Saturday, 13 February 2016

ME YASA HAKA 'YAN AREWA?

ME YASA HAKA 'YAN AREWA?
********
Malamai masana suka ce, "IDAN HAR A LOKACIN DA KAKE CIKIN FARA'A DA ANNASHUWA BAKA TUNA ALLAH BA ME YASA A LOKACIN DA WANI ABU MARAR DADI YA SAMEKA ZAKA TUNA ALLAH?"

So da yawa nake mamakin 'yan arewa a lokacin da Allah ya azzurtasu ya kuma wadata musu aljihunsu bazakaji sunyi godia tare da neman mai neman taimako ba don su taimake shi, amma daga ranar da baida kuddi zaka ji shi yana ta ganin laifin mutane tare da yin tsinuwa ga wasu.

Babu shakka wannan mulki na Shugaban Kasa Buhari wasu daga cikin talakawa dama wasu wayanda ba talakawa ba na cikin wani hali na rashi.

Shin tsinuwa ce zata fitar da mu daga wannan halin? Sam tsinuwa da munanan kalamai ba sune mafita ba.

Wata Rana Annabi (saww) yana tafiya tare da Sahabbansa (RA), wani daga cikin sahabban Rakuminsa yaqi tafiya sai wannan mutumen ya tsinewa rakumin nasa tare da la'antarsa.

Nan take Annabi (saww) yace a dakata. Bayan an dakata sai Annabi (saww) ya dubi sahabin yace, to tunda ka tsine masa ka sake shi ya shiga daji hakika mu ba zamuyi tafiya da tsinanne ba.

Wannan ta sa dole wannan mutumen ya saki wannan rakumi ya shiga daji, suka ci gaba da tafiya.

Da yawa daga cikin mu 'yan Arewa mu ke janyowa kan mu matsala, tun mulkin Goodluck Jonathan har zuwa yanzu Mulkin Buhari 'yan Arewa sune kan gaba wajen 'bata lamarin mulkin kasar nan.

Hakika cenja halittar shugabanni ta hanyar mai dasu siffar mata ko wata kaskantacciyar siffa na daga cikin abinda ke 'bata mulkin kasarnan.

Hakika ina bakin ciki yanda wasu ke cenja siffofin shuwagabannin Kasarnan, da wannan nake son tunatar da mu hadisin Annabi (saww) da ke cewa, Allah ya tsinewa ya koma ya tsinewa namiji mai cenja siffansa zuwa siffar mata, haka kuma ya tsinewa duk maccen da ta siffantu da siffofin maza.

Ka sani ya kai 'dan uwa a lokacin da ka dauki photon wani ko wata ka cenja masa fasali zuwa macce ko namiji to wannan tsinuwar zata hau kanka ne.

Jamilu Sani RARAH
Sat 13/02/2016.

No comments:

Post a Comment