Monday, 11 July 2016

GAJERUN KALAMAN DR. BILAL PHILIPS GUDA 20



GAJERUN KALAMAN DR. BILAL PHILIPS GUDA 20 AKAN MANUFAR KARATUN ALQUR'ANI.


1. A cikin Watan Azumi Allah (SWT) ya saukarwa da Annabi Muhammad (SAWW) da Al-qur'ani mai Girma.

2. Hakika Allah (Swt) ya saukar da Alqur'ani ne don Ya zama rahama a gare mu (kamar yadda bayanin hakan yazo a cikin Suratul Al-Baqara).

3. Yawaita Karanta (Al-Qur'ani) a cikin Wannan wata (na Azumi) ba Karamar lada ake samu ba.

4. Daga cikin ladubban karatun Alqur'ani akwai buqatar tunani a kan ma’anoninsa yayin karatun
sa. Wannan kusan shi ne mafi muhimmancin ladaban karatun Alqur’ani gaba daya.

5. Al-Qur'ani gaba dayansa waraka ne, idan kana dauke da Cutukkan zamani kamarsu HIV, Cancer to ka dukufa wajen karanta shi Zaka samu waraka da Iznin Allah.

6. Allah (Swt) a cikin Alqur'ani Yana Gaya mana Cewa, "Al-Qur'ani Waraka ne amma ga muminnai". Don haka makawar mumini ya yawaita karanta (Al-Qur'ani) to Allah zai bashi lafiya.

7. Idan kana son ka samu labarai da sakonni daga Ubangijinka to ka nemi al-Qur'ani ka karanta.

8. Dukkan Wani Sako da yazo a Cikin Al-Qur'ani to zaka same shi a cikin Suratul-Al-bakara.

9. Ka tsaya ka Karanci suratul Bakara tare da Sanin sakonnin da take dauke da shi, shiya fiye ma da ka karance duka Al-Qur'ani amma baka san ma'anarsa ba.

10. Ko mu karanta Al-Qur'ani ko kada mu karanta, babu abinda zai rage ko kara Allah (SWT) da shi. Don haka 'dan Adam ya karanta (Al-qur'ani) domin ya samu albarkar da ke ciki.

11. Matan da ke dauke da Jinin Al'ada zasu iya karanta Al-Qur'ani da ka. Ba tare da sun dauki (Shi Al-Qur'anin) ba, domin su samu albarka da kariyar da ke cikin karanta shi.

12. Makawar Al'umma basu chanja halayensu ba to Allah ba zai fitar dasu daga kangin da suke ciki ba. Don haka mu cenja Rayuwar mu ta hanyar karanta Al-qur'ani.

13. Zaka samu musulmi masu kallon Kwallo (ball) Idan anyi abu mai kyau a cikin wasan zasu tafa da nuna jinjina amma basu cika damuwa da yin sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah) ba.

14. Idan har kana cikin tsanani to kafin ka koka kafara yin sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah).

15. Idan har ka tsinci kanka da samun wani alheri to ka gaggauta yin Sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah) domin nuna godiya akan wannan Ni'Imar.

16. Sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah) ana yin ta ba tare da Alwala ba.

17. Sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah) Mata zasu iya yin ta koda suna a cikin Jinin Al'ada. Don haka a kowane lokaci farin ciki ko bakin ciki ya same ka ka gaggauta yin ta.

18. Yaren larabci Shine yare na biyu ga kowane dan adam (musulmi da ma wanda ba musulmi ba), domin idan bahaushe yaje kasar chana ya tarar ana kiran sallah da yaren Chananci ba zai fahimci me suke yi ba, amma makawar akayi da larabci to, kowa ma yasan kiran Sallah ne.

19. Idan har ka samu damar karanta Al-Qur'ani ka qi kayi to babu makawa wahalhalu da matsaloli zasu dabai-baye ka.

20. Kada mu bari mu koma ga Allah (Swt) ba tare da Munyi Sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah) ko sau daya ne a rayuwar mu ba.

Wayannan kalamai zamu iya kiran Su da gajerun Kalamai a baki ko a karance amma ta fuskar fahimta tarin tulin Ilmi ne a dunkule tattare a wuri daya.

Dr. Bilal phillips (Abu Ameena) ya gabatar da Wayannan Kalamai ne a muhadarar da ya gabatar a Usman Danfodio University Sokoto akan manufar dake cikin karanta Al-Qur'ani a jiya Laraba 15/6/06.

Jamilu Sani Rarah Sokoto.
Thu 16/06/2016

No comments:

Post a Comment