Monday, 11 July 2016

SABODA ME ZAMU KARANTA AL-QUR'ANI ALHALI BAMA JIN LARABCI?



SABODA ME ZAMU KARANTA AL-QUR'ANI ALHALI BAMA JIN LARABCI?
******************************************************************
***
Ina mamakin yadda kakana a koda yaushe yake kokarin Karatul Al-Qur'ani alhali baya jin abinda ake fadi (ma'ana baya jin Larabci).

Kamar kullum safe da rana da dare yake wannan karatu na al-qur'ani, yau dai da rana ne ya zauna yana karanta al-qur'anin sai gani nazo.

Abin nema ya samo dama ina bukatar in ganshi yana karanta wannan al-qur'ani domin in tambayesa dalilinsa na karanta al-qur'ani alhali baya jin larabci.

Na samu wuri na zauna ina jiransa domin ya kai aya muyi magana. Na zauna har tsawon mintuna 2 sannan daga baya ya tsayar da karatun da yake yi.

Nace dashi, Ya kai mahaifin babana akoda yaushe ina so inyi maka wata tambaya ce amma ban samu dama ba sai yau, Allah yasa zaka amsa min wannan tambayar tawa ba tare da kaji haushina ba.

Ya girgiza kai yayi min ishara da hannu da cewa in fadi tambayar yana jina. Nan sai na fara da cewa, "Naga kai ba balarabe ba, kuma kai ba Malami ba, kuma kai ba wanda ya zauna kasashen larabawa ba, hasalima kasashen turawa kayi karatun ka amma me yasa a kullum kake kokarin karanta Al-qur'ani Alhali baka jin yaren Larabci?"

Kakana ya nisa ya danyi tari, uhuk! uhuk! Sannan ya dubeni ya sake dubin gefensa na hagu sai ya dubi wani kwando (ga alama anyi aikin laka) da kwandon domin duka laka ya bata shi.

Sai yace dani, "Dauki wancen kwando je ka debomin ruwa a rijiya" taya yaya kwando zai iya diban ruwa? Nace da kakan nawa.

Kakana Yace dani, In shaa Allahu zai debo je kawai ka debo ruwan a cikin kwando. Ba tare da bata lokaci ba na tashi na dauki kwando na je rijiya na yi ta zuba ruwa a cikin kwandon amma dana zuba da ruwan sun zube a kasa.

Na zuba ruwan yafi a kirga amma da na zuba suke zubewa, nayi nayi har na gaji. Sai na dauki wannan kwandon naje na kaiwa kakana nace da shi, wallahi kwando ba zai iya debo ruwa ba amma idan ruwan kake so da gaske to bani wani abu (wanda ba kwando ba) inje in debo ma ruwan.

Kakana yace, a'a ni a kwando nake so kaje ka debomin ruwan. Anan na nuna masa kwando fa ba zai debo ruwa ba, amma ya matsamin akan sai naje na debo. A hakan na hakura na koma rijiyar domin debo ruwan a karshe dai na dawo ba tare da na debo ruwan ba. Saboda duk sa'adda na zuba ruwa a cikin kwandon zubewa sukeyi a kasa.

Bayan na dawo kakan nawa yace dani, har yanzu ka kasa debo ruwan ne? Nace masa, Eh bazasu debu ba. Sai yace dani, To shikenan amma dubi kwandon ka gani haka kaje dashi wajen debo ruwan?

Na dubi kwandon da kyau sai na ganshi yayi haske duk wannan lakar da ke manne a jikinsa ta debe kuma kwandon ya kara kyau, saboda wannan hasken da yayi.

Sai kakana Yace, TO HAKA AL-QUR'ANI YAKE A DUK LOKACIN DA KA KARANTA SHI KO BAKA JIN ABINDA AKE FADI TO ZUCIYARKA ZATA WANKE FES (Idan kana karantashi zai wanke ma daukar Hassada, Cuta, dasauran abubuwa).

Hakika tun daga ranannan na koma kamar Kakana Wajen Karanta Al-Qur'ani. Hakika naga fa'idar Karanta shi domin na kasance a cikin hassada da Kyashi kuma kullum nine gulma da sa'ido amma Cikin Ikon Allah duk na daina yin Wayannan abubuwan.

Jamilu Sani Rarah
Mon 23/05/2016.

No comments:

Post a Comment