Monday, 11 July 2016

KYAKYKYAWAR MU'AMULA NA SA A KAUNACI MUSULUNCI


KYAKYKYWAR MU'AMULA NA SANYA A KAUNACI MUSULUNCI
************************************************************
A lokacin da aka fara yin sufuri da jirgin European Airline, da akwai wani musulmi mai tsoron Allah a zuciyar shi a cikin Jirgin. Shi Wannn bawan Allah yana zaune ne a wurin da masu fada aji suke zama (Wato first class section a turance).

A daidai lokacin da Jirgi ya fara tafiya sai ma'aikaciyar Jirgi (wato air hostes) ta gabatar masa da kyautar kofin giya wadda kamfanin Jirgin ya dauki nauyin bayarwa ga fasinjojin jirgin.

Cikin ladabi da girmamawa ya kalle ta yace, "Nagode aini bana shan Giya" ta kalle shi cikin natsuwa ta gyangyada kai (alamar mamaki).

Wannan matar ta damu ainun da Qin shan Wannan giya da yayi, nan take taje ta sanarda Manajan akan akwai wani da yaki karba "..Wai baya shan Giya".

Manaja yayi tattaki har wajen wannan bawan Allah, Shima dai dauke yake da Giyar Yace da wannan mutumen; "Shin ko akwai abinda kake tunani game da mune? Hakika ka karba kasha wannan kyauta ce ta musamamman daga kamfanin mu".

Bawan Allah Cikin Ladabi Ya kalli Manajan Yace da shi, "Ni Musulmi ne kuma musulmi basa shan Giya".

Manaja yace yaji amma yana son ya karba ya shan ko da sau daya ko biyu ne domin wannan rana ta yau ranar farin ciki ce.

Wannan bawan Allah yayi murmushi ya dubi manajan Yace da shi, yaji zai sha amma suje ya fara bawa direban Jirgin ya fara sha sannan shi ma yasha.

Cikin mamaki manajan Jirgin Yace; "taya Direba zai sha Giya Alhali yana aiki (na jan jirgi?) Ai da zarar ya sha giya wannan jirgin zai samu Hatsari".

Wannan bawan Allah ya kalli wannan Manajan Yace da shi, "Ni musulmi ne sannan akoda yaushe ina kan aikina na tsare Imani na Idan har na sha wannan barasar to kuwa zan sanya rayuwa ta cikin hatsari domin zan rasa Imani na".

Allahu Akbar, Wannan ta sa Wannan manaja da wannan matar duka suka girgiza suka shiga tunanin karbar Musulunci daga hannun Wannan Bawan Allah.

Hakika haka Ake Son Musulmi ya siffantu da kyawawan dabi'u da kuna iya zance kada ya mayarwa da musulmi da wanda ba musulmi ba magana cikin zafi ko jin haushi.


Jamilu Sani Rarah Sokoto
Fri 24/06/2016

No comments:

Post a Comment