KUSKUREN MU A SHEKARAR 2009
*******
Shekaru biyar da Suka gabata, Sitayrin Motar wani Aminina ya kulle a
daidai lokacinda ya juya Sitayrin domin Shiga kwana, bai an kara ba
kawai Sai jin motar yayi ta mazgi wani katon Iccen Darbejiya (Neem
Tree).
Wanda wannan yayi Sanadiiyar lalacewar Gaban motar Sosai da sosai, muka ja motar muka kai wajen gyara.
Wannan daliline yasa muka Ari Mashin hannun wani Abokin mu domin yin
Zirga-Zirga zuwa wajen gyaran motar. Ai kuwa ashe rabon ayine.
Domin Wannan Mashin din bai kwana biyu a hannun mu ba aka dauke shi,
ganin an dauke shi a hannun mu sai wasu suka bamu shawara akan kada mu bayyana bacewar Mashin din kowa yaji muyi neman sa a boye.
Haka kuwa akayi mukayi ta neman wannan mashi lungu da sako amma ba
labari, a haka har muka kai wajen masu gyaran mashin a tunanin mu ko
za'a kai shi wajen a cenja masa fasali.
Nan dai muka duba ko
ina amma bamu samu ganin mashin din ba, mun fito zamu wuce kenan Sai
muka hadu da wani yaro (ga alamu Gyaran mashin yake). Anan dai Muka gaisa da shi, Sai ya dubi wanda muka ari mashin dinsa yace masa, "ALMUSTAPHA INA MASHI?"
Almustapha Wanda Shi ke da mashin din da aka dauke Yace da Shi, "MASHIN
YANA HANNUN WANI" (Ba tare da ya gaya masa 'dauke mashin din aka yi
ba).
Anan dai Mukayi sallama da yaron Muka wuce, bayan mun
wuce ne muka tambayarsa ina yasan wannan yaro? Shine yake gaya mana
cewa, ai shike masa gyaran mashi din.
Muka ce ai kuwa irinsa
bai kamata ka boye masa da'uke mashin din akayi ba, anan muka juya domin
a gaya masa abinda ke faruwa, domin yasganshi.
Ai kuwa Muna zuwa Sai yake gaya mana cewa, Yanzu ko ya ga Mashin din an
wuce da shi, nan muka bi hanyar da aka bi da mashin din tare da shi ko
zamu samu ganin mashin din.
Amma ina mashin yayi nisa, har
muka gaji da nema a karshe dai muka dauki hukunci Muka saya masa wani
mashin din, har yanzu dai babu zancen ganin mashin din.Shekaran Jiya da Rana Wata 'yar Uwata ta fita kasuwa da motar mahaifiyarta.
Kwatsam tana fitowa daga kasuwa sai ta tarar an dauke motar (anyi awon gaba da motar).
Nan take aka gayawa dukkan makusanta (ma'ana 'yan uwa na nesa dana kusa) akan sace wannan motar da akayi.
Ai kuwa da Allah yasa raboce cikhn awoyi Shida (6 hours) aka ga motar a hanyar Sheme (dake Jahar Katsina).Babu Shakkah Saurin bayyana 'bacewar abu ga 'yan uwa kan taimaka ainun domin kabke 'barawon abin.
Hakika da Allah ya kaddaremu da gayawa Mai gyaran mashin din 'bacewar
mashin din da Mun samu kama 'barawon da hannun mu, amma a tunanin mu kar
aga mun cika raki muka boyewa jama'ah sace Mashin sai muka yi rashin
sa'ar kama 'barawon mu.
A karshe ina bamu shawarar idan abinn
mu ya 'bata to mu gaggauta shelantawa makusantan mu wayanda ke gari da
ma wayanda basa gari.
Babu shakka wannan hanyar zata taimaka mana sosai waj kame 'barayin mu.
Ya Allah ka Shiryarda mu akan gaskia.
Jamilu Sani RARAH
Mon 11/01/2016.
No comments:
Post a Comment