YIN SADAKI MILION 12 ADDINI KO WAYEWA?
******************************************
Yana da kyau
Idan kana Shugaba ka rika yin abinda idan Kayi shi talakawa da wayanda
ke Biye da kai zasu kwaikwaya domin daukar darasi daga gareka.
Nayi Mamaki ainun Lokacin da naji cewa Naira na Gugar naira har naira
Million goma sha biyu (12 Million), aka yi sadakin 'yar Galadiman Zazzau
kuma ta hannun Sarkin Zazzau
Hakika indai ta tabbata haka
akayi sadakin to kuwa Sarkin Zazzau ya fita daga Jerin Sarakunan
Musulmai. Domin wannan Ruguza Musulunci ne.
Dalilina anan
Shine duk wani musulmi yana son Annabi (saww) tare da kwaikwaya daga
gare shi. Domin nuna biyayya da kauna a gareshi.
Shin ko 'yar Sarakai tafi Nana Fatima (RA) matsayi da daukaka ne?
Idan ana maganar kyaune ko matsayi a duniya idan aka kawo Nana Fatima
(RA) to kuwa Sai dai a shafe fatiha a tashi (domin itace KHAIRUL NISA'IL
ALAMINA).
Bayan kasancewarta Mace mai matsayi kuma kyakykyawa haka ma Mahaifinta yafi kowa matsayi a duniya da lahira.
Lokacin da Sayyidina Aliyu (RA) ya yanke hukuncin zuwa neman Auren Nana
Fatima (RA), Daga nan ya tashi ya yi wanka sannan ya yi alwala ya kuma
yafa mayafinsa ya yi nafila raka'a biyu, ya nufi wajen Annabi (Saww) a
lokacin Annabi (saww) yana dakin Ummu Salama (RA).
Da Isar Sayyidina Aliyu Ya yi sallama, Manzon Allah (saww) ya amsa masa, Sai Sayyidina Aliyu (RA) ya zauna a gaban Manzo ya dukar da kai kasa; ganin haka sai Annabi ya ce masa: "Ya Aliyu, Ka zo da wata bukata ce?"
sai Sayyidina Aliyu ya ce: "Na'am, na zo neman auren 'yarka Fatima ne;
ko za ka aurar min da ita Ya Manzon Allah?"
Ummu Salama ta ce: "A lokacin sai na ga fuskar Manzon Allah ta cika da annuri na farin ciki da murna,
Sannan ya kalli Sayyidina Aliyu ya yi masa murmushi. Daga nan sai
Manzon Allah (saww) ya shiga wajen Nana Fatima ya ce mata: "Ali bin Abi
Dalib, wannan da kika san kusancinsa da darajarsa a Musulunci ne, ya zo
yana zance a kan al'amarinki (wato yana neman auren ki).
Hakika kuwa da ma ni na roki Ubangijina da ya aurar da ke ga mafi alherin talikanSa. To me kike gani?" Sai ta yi shiru.
Sai Manzo Allah (saww) ya fita yana cewa: "Allahu Akbar! Shirunta
yardarta ne". Sannan ya cewa Sayyidina Aliyu (RA): "Ya Aliyu, shin kana
da wani abu
da zan daura maka aure da shi (sadaki)?".
Sai
Sayyidina Aliyu (RA) ya ce: "Sai takobina da garkuwata, sai kuma
rakumina na ban ruwa ", (a wata ruwayar an ce doki ne maimakon rakumin).
Sai Manzon Allah (Saww) ya ce: "Amma takobinka kana da bukatarsa, za ka
yi yaki da shi a tafarkin Allah kuma ka kashe makiya Allah da shi.
Rakuminka kuma kana shayar da (gonar) dabinonka da shi, haka kana daukar kaya da shi,
kuma yana daukarka a tafiye-tafiyenka.
Don haka je ka yi yadda za ka yi da garkuwarka". Sai Sayyidina Aliyu
(RA) ya je ya sayarwa Sayyidina Usman bin Affan (RA) da garkuwarsa a kan
farashin dirhami 480, sai ya kawo wa Manzon Allah (saww).
Daga nan Manzon Allah (Saww) ya sanar da Musulmi zancen auren. To
Sadakin Nana Fatima (RA) kenan fa. Ina ga diyar Galadiman Zazzau da ba
'yar kowa ba?
Hakika bayan wannan akwai hadisi sukutukum wanda
Manzon Allah (saww) yake cewa, Aure Mafi albarka shine wanda sadakinsa
ya zamo mafi sauki".
Har An Ruwaito Cewa Sahabbai (RA) suna Cewa, "FIYAYYEN AURE SHINE AUREN UMMU SULMAN (RA), DOMIN ITA SADAKINTA MUSULUNCI NE."
Ummu Sulman Itace Mahaifiyar Anas Bin Malik lokacinda mahaifinsa ya
rasu, taqi yin aure har Saida Abu Talha ya fito yana Sonta sannan ta
amince zata aure shi amma da sharadi zaya Musulunta (Musuluntarsa Shine
Sadakinta).
Bayan manyan attajirai da Masu mulki da Sadaukai sunyi ta fito mata amma taki amincewa dasu.
Hakika Am Very Disappointed akan Masarautar Zazzau Sun Ci Mutuncin Addinin mu in dai hakan ta tabbata akan wannan Sadakin.
Domin Ko Rantsuwa nayi bana bukatar kaffara cewa, A cikin dangin angon
ko dangin Amaryar akwai wanda ke Bukatar Taimakon Dubu goma (10
thausand) ta gagare shi.
Akwai ma wanda Ke neman abinda zaici, haka kuma akwai masu neman Tallafi domin Suyi karatu ko auren.
A karshe Ina Kira ga Matasa Wallahi duk inda kaje neman Aure aka zabga
maka Sadaki Mai yawa ka barta ka nemi wata, domin Muddin Sadaki yayi
Yawa a aure to An riga da an debe Albarkar Auren. Kuma Allah yana Fushi
da kai da Iyayen Matar.
Babu Shakkah da Wani Attajiri ne ya
bada 'yarsa akan wannan sadakin ba zamu damu ba, kasancewa baya amsa
suna da Jagorar Musulmi.
Da Wannan nake Addu'ar Allah ya
Shiryemu, Allah kuma Ya jikan Marigayi Jafar 'dan Ishaqa, domin a
lokacinsa Zazzau take masarauta me bin koyarwar Musulunci.
Jamilu Sani RARAH
Wed 13/01/2016.'
No comments:
Post a Comment