Sunday, 14 February 2016

RANAR MASOYA TA DUNIYA

VALENTINE DAY BA DANI BA.
*********
Kasan Cewa Ruwayoyi sun banbanta game da ainahin dalilin da yasa ake wannan Biki na Ranar Masoya wasu suka ce;

Valentine sunan wani shahararren malamin kiristoci ne wanda ya rayu a shekaru masu yawa, zamanin Claudius II Sarkin Rome.

Wata Rana Sarkin Rome, Claudius II ya sanya dokar hana sojoji yin aure wai a ganinsa aure zai shagaltar da su, kuma ya kau da tunaninsu daga yaki.

Shi kuma Valentine ya bijire wa wannan doka ta Sarki, kuma ya ci gaba da daura wa sojoji aure a boye ba tare da an sani ba.

Da sarkin ya gano, sai ya jefa shi cikin kurkuku, kuma ya yanke masa hukuncin kisa.

Yana cikin kurkuku ne ya kamu da ciwon son `yar sarkin, amma a boye, duk da cewa haramun ne ya so wata mace ko kuma ya yi aure, a matsayinsa na babban malamin kirista, kasancewar dokokin kiristanci sun hana.

Kasancewar Sa Babban Malamin Kiristoci sarkin Romawa ya nemi Valentine ya bar kiristanci, ya bauta wa gunkin Romawa, shi kuma zai mai da shi daya daga cikin makusantansa kuma ya aurar masa da 'yarsa.

Shi kuma Valentine ya ki yarda da haka, Sai sarkin yasa aka kashe shi a ranar 14 ga Febreru 270 CE, a daren 15 ga watan Febrerun da aka saba yin wani bikin wai Lupercalis.

Daga nan aka canza sunan bikin ya koma ranar tunawa da Malam Valentine, wai saboda dagewar da ya yi a kan kiristanci, wasu kuma suka ce a'a saboda goyon bayan da ya nuna wa sojojin da suka fada cikin soyayya, har hakan ya kai shi ga rasa ransa.

Daga nan, sai Pope, shugaban kiristocin da ya gaji Saint Peter, ya mai da ranar 14 ga Febreru 270 CE a matsayin ranar bikin soyayya, kuma ya shar’anta wa duk kan kiristoci murnar zagayowar wannan rana a kowace shekara.

To In dai Haka ne Ni Jamilu 'dan Sani Jikan Adamu Jikan Isah me zai saka ni murnar wannan Rana?

Shin ko 'yan uwa zasu tuna da wani hadisin Annabi (Saww) wanda yake Cewa, KUYI SALLA DA TAKALMI KO SAU DAYA NE A RAYUWARKU DOMIN KU SA'BAWA YAHUDAWA?

A wani hadisi kuma yace, KADA KU ASKE GEMU KU BAR GASHIN BAKI DOMIN YAHUDAWA NE KE YIN HAKA.

A wani hadisin kuma, umurtar mu yayi da cenja kalar farin gemen mu domin mu sa'bawa yahudawa.

Bikin valantine biki ne da ya kunshi kamanceceniya da mushrikan Romawa da kuma tarayya da kiristoci.

Sanin kan ku ne Yin kamanceceniya da kafirai ko tarayya da su a cikin addininsu ko akidarsu ko ibadarsu ko wata al’ada da ta kebanta da su, haramun ne Ina Rokon Matasa da kauracewa wannan Bikin.

#NoForValanTineIamMuslim.

Jamilu Sani RARAH
14/02/2016.

No comments:

Post a Comment