Monday, 11 July 2016
LABARI MAI MA'ANAR GASKE
WANNAN WANI LABARI NE MAI BAN SHA'AWA NA WATA MATA MAI SUNA LAYLA 'YAR KASAR MOROCCO WADDA ALLAH YA JARABA DA CUTAR CANCER.
Likitoci sun taimaka matuka domin samarwa
da Wannan Mata Lafiya, amma Allah bai sa andace ba, hatta ita kanta Layla din ta debe tsammani daga Samun Waraka.
Ga abinda LAYLA ke cewa; Shekara tara Ina fama da Cutar Cancer duk wanda ya sanni ya san ina fama da wannan matsalar, kai hatta sunana aka fada Sai mutane sun tausaya min kasancewa Ina cikin wani hali na rai kwai-kwai mutu kwai-kwai.
Nayi tunanin in je in Kashe Kaina amma kuma tunanin irin hukuncin da zan tarar a Wajen Allah da kuma son da nake yiwa Mijina da 'ya'yana ya sanya dole na daina wannan tunani.
A lokacin da muka ziyarci Belgium, muje mun samu wasu likitoci game da matsala ta.
Shine suka gayawa Mijina Dole za'a debe nono na daya, sannan kuma zasu hadani da wasu maganguna.
Lokacin da suka bayyana mana sunan magungunan, sai naga ai da dadewa na taba amfani dasu.
Sukan sanya gashin kai na Zuba, sukan kuma sanya idona Fitar da kwantsa. Haka kuma sukan sanya Akaifun hannayena Kakkaryewa tare da sanya hakorana karyewa.
Kasan cewa, na san wannan maganungunan muka ki yarda da hakan. Na fiso in mutu da in koma amfani da wayannan magunguna.
Na buka ci likitocin da su cenja min magungunan saboda wayannan suna bani matsala, amma suka qi yarda da cenja min magungunan.
Na koma morocco in da likitana, Likitan nawa Ya bani Shawarar inje kasashen Yamma (Europe).
A Belgium akwai wani bala'i da suka tono min, domin kuwa likitocin sun gayawa mijina cewa, wannan Cutar ta shafi dukan Jikina Domin gaba daya wannan cutar ta mallake huhuna suka gayawa mijina babu wani abu da zasu iya akai don haka ya dauke ni ya mayar da ni Gida domin in mutu ko Allah yasa in mutu a cen.
A lokacin Mijina Ya Tsorata kwarai da gaske Amma mai makon mu koma gida morocco, Sai Muka Wuce faransa, a tunanin mu zamu samu mafita a cen (faransan).
Mu kaje Faransa amma babu wata mafita face irin Bayanin da muka samu a Belgium.
Daga Karshe sai muka yanke shawarar kawai a cire min Nonuwan in huta kamar yadda likitocin Belgium suka fada.
Muna cikin wannan tunanin ne kawai sai tunani ya fadowa Mijina "Hakika mun manta wanu abu guda wanda bamu damu da shi ba"
Na tambaye shi, "Menene?" "Bamu gaya wa Allah wannan Matsala taki ba" ya bani amsa.
Nan take mijina Ya Biya mana kuddin Visa da Taketi na jirgi na zuwa Saudiya (domin mukai kukan mu a dakin Allah).
Mu ka bar Paris "Allaho Akbar, La Ilaha Illa Allah" (Allah mai girma hakika babu sarki sai Allahh).
Nayi matukar farin ciki domin wannan shine farkon lokacin da zan yi tozali kuma in ziyarci dakin Allah.
Tun a paris na sayi Alqur'ani mai Girma abinda ban taba mallakarsa ba (na wa) a rayuwa ta.
Da shigar mu makka.. a lokacin da muka shiga masallachi tsarki, ai kuwa daga shiga ta ciki na fashe da kuka (kuka ba kadan ba).
Irin yanda naga an tsara wurin an qawata shi kuma na tuna da wurin da Annabi yayi Ibada kenan wuri mai falala da rahama shi yasan ya ni kuka.
Sannan a gefe daya ina kukan ne saboda ban taba fuskanta ko tunanin wannan wuri ba a rayuwa ta kuma ban taba rokon Allah ko tuna shi ba a shekarun baya.
Anan Nace, "Ya Allah! Kaine likitan likitocin da suka kasa warkar dani, duka kofofin samun waraka sun rufe min, banda wata mafita baya fa In rokeka, Ya Allah! Ya Allah! Kada ka rufe min kofar waraka".
Na ci gaba da kewayar dakin ka'aba ina rokon Allah akan Ka barni in koma hannu sake ba tare da na samu waraka daga gare shi ba.
Kamar yadda na fada a baya cewa, ni macce ce da bata da mu da harkokin musulunci ba, hasalima duk wani abu da ya jibanci musulunci kauyanci nake ganinsa.
Amma yau da kaina naje wajen wasu manyan malamai dake kasa mai tsarki ina neman taimako a garesu.
Suka bani shawara akan In je in rika karanta Alqur'ani Mai Girma, Sannan kuma suka bani shawarar in rika amfani da ruwan Zamzam.
Su Umurceni da In rika yin "Tadhalloo" kamar yadda suka kiransa da larabci ( Tadhalloo shine ka sha ruwan Zamzam Masu yawan gaske har sai ka ji ka koshi).
Sannan suka bani shawarar akan a duk lokacin da zan sha wannan ruwan in fadi sunan Allah tare da yin Salatin Annabi (Saww)
Suka bani tabbacin In shaa Allahu Idan har na Rika yin haka Allah zai bani Lafiya in dawo kamar kowa.
Anan na roki Mijina akan ya barni I zauna a Haram ba sai na koma Hotel ba l, mijina ya amince min akan in zauna a masallacin Haram shi ya koma a Hotel yaci gaba da zama.
A masallacin ne na hadu da wasu matan da suka zo daga Egypt da turkiya wayanda suka tausayamin a lokacin da nake yin kuka mai tsanani.
Suka tambayeni dalilin da yasa nake kuka, anan na sanar dasu duka labari na da kuma ciwon da ke tare da ni.
Allah Sarki basu gujeni ba suka zauna tare dani haka suma suka tambayi Izni daga mazansu akan su barsu domin su zauna a tare dani a masallaci.
A wannan zaman bama wani bacci kuma bama wani cin abinci mai yawa ko mai gina jiki, amma fa su ruwan zamzam mukan sha su da yawa har sai sun cika cikin mu.
Dama kuma Annabi (Saww) yace, duk wanda ya sha Ruwan Zamzam Allah zai warkar da shi idan har ya sha da niyar hakan.
A haka muka ci gaba da shan wannan ruwan muna rokon Allah kuma muna Dawafi tare da karatun Alqur'ani Mai girma. Wannan shine aikin mu safe da dare.
A lokacin da muka zo Dakin Allah babu shakka duka sassan Jikina yayi rauni sosai da sosai, domin Nonuwa na har fitar da Wasu ruwa masu wari hade da jini suke yi.
Saboda wannan kansar ta gama Illata min sassan Jiki na Duka.
To a lokacin cin Sai Wayannan Qawayen nawa suka Bani shawarar in rika wanke duka sassan jikin nawa da ruwan Zamzam. Ni kuma naki saboda ina tsoron Abinda zai iya biyowa baya domin ina gudun taba wannan Jikin nawa musamman Nonuwana.
Da ga farko na ki yarda da in rika wanke duka Jikina amma suka matsamin tare da takurani akan lalle sai na rika wanke jikina da ko wanka da wayannan Ruwan. A haka dole na bi shawarar su.
Na fara wanke Jikin nawa da wayannan Ruwa da farko na fara jin ciwo amma sai na daure na rika wanka da wayannan ruwan.
Cikin kwana Goma Sha Biyar da nayi Ina Wannan Wankan Na tarar da wani abu wanda sam nayi tunanin ba zai taba yiwuwa ba.
Domin ina taba Nonuwana na tarar babu jini babu Ciwo, nan da nan na bude duka sassan Jikin Nawa, domin ganin abin da ke faruwa da jikina.
Na tsarata kwarai da gaske ainun domin babu alama guda da zata tabbatar ma cewa nayi fama da Ciwo a Jikin nawa.
Nan na bude wa daya daga cikin Qawayen nawa jikina na Umurce ta da ta taba jikin nawa taji ai kuwa tana tabawa Dukan su Suka Dauki kabbara.
Allahu Akbar.. Allahu Akbar!! Na take na Arce da gudu na koma Hotel wajen Mijina.
Na Cira Rigata sama na Ce da shi, "Ka dubi taimakon Allah!" Anan na gaya masa duk abubuwan da suka faru da abinda kawayena suka sani in rika yi.
Nan take ya fashe da Kuka yace dani, "Shin ko ke san Likitoci sun Rantse da Allah akan nan da sati 3 zaki mutu akan wannan cutar?"
...Na Ce da shi; "Duka kaddara tana hannun Allah (Swt) babu wanda ya san abinda zai faru da wani face Allah Shi kadai.
Anan muka zauna har tsawon Sati daya, Na yiwa Mijina Godiya sosai da sosai abisa kokari da hakurin da yayi dani, su kuma wayannan kawayen nawa muka zama kamar Juna Ni da su.
Baya ga haka muka koma masallacin Annabi (Saww) da ke Madina. Daga nan muka wuce France.
A cen Lokacin da muka ziyarci Likitocin cen, duka wayannan likitocin suka Shiga mamaki tare da tambaya ta akan, 'Anya kuwa ke ce mai dauke da wannan Cuta?'
Cikin Izzan Na Ce da Su, YESS!! ..and this is my husband..we have
returned to God.. and I now fear nothing but Allah SWT.. (Ma'ana, Eh sannan kuma wannan Mijina ne mun koma nema ga Allah ne, Sannan yanzu babu wani abu da nake tsoro face Allah (SWT)).
Suka Ce Cuta ta babba Ce sosai da Sosai, Sannan Suka Sake Bukatar su sake yimin Gwaji.
Suka gwada amma basu tarar da wata matsala ba ko da ta Matsalar ciwon Kai Ce.
Bayan 'yan watanni na Samu "seerah" (tarihin Annabi (Saww) na rika karantawa da na shi da na sahabbansa (RA).
Hakika nayi Kuka kuma nayi da na sanin lokacin da na bata ba tare da kulawa da Wayannan Tarihin ba.
Hakika Na Yarda Cewa, Ruwan ZamZam Magani ne Makawar Ka sha da Niya kamar Yadda Hadisan Annabi (Saww) Suka Bayyana.
Jamilu Sani Rarah
Mon 13/06/2016.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment