Saturday, 9 January 2016

HANKALINA YA TASHI DANA GA JAHILCI KARARA

HANKALINA YA TASHI DANA GA JAHILCI KARARA
**********
Sako Zuwa Ga Dalibban Ilmi (Almajirai masu neman Ilmi), Kuma Wannan Sakone Ga Malamai (Masu karartarwa).
.
Hakika An turomin Wani Vedio a Whatsapp, babu shakkah Hankalina ya tashi dana kalli vedion.
.
A Vedion an nuna wani Zindikin Malami a saman Kujera yana Alwala, wasu almajiransa Suna kewaye da shi suna jiran ya idar da Alwalar.
.
Bayan yakai wajen wankin Kafafuwa (ya zuba ruwa yana wanke wa), kawai sai Wayannan Almajiran nasa suka tara hannayensu suka shanye ruwan tare da shafe ragowar Ruwan a jikinsu (da sunan Neman Albarka). Wa'iyazubillah.
.
Kirana ga Dalibban Ilmi shine, Hakika Duk duniya ba'a ta6a Malami masani Mai albarka ba kamar Annabi (saww).
.
Hakika Fitsarin Ma'aiki (saww), Maganine, Zufan Jikinsa yafi Miski Kamshi, hakika Yawun Bakinsa (saww) Maganine.
.
Amma duk Irin Wannan Baiwar ta Fiyayyen Halitta (saww), Ya hana SahabbanSa (RA) tashi tsaye idan Suka ganshi.
.
Hakika yana Mu'amula da su ta aminci tare da Shiryar da su bisa hanya madaidaiciya.
.
Hakika yana da matukar kyau Girmama Malami, amma Sam ba irin wannan ba.
.
KUSANI NI JAMILU SANI RARAH BANA DURKUSAWA MUTUM KOMAI ILMINSA KO KUDDINSA KO MATSAYINSA.
.
Hakika Ina Rusunawa In gaida mai kuddi ko Ilmi amma ba na kaiwa har kas, don haka Kaima Ina so kaima mai karatun wannan rubutu ka zamo haka (kamarni).
.
Nima kuwa na Kwaikwayi Wannan ne daga Babban Shahabin Manzon Allah (saww), wato Abdullahi Bin Abbas (RA).
.
IBN ABBAS (RA) shine wanda a lokacin aikin Hajji ya Sumbaci HAJRUL ASWAD (bakin dutsin da ke dakin Ka'aba), Wanda Sumbatarsa na daya daga cikin Farillan aikin hajji.
.
Bayan Ya Sumbaci Dutsin Sai Yace, NA SUMBACE KA NE KAWAI DON ALLAH YAYI UMURNI A YI, AMMA NI NA SAN BAKA CUTARWA KUMA BAKA DA WANI TAIMAKO DA ZAKA IYA MINI.
.
Hakika wannan ya nuna mana Girmama abu Fiye da Kima na da Matsala.
.
Sannan Ku kuma malamai Kuji tsoron Allah jallah wa Azzah, domin Allah zai tambayeku akan Abinda Kuka koyar tare da Aikatawa.
.
Allah ya ganar damu Gaskiya Ya kuma bamu ikon Binta, Ya nuna mana Karya ya bamu ikon kauce mata.
.
Jamilu Sani RARAH.
Fri 08/01/2016.

No comments:

Post a Comment