BUHARI YA RAINA HANKALIN MU DA BINCIKE
**********
Aka Ce Idan kanada Gaskia to kar kaji tsoron Magana ko a gaban waye ko waye shi.
Labari Ya Isheni Cewa, Hukumar EFCC ta sallami Lawal Jafar Isah wai don
ya bada kaso 60 cikin 100 na kuddin da ake tunanin ya handame da
Jama'ar Nigeria.
Lalle Idan hakane ta tabbata Nigeria ba zata
gyaru ba a hannun Shugaba Buhari domin kuwa Sam ba Adalci yake nufi ba a
wannnan Lamari.Hakika duk Mulkin da Ba'a adalci a cikinsa to Mulkin Baza'a samu nasara a cikinsa ba, ko da kuwa Shugaban Cikakken Musulmi ne.
Ina da Tabbaci akan Duk Mulkin da ake adalci a cikinsa Za'a dade ana
cin moriyar Mulkin koda na kafiri ne, mu dau darasi daga America.
Na san baku da bukatar Sanin Waye Lawal Jafar Isah, du da haka zan karaa aska muku domin ku kara sanin waye Shi.
Lawal Jafar Abokin Shugaba Buhari ne na Kud da kud, kuma tare suke
Siyasa tun tali-tali, hakika idan har an Sake Lawal Jafarr to Kuwa Babu
Sauran "MAGANAR CHANGE A NIGERIA" tabbas nageria an gama yaudarar ku da
Fuskar Salihan Bayi domin ayi Ramuwar gayya ga 'yan adawa.
Allah ya taimaki duk Mai Gaskia ya bayyanar da duk Mai karya.
Jamilu Sani RARAH
Mon 11/01/2016.
No comments:
Post a Comment