar tawa ta bani shawarar ni ma idan ina son 'ya'yana su kasance haka to nima In dukufa wajen karanta wannan addu'ar a koyaushe.

Tun lokacin da na dukufa wajen karanta wannan addu'ar 'yata ita ce ta farko wajen gabatar da sallah a gidan mu ba tare da an tsawatar mata ba.

Takan kuma tashi sallar asuba ba tare da ta saka alam ba. Haka ma duka 'yan uwanta da aka haifa daga baya suna sallah a lokaci.

Har ma dai aka kai itace ke tayar da mu sallar asuba kuma ita ke gaya mana lokacin sallah idan yayi Na san kun Matsu kuji Wace addu'ah ce nake karantawa to aya ta 40 ce a cikin Suratul Ibraheem
ِ
Wato, "Rabbi-Ajal'ni muqeema salaati, wa min Dhurriyyati, rabbana wataqabbal duaa" Hakika duka baya shiryar da 'ya'ya addu'ah ce ke shiryar dasu. Da fatan za'ah rika karanta wannan ayar da niya.

Jamilu Sani Rarah
Thu 19/05/2016


No comments:

Post a Comment