WANNAN LABARIN YA FARU DA GASKE
*********
An yi wani mutum a Egypt, wannan mutumen ya kasance yana da matsalar ciwon zuciya. Ya kama hanya yaje asibito domin a duba shi.
Bayan gama yi masa dukkanin gwaje-gwaje (medical cheak up), sai likitan ya ce da shi, "HAKIKA DUKKAN JIJIYOYIN DA KE KAI JINI A ZUCIYARKA BASA KAI JININ YANDA YAKAMATA."
Mutumen ya dubi likita yace da shi, To me zai hana ayi min tiyata ko zan samu lafiya? Likitan ya shaida masa cewa, akwai wani likita gwani a wannan fanni dake zaune a kasar Germany don haka kaje wajensa zai yima wannan tiyata.
Bayan 'yan kwanakki wannan mutumen ya tashi daga Egypt zuwa Germany, bayan ya sauka yaje masaukinsa ya kwata.
Da wayewar Safiya wannan mutumen yaje ya samu likitan, likitan ya shaida masa cewa, Hakika na dau shekaru ina wannan aikin wasu ana samun nasara wasu kuwa ba'a samun nasara, don haka idan ka amince kaje jibi ka dawo in yima aiki.
Bayan kwana biyu wannan mutumen ya koma wajen likita tare da neman uzuri akan ya bari ya koma gida domin ya biya bashin da ake binsa kuma yayi ban kwana da matarsa da 'ya'yansa da iyayensa da sauran 'yan uwa.
Likita yace, ba damuwa, wannan mutumen ya koma gida (Egypt), bayan komawarsa gida da kwana biyu yana tafiya a dai-dai wata tashar mota kawai sai ya ga wata tsohuwa tana tsintar kashin da aka ci aka raga wajen wani mai sayarda nama.
Wannan mutumen yaje ya tambayeta dalilin da yasa take tsintar wayannan kasusuwan, sai matar ta buda baki tace da shi, "YAU KUSAN SHEKARA BIYU HAKA MUKE CIN NAMA NI DA 'YATA (MARAINIYA), SABODA BAMU DA KUDDIN DA ZAMU SAYI NAMAN."
Daga jin hakan wannan mutumen ya cewa mai sayarda naman, Zan biyaka kuddi ka rika ba wannan mata nama kullum har tsawon shekara daya.
Nan take wannan matar ta fara yi masa addu'ah, "Ya! Allah ka baka lafiya da kai da iyalinka, ya Allah ka biya maka bukatunka duniya da Lahira" Wannan mutumen ya wuce zuwa inda zashi.
Bayan ya koma gida sai 'yarsa tace, Baba wallahi naga komai naka ya cenja, hakika yau na ganka cikin fara'a, meke faruwa?
Ya bata amsa akan babu abinda ke faruwa, bayan ya gama abubuwan da yake kwana biyu yayi sallama da gida ya koma zuwa kasar Germany domin aiki.
Bayan yaje wajen likita sai likitan ya kara yi masa wasu gwaje-gwaje wanda daga sune za'a shiga yi masa wannan tiyatar.
Lokacin da likitan ya gama gwaje-gwajen da yake sai ya tambayi mutumen, Wace Asibiti kaje? Mutumen yace, Babu asibitin da naje.
Likitan yace, A'a kada muyi haka da kai hakika kaje wata asibiti sun baka wani magani domin duka jijiyoyin da suka rufe yanzu sun bude don haka baka bukatar aiki (operation).
Mutumen yayi murmushi yace, "HAKIKA NA SAN WANDA YA WARKAR DA NI, SHINE ALLAH. SABODA NA TAIMAKI WATA MATALAUCIYAR MATA LOKACIN DA NA KOMA".
Allahu akbar, Shin 'dan uwa Sau nawa ka bada sadaqa a rayuwar nan ta duniya?
Hakika An karbo Hadisi daga Abu Huraira (rta) yana Cewa, Manzon Allah (Saww) Yace, Sadaqa bata rage yawan dukiya, babu wani daga cikinku wanda zai yafewa 'dan uwansa face shima Allah ya masa gafara, sannan ba wanda zaiyi tawali'u (gaskantar da kai ga Allah) face Sai Allah ya daukaka darajarsa.
Don Girman Allah mu rika lura da Almajira da mabukata, kai kana zamanka hankali kwance kaci mai kyau ka sha mai kyau wallah daga cikin mabukatan nan akwai wanda bai ta'ba cin abinci mai dadi ko 'dan'dano ba.
A kula da mabukata ko za'a samu biyan bukata.
Jamilu Sani Rarah
Sat 13/02/2016
No comments:
Post a Comment