Saturday, 23 January 2016

DUNIYA INA ZAKI DAMU?

DUNIYA INA ZAKI DAMU NE?
****************************

Kalubane Ga Malammai Da Masana Tare da Iyaye da Abokanai da Shuwagabanni.

Wannan Labarin ya Saka ni Jin haushi kuma na Rasa a wajen wa Zan huce Haushina? kuma laifin wa zan gani?

Wani mutum ne 'dan Asalin karamar hukumar Rogo a Jihar Kano , ya yi aure amma sai ya kasa gusar da budircin matarsa.

Sai ya je ya samu Wani Abokinsa akan ya taimakeshi ya je ya gusar masa da Budurcin na Amaryarsa, shi kuma abokin ya aminta da hakan amma da Sharadin zai bashi Naira dubu da dari biyar (1,500).

Da abokin angon ya je zuwan farko shima sai ya dawo ya nuna aikine mai wuya don haka sai an kara masa Naira 1,000.

Angon ya amince, da ya sake komawa zuwa na biyu sai aka yi sa'a sannan ya zo ya shaida masa cewa an riga an gama ko mai don haka ya bashi kudinsa.

To anan ne Angon ya bashi Naira 1,500 maimakon 2500, tare da bashi hakuri.

Shi kuma ya nuna sam ba zai yarda ba wannan ba sai an biya shi kuddinsa duka.

Anan ne amarya ta bukaci da ya yi hakuri tunda ai ko babu komai shima ya ji dadi. Wannan labarin ya sakani masassara (zazzabi tare da jin taici).

Shin laifin Waye Anan? Babu shakkah Laifi na farko na daura shi kaco kan akan Iyaye domin 'ya'ya kiwo ne Allah ya bawa iyaye, kuma ya tanadi wata ukuba mai yawa ga wanda ya kasa kula da wannan hakkin.

Manzon Allah (saww) na Cewa,

ﻣﺎ ﻣﻦ ﻋﺒﺪ ﻳﺴﺘﺮﻋﻴﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺭﻋﻴﺔ ﻳﻤﻮﺕ ﻳﻮﻡ ﻳﻤﻮﺕ ﻭﻫﻮ ﻏﺎﺵ ﻟﺮﻋﻴﺘﻪ ﺇﻻ ﺣﺮﻡ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺍﻟﺠﻨﺔ

Ma'ana, Babu wani bawa da Allah zai ba shi kiwo, ya mutu ranar mutuwarsa yana mai algushu ga abin kiwon da Allah ya ba shi face Allah ya haramta masa shiga Aljannah.

Babu ko Shakkah Wannan hadisin kalubale ne ga iyaye domin daga cikin Hakkokin 'ya'ya akan iyaye akwai, Tarbiyantar da su, Kaisu Makaranta, Ko ya musu Sallah, tare da zabar musu mata.

Wasu daga cikin Iyayen Yanzu basa kula da karatun 'ya'yansu na Addini sai dai na Boko kawai.

Laifi na Biyu kuma na jingina shi ne ga malamai, Domin da ace Malamai suna, Sanarda dalibbansu Hanyoyin zama da miji ko Mata.

Tare da Sanar dasu Abubuwan da Saduwar Aure ke bukata da ma wanda bata bukata.

Hakika Wannan Kalubale ne ga Malamai (na boye Ilmi), Domin Annabi (Saww) Yace,

ﺃﻳﻤﺎ ﺭﺟﻞ ﺃﺗﺎﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻤﺎ ﻓﻜﺘﻤﻪ، ﺃﻟﺠﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﺑﻠﺠﺎﻡ ﻣﻦ ﻧﺎﺭ.

Ma'ana "Dukkan mutumin da Allah ya bashi ilmi kuma ya
Boyeshi to Allah zai yi masa linzami da wuta a Ranar Alkiyama.

ALLAH YA KIYAYE MU DAGA AIKIN RASHIN ILMI TARE DA BOYE WA JUNA DUK WANI ABU DA MUKA SANI.

Jamilu Sani Rarah
Sun 17/01/2016.

No comments:

Post a Comment