SAN WANI ABU GAME DA MUFTI MENK
*********
A musulunce idan aka kira mutum da suna mufti to ana nufin shahararren mai bada fatawa game da hukunce-hukuncen da suka shafi addinin musulunci.
Ba za'a bawa mutum mufti ba face sai ya kasance sananne a kowane fanni na musulunci. Hakika idan za'a bada wannan kujera ta mufti sai an tara dukkanin malaman kasar daga kowace akida. Idan har sun yarda to sai a bawa mutum wannan kujerar ta mufti. Idan kuma basu yarda ba sai mutum yayi zamansa a matsayin Shiekh.
Mufti menk cikakken sunansa Ismail sunan mahaifinsa musa Menk an haifeshi a garin Harare dake kasar Zimbabwe.
Ya fara hardar alqur'ani mai girma a gaban mahaifinsa tun yana da shekara tara a duniya ya samu nasarar hardace shi yanada shekara goma sha biyu (9 to 12 years).
Mufti menk ya samu ilmin addini sosai a wajen mahaifinsa shiek Musa wanda shima shahararen mai bada fatawa ne a kasar ta zambabuwie kuma mabiyin mazhabar Hanafi.
Daga nan mufti menk ya samu tafiya jami'ar musulunci ta dake saudia in da ya karanci fannin sharia wanda kuma dama shi ya karanta a wajen mahaifinsa.
Daga nan kuma ya koma kasar india ya karanci ilmi fiqhu (Jurisprudence), mufti isma'il ya kasance mai sauqin kaine da kuma girmama mutane ko wayanni iri (ma'abota musulunci da ma wayanda ba musulmai ba).
Dama ance 'daukaka bata zowa mutum a banza ba tare da anjarabeshi ba
A watan augusdin shekarar 2014 wasu gungun marasa imani suka kai gagarumin hari da mufti da niyar hallaka shi amma Allah cikin ikonsa ya tsare mufti daga kai dinsu.
Yanda abin ya faru, wata rana ne da yamma mufti menk yaje domin ya saye wani abu kamar yanda ya saba. Bayan ya kare sayayyar ya shiga motarsa direbansa ya ja mota sun fara tafiya kenan sai suka tarar da gungun wasu mutane suna jiran isowarsa domin su gaisar da shi.
Suna isa gun mutane sai Mufti ya saukarda glass din motarsa tare da yi musu sallama, hadi da mika musu hannu domin suyi musabuha.
Mufti na tsakiyar gaisawa da mutane sai wani mutum daga cikin mutanen ya fara zagensa yana Cewa, "KAI MAQIYI ANNABI NE KAFIRI KAWAI."
Mufti baice masa uffan ba a na haka sai kawai 'yan uwansa sukazo dauke da bindigogi da niyar su harbi mufti nan take mufti ya taka su mufti suka fice da gudu su kuma wayannan mutane suka rinka harbin motar, cikin tsarin Allah mufti ya tsira daga kaidinsu.
Babu shakka irin haka tayi ta faruwa ga mufti amma bai ta'ba nuna damuwarsa ko jin tsoro ba, haka kuma hakan bai hana shi ya'da da'awa ba.
Duk lokacin azumi mufti yakan ha'da kayansa yaje 'kauye me nisa daga birnin domin ya gabatar musu da tafsiri domin su san yana kaunarsu.
Wani abin mamaki ga mufti kuma idan aka gayyace shi ako wane gari yakanje kuma baya bukatar ace sai an tara masa kudade kafin yazo a gari komai nisan garin.
Abin mamaki kowa da inda yake karar da lokacinsa, wani a wajen alkheri wani kuma awajen sharholiya to shi mufti gaba daya lokacinsa da dukiyarsa ya sadaukar da sune akan 'daukaka kalmar Allah.
Kusan sati 3 ko ma fiye da haka mufti ya kasance a hanyar ya'da da'awa, daga kasar philipps ya taso yazo senghpor daga cen ya taso sai nigeria.
A wannan zuwa da yayi a nigeria ya so ya ziyarci wasu jahohi domin sada zumunci da kuma gabatar da lecture kamar yadda ya gabatar a kano, amma wasu abubuwa sun hana shi ciki wannan gurbi.
Ranar jumu'ah (jiya kenan. 05/02/2016) na bukaci ina son mu hadu da shi a zahirance nan take mufti ya bukaci in bashi number wayata domi munyi waya misalin karfe daya na rana a daidai lokacin da yake shirin tafiya gabatar da sallar jumu'ah a B.U.K da ke kano ya kirani muka dauki kusan mintuna 04 muna waya da shi.
Kwarjinin mufti ya sakani kasa sakin jikina inyi magana da shi yanda ya kamata, da ya fahimci haka sai ya gayamin cewa, idan har ina da wata bukata kada in damu zan iya tuntubarsa a koda yaushe da wannan layin da ya kirani da shi.
Daga baya na tura masa tex akan cewa muna gayyatarsa zuwa sokoto, sai bai min replay ba sai jiya assabar karfe takwas na dare mufti sai ga kiran mufti.
Bayan na 'dauka na masa gaisuwa cikin girmamawa ya gayamin cewa yaga tex messege dina amma kuma yana bani hakuri da sauran 'yan sokoto akan cewa ba zai samu zuwa ba amma ya min alkawari akan cewa nan da sati biyu zai sake tuntubata ya gani ko akwai yiwuwar ya zo sokoton.
In shaa Allahu mufti zai bar nigeria a yau lahadi tare da kewar kanawa, hakika mufti ya ji dadin zuwa kano tare da alfahari da matasan kano akan yanda ya ga suna so da kaunar addini.
Hakika na samu karantar wasu daga halayen mufti sosai da sosai. Na farko shahararren malamine, mai kuddine, ya shahara a wajen wa'azi ya shahara a wajen sarrafa yaren larabci da kuma turanci.
Mufti komai talaucinka koya shekarunka suke zaiyi mu'amula da kai ta kamala kamar yadda yake yi da kowa.
Wani abin sha'awa game da Mufti lokacin da zai fara gabatar da lecture sai da ya yi hausa.
Ina Rokon Allah ya albarka ce mu da ire-iren mufti a nigeria. Kuma Allah ya saka masa da mu kanmu da alkhairi duniya da lahira.
Jamilu Sani RARAH
Sun 07/02/2016.
No comments:
Post a Comment