Wednesday, 3 February 2016

ZUWA GA 'YAN GANI KASHENI BUHARI

ZUWA GA 'YAN GANI KASHENI BUHARI
*******
Da yawa daga Cikin Mu 'yan Nigeria Mun Jahilci Menene SO? mun Kuma Jahilci Menene Gaskiya.

Wataran masoyinka sai yayi kuskure, kuma ka sani sai soyayya ta rufe maka ido ka kasa ganin wannan Kuskuren  Nashi.

Kamar yanda Watarana makiyinka sai yayi daidai, amma kiyayya ta rufe maka ido sai ka Nuna Kuskure yayi.

Abinda zamu duba a nan shine duk kiyyayar da Allah yake yiwa
yahudawa amma da aka sami masu rike amanar kudi a cikinsu sai da Allah ya fada.

Haka kuma mu duba irin soyyayar da Allah yake yiwa Annabi (saww), amma da makaho yazo wajensa ya daure fuska sai da Allah ya fada.

Mu tuna yadda Annnabi (Saww) yake son Nana Aishah (Ra), har an taba tambayars Cewa, Wakafi So ya Rasulillahi? Ya bada amsa cewa, "AISHA, A CIKIN MAZA KUMA MAHAIFINTA (Sayyidina Abubakar (Ra))", amma Annabi (saww) yace, da zata fasa kwanon Nana Safiyya (RA) da sai ta biya.

Nana Aisha (RA) da kanta take Cewa, Wata rana Manzon Allah (saww) zai fita daga gida, sai ya tuna da Khadijah, ya fadi wasu
kalmomi na girmamawa gare ta. To amma sai na gagara rike kai na sai na ce masa; 'Ita dai ba wani abu ba ne face tsohuwar mace, kuma a halin yanzu Allah ya musanya maka wadanda suka fi ta'.

Nan take Manzon Allah (saww) ya maya min da martani, cikin fushi yana cewa: "Lallai ba haka ba ne...lalle ban samu wadanda suka fi ta ba. Don kuwa ita ce ta yarda da Annabcina a lokacin da kowa ya kyale ni. Ta ba ni dukkan dukiyarta a lokaci mafi tsanani (na bukatuwa da su).

Kuma Allah Ya ba ni zuriya ta hannunta, alhali kuwa ya haramta min daga wasunta".

Lalle Wannan Kadai Zai saka mu fahimci Cewa, Fadin Gaskia ga Masoyi Shine Cikakken So, ba boye Gaskia ba.

Sannan Allah (swt) yana umurce mu da fadin Gaskia ko da akan kan mune.

Manzon Allah (saww) yace: "ku
lamunce min abu shida (6) zan lamunce muku shiga Aljanna:

(1) Ku rinka fadar gaskiya. (2) ku rinka cika alkawari. (3) Ku rike amana. (4) ku kame kanku. (5) Ku kame hannuwanku daga abubuwan da ba naku ba".
(Ahmad 5/233/323).

Don haka mu rika Fadan Gaskia akan kowa komai ma tsayin mu, Idan kuma muna tunanin sai mun qi fadin gaskia zamu samu abinci to mu Muji tsoron Allah, FATTABU INDALLAH, Munema A wajen Allah, domin shine me bayarwa da hanawa.

Allah yasa Mu dace.

Jamilu Sani RARAH
Fri, 01/01/2016.

No comments:

Post a Comment