Saturday, 23 January 2016

SADAKIN MILIYAN 12 ADDINI KO WAYEWA?

YIN SADAKI MILION 12 ADDINI KO WAYEWA?
******************************************

Yana da kyau Idan kana Shugaba ka rika yin abinda idan Kayi shi talakawa da wayanda ke Biye da kai zasu kwaikwaya domin daukar darasi daga gareka.

Nayi Mamaki ainun Lokacin da naji cewa Naira na Gugar naira har naira Million goma sha biyu (12 Million), aka yi sadakin 'yar Galadiman Zazzau kuma ta hannun Sarkin Zazzau

Hakika indai ta tabbata haka akayi sadakin to kuwa Sarkin Zazzau ya fita daga Jerin Sarakunan Musulmai. Domin wannan Ruguza Musulunci ne.

Dalilina anan Shine duk wani musulmi yana son Annabi (saww) tare da kwaikwaya daga gare shi. Domin nuna biyayya da kauna a gareshi.

Shin ko 'yar Sarakai tafi Nana Fatima (RA) matsayi da daukaka ne?

Idan ana maganar kyaune ko matsayi a duniya idan aka kawo Nana Fatima (RA) to kuwa Sai dai a shafe fatiha a tashi (domin itace KHAIRUL NISA'IL ALAMINA).

Bayan kasancewarta Mace mai matsayi kuma kyakykyawa haka ma Mahaifinta yafi kowa matsayi a duniya da lahira.

Lokacin da Sayyidina Aliyu (RA) ya yanke hukuncin zuwa neman Auren Nana Fatima (RA), Daga nan ya tashi ya yi wanka sannan ya yi alwala ya kuma yafa mayafinsa ya yi nafila raka'a biyu, ya nufi wajen Annabi (Saww) a lokacin Annabi (saww) yana dakin Ummu Salama (RA).

Da Isar Sayyidina Aliyu Ya yi sallama, Manzon Allah (saww) ya amsa masa, Sai Sayyidina Aliyu (RA) ya zauna a gaban Manzo ya dukar da kai kasa; ganin haka sai Annabi ya ce masa: "Ya Aliyu, Ka zo da wata bukata ce?" sai Sayyidina Aliyu ya ce: "Na'am, na zo neman auren 'yarka Fatima ne; ko za ka aurar min da ita Ya Manzon Allah?"

Ummu Salama ta ce: "A lokacin sai na ga fuskar Manzon Allah ta cika da annuri na farin ciki da murna,

Sannan ya kalli Sayyidina Aliyu ya yi masa murmushi. Daga nan sai Manzon Allah (saww) ya shiga wajen Nana Fatima ya ce mata: "Ali bin Abi Dalib, wannan da kika san kusancinsa da darajarsa a Musulunci ne, ya zo yana zance a kan al'amarinki (wato yana neman auren ki).

Hakika kuwa da ma ni na roki Ubangijina da ya aurar da ke ga mafi alherin talikanSa. To me kike gani?" Sai ta yi shiru.

Sai Manzo Allah (saww) ya fita yana cewa: "Allahu Akbar! Shirunta yardarta ne". Sannan ya cewa Sayyidina Aliyu (RA): "Ya Aliyu, shin kana da wani abu
da zan daura maka aure da shi (sadaki)?".

Sai Sayyidina Aliyu (RA) ya ce: "Sai takobina da garkuwata, sai kuma rakumina na ban ruwa ", (a wata ruwayar an ce doki ne maimakon rakumin).

Sai Manzon Allah (Saww) ya ce: "Amma takobinka kana da bukatarsa, za ka yi yaki da shi a tafarkin Allah kuma ka kashe makiya Allah da shi.

Rakuminka kuma kana shayar da (gonar) dabinonka da shi, haka kana daukar kaya da shi,
kuma yana daukarka a tafiye-tafiyenka.

Don haka je ka yi yadda za ka yi da garkuwarka". Sai Sayyidina Aliyu (RA) ya je ya sayarwa Sayyidina Usman bin Affan (RA) da garkuwarsa a kan farashin dirhami 480, sai ya kawo wa Manzon Allah (saww).

Daga nan Manzon Allah (Saww) ya sanar da Musulmi zancen auren. To Sadakin Nana Fatima (RA) kenan fa. Ina ga diyar Galadiman Zazzau da ba 'yar kowa ba?

Hakika bayan wannan akwai hadisi sukutukum wanda Manzon Allah (saww) yake cewa, Aure Mafi albarka shine wanda sadakinsa ya zamo mafi sauki".

Har An Ruwaito Cewa Sahabbai (RA) suna Cewa, "FIYAYYEN AURE SHINE AUREN UMMU SULMAN (RA), DOMIN ITA SADAKINTA MUSULUNCI NE."

Ummu Sulman Itace Mahaifiyar Anas Bin Malik lokacinda mahaifinsa ya rasu, taqi yin aure har Saida Abu Talha ya fito yana Sonta sannan ta amince zata aure shi amma da sharadi zaya Musulunta (Musuluntarsa Shine Sadakinta).

Bayan manyan attajirai da Masu mulki da Sadaukai sunyi ta fito mata amma taki amincewa dasu.

Hakika Am Very Disappointed akan Masarautar Zazzau Sun Ci Mutuncin Addinin mu in dai hakan ta tabbata akan wannan Sadakin.

Domin Ko Rantsuwa nayi bana bukatar kaffara cewa, A cikin dangin angon ko dangin Amaryar akwai wanda ke Bukatar Taimakon Dubu goma (10 thausand) ta gagare shi.

Akwai ma wanda Ke neman abinda zaici, haka kuma akwai masu neman Tallafi domin Suyi karatu ko auren.

A karshe Ina Kira ga Matasa Wallahi duk inda kaje neman Aure aka zabga maka Sadaki Mai yawa ka barta ka nemi wata, domin Muddin Sadaki yayi Yawa a aure to An riga da an debe Albarkar Auren. Kuma Allah yana Fushi da kai da Iyayen Matar.

Babu Shakkah da Wani Attajiri ne ya bada 'yarsa akan wannan sadakin ba zamu damu ba, kasancewa baya amsa suna da Jagorar Musulmi.

Da Wannan nake Addu'ar Allah ya Shiryemu, Allah kuma Ya jikan Marigayi Jafar 'dan Ishaqa, domin a lokacinsa Zazzau take masarauta me bin koyarwar Musulunci.

 Jamilu Sani RARAH
Wed 13/01/2016.'

GUDUMMAWAR FINAFINNAI

DUNIYA INA ZAKI DAMU NE?
****************************

Kalubane Ga Malammai Da Masana Tare da Iyaye da Abokanai da Shuwagabanni.

Wannan Labarin ya Saka ni Jin haushi kuma na Rasa a wajen wa Zan huce Haushina? kuma laifin wa zan gani?

Wani mutum ne 'dan Asalin karamar hukumar Rogo a Jihar Kano , ya yi aure amma sai ya kasa gusar da budircin matarsa.

Sai ya je ya samu Wani Abokinsa akan ya taimakeshi ya je ya gusar masa da Budurcin na Amaryarsa, shi kuma abokin ya aminta da hakan amma da Sharadin zai bashi Naira dubu da dari biyar (1,500).

Da abokin angon ya je zuwan farko shima sai ya dawo ya nuna aikine mai wuya don haka sai an kara masa Naira 1,000.

Angon ya amince, da ya sake komawa zuwa na biyu sai aka yi sa'a sannan ya zo ya shaida masa cewa an riga an gama ko mai don haka ya bashi kudinsa.

To anan ne Angon ya bashi Naira 1,500 maimakon 2500, tare da bashi hakuri.

Shi kuma ya nuna sam ba zai yarda ba wannan ba sai an biya shi kuddinsa duka.

Anan ne amarya ta bukaci da ya yi hakuri tunda ai ko babu komai shima ya ji dadi. Wannan labarin ya sakani masassara (zazzabi tare da jin taici).

Shin laifin Waye Anan? Babu shakkah Laifi na farko na daura shi kaco kan akan Iyaye domin 'ya'ya kiwo ne Allah ya bawa iyaye, kuma ya tanadi wata ukuba mai yawa ga wanda ya kasa kula da wannan hakkin.

Manzon Allah (saww) na Cewa,

ﻣﺎ ﻣﻦ ﻋﺒﺪ ﻳﺴﺘﺮﻋﻴﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺭﻋﻴﺔ ﻳﻤﻮﺕ ﻳﻮﻡ ﻳﻤﻮﺕ ﻭﻫﻮ ﻏﺎﺵ ﻟﺮﻋﻴﺘﻪ ﺇﻻ ﺣﺮﻡ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺍﻟﺠﻨﺔ

Ma'ana, Babu wani bawa da Allah zai ba shi kiwo, ya mutu ranar mutuwarsa yana mai algushu ga abin kiwon da Allah ya ba shi face Allah ya haramta masa shiga Aljannah.

Babu ko Shakkah Wannan hadisin kalubale ne ga iyaye domin daga cikin Hakkokin 'ya'ya akan iyaye akwai, Tarbiyantar da su, Kaisu Makaranta, Ko ya musu Sallah, tare da zabar musu mata.

Wasu daga cikin Iyayen Yanzu basa kula da karatun 'ya'yansu na Addini sai dai na Boko kawai.

Laifi na Biyu kuma na jingina shi ne ga malamai, Domin da ace Malamai suna, Sanarda dalibbansu Hanyoyin zama da miji ko Mata.

Tare da Sanar dasu Abubuwan da Saduwar Aure ke bukata da ma wanda bata bukata.

Hakika Wannan Kalubale ne ga Malamai (na boye Ilmi), Domin Annabi (Saww) Yace,

ﺃﻳﻤﺎ ﺭﺟﻞ ﺃﺗﺎﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻤﺎ ﻓﻜﺘﻤﻪ، ﺃﻟﺠﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﺑﻠﺠﺎﻡ ﻣﻦ ﻧﺎﺭ.

Ma'ana "Dukkan mutumin da Allah ya bashi ilmi kuma ya
Boyeshi to Allah zai yi masa linzami da wuta a Ranar Alkiyama.

ALLAH YA KIYAYE MU DAGA AIKIN RASHIN ILMI TARE DA BOYE WA JUNA DUK WANI ABU DA MUKA SANI.

Jamilu Sani Rarah
Sun 17/01/2016.

DUNIYA INA ZAKI DAMU?

DUNIYA INA ZAKI DAMU NE?
****************************

Kalubane Ga Malammai Da Masana Tare da Iyaye da Abokanai da Shuwagabanni.

Wannan Labarin ya Saka ni Jin haushi kuma na Rasa a wajen wa Zan huce Haushina? kuma laifin wa zan gani?

Wani mutum ne 'dan Asalin karamar hukumar Rogo a Jihar Kano , ya yi aure amma sai ya kasa gusar da budircin matarsa.

Sai ya je ya samu Wani Abokinsa akan ya taimakeshi ya je ya gusar masa da Budurcin na Amaryarsa, shi kuma abokin ya aminta da hakan amma da Sharadin zai bashi Naira dubu da dari biyar (1,500).

Da abokin angon ya je zuwan farko shima sai ya dawo ya nuna aikine mai wuya don haka sai an kara masa Naira 1,000.

Angon ya amince, da ya sake komawa zuwa na biyu sai aka yi sa'a sannan ya zo ya shaida masa cewa an riga an gama ko mai don haka ya bashi kudinsa.

To anan ne Angon ya bashi Naira 1,500 maimakon 2500, tare da bashi hakuri.

Shi kuma ya nuna sam ba zai yarda ba wannan ba sai an biya shi kuddinsa duka.

Anan ne amarya ta bukaci da ya yi hakuri tunda ai ko babu komai shima ya ji dadi. Wannan labarin ya sakani masassara (zazzabi tare da jin taici).

Shin laifin Waye Anan? Babu shakkah Laifi na farko na daura shi kaco kan akan Iyaye domin 'ya'ya kiwo ne Allah ya bawa iyaye, kuma ya tanadi wata ukuba mai yawa ga wanda ya kasa kula da wannan hakkin.

Manzon Allah (saww) na Cewa,

ﻣﺎ ﻣﻦ ﻋﺒﺪ ﻳﺴﺘﺮﻋﻴﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺭﻋﻴﺔ ﻳﻤﻮﺕ ﻳﻮﻡ ﻳﻤﻮﺕ ﻭﻫﻮ ﻏﺎﺵ ﻟﺮﻋﻴﺘﻪ ﺇﻻ ﺣﺮﻡ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺍﻟﺠﻨﺔ

Ma'ana, Babu wani bawa da Allah zai ba shi kiwo, ya mutu ranar mutuwarsa yana mai algushu ga abin kiwon da Allah ya ba shi face Allah ya haramta masa shiga Aljannah.

Babu ko Shakkah Wannan hadisin kalubale ne ga iyaye domin daga cikin Hakkokin 'ya'ya akan iyaye akwai, Tarbiyantar da su, Kaisu Makaranta, Ko ya musu Sallah, tare da zabar musu mata.

Wasu daga cikin Iyayen Yanzu basa kula da karatun 'ya'yansu na Addini sai dai na Boko kawai.

Laifi na Biyu kuma na jingina shi ne ga malamai, Domin da ace Malamai suna, Sanarda dalibbansu Hanyoyin zama da miji ko Mata.

Tare da Sanar dasu Abubuwan da Saduwar Aure ke bukata da ma wanda bata bukata.

Hakika Wannan Kalubale ne ga Malamai (na boye Ilmi), Domin Annabi (Saww) Yace,

ﺃﻳﻤﺎ ﺭﺟﻞ ﺃﺗﺎﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻤﺎ ﻓﻜﺘﻤﻪ، ﺃﻟﺠﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﺑﻠﺠﺎﻡ ﻣﻦ ﻧﺎﺭ.

Ma'ana "Dukkan mutumin da Allah ya bashi ilmi kuma ya
Boyeshi to Allah zai yi masa linzami da wuta a Ranar Alkiyama.

ALLAH YA KIYAYE MU DAGA AIKIN RASHIN ILMI TARE DA BOYE WA JUNA DUK WANI ABU DA MUKA SANI.

Jamilu Sani Rarah
Sun 17/01/2016.

MUN SAKE SAKA KAFAR WANDO DAYA DAKU 'YAN SHI'A

MUN SAKE SAKA KAFAR WANDO DAYA DAKU
********************************************

Ina Godiya Ga Allah da Ya tasheni Lafiya, Haka kuma Ina Tare da Allah ya Isa Ga 'yan Shi'ah.

 Daga Buda wayata naga Whatsapp dina ya nuna min an sakani a wani Group wai shi (ZAMANI), ba zance duka ba, amma ina kyautata Zaton duk 'yan Shi'a ne a ciki.

Suna Ta Zagin Shugaban Kasa Buhari tare da La'antarsa daga Karshe Idona suka dorani a wani Rubutu mai ban Tsoro da Firgici, Title din Rubutun "YADDA ABUBAKAR DA UMAR DA USMANU SUKAYI YIN KURIN YIWA NANA FYADE" wa'iyazu billahi.

Nikam Na Fita da gudu ba tare da dubawa ko nasan wani daga cikinsu ba.

Ya Allah ka isarwa Bayinka (HULAFA'U RASULU) gareku 'yan Shi'ah, Haka kuma Allah ya Taimaki Buhari a kanku munafukkai.

Kuma daga Yau Balbalin tona Muku asiri ya Kankama muje Zuwa 'ya'yan BAYAHUDE IBN SABA'I.

Jamilu Sani RARAH
Tue 19/01/2016.


BAN BANCIN DA KE TSAKANIN MU DA 'YAN SHIA

BANBANCIN DA KE TSAKANIN MU DA SHI'A
*******************************************
Babu Shakkah akwai wasu banbance-banbance dake tsakanin duk musulmi da 'yan Shi'ah, ga su kamar haka;

-Musulmi duk ya yarda da Ingancin Alqur'ani, ya yinda mabiya shi'a ke hangen an rage wani abu daga cikinsa lokacin harhada shi.

-Musulmi duk ya yarda da hadisan da aka tabbatar da sahihancin Ruwayoyinsu, Yayin da mabiya Shi'a basu yarda da hadisan da ba ahlul bayti ne suka ruwaito su ba.

-Musulmi duk ya yarda Cewa, Matan Annabi (saww) iyayensa ne, yayin da 'yan shi'ah ke ganin Nana A’ishatu da Nana Hafsah a matsayin kafirai (wa'iyazubillah)

-Musulmi duk ya yarda da Halifancin khalifofi guda hudu (Abubakar, Umar, Usman da Aliyu (RA)), yayin da 'yan shi'ah basu yarda da wayannan khalifofi ba in baicin na Sayyidina Aliyu (RA).

-Musulmi duk ya yarda da Ganin Allah a Lahira yayinda 'yan Shi'ah basu yarda ba.

-Musulmi duk yana da yakinin cewa kowa zai iya shugabantar daular musulunci matukar ya cencenta, Yayin da Shi'awa ke ganin babu wanda ya cancanci mulkar daular musulunci baicin Ahlul baiti.

-Musulmi duk ya yarda da ba'a had'e jam'in sallar azahar da la'asar amma su yan shi'ah sun yarda ana hadewa.

-Musulmi duk ya yarda da Dukkan kasa Mai tsarki ana sujuda akanta, yayinda 'yan shi'ah ke ganin duk kasar duniya bata da tsarki in baicin ta karbala.

-Musulmi duk bai yarda da boye addininsa ba amma su 'yan shi'a su yarda da takiya (boye addininsu).

-Musulmi duk bai yarda da arawa Abokinsa matar shi ya kwana da ita ba, yayinda 'yan shi'ah ke ganin wannan a matsayin wata hanyar samun lada.

Babu shakkah wannan sune manyan Banbancin musulmi da 'yan Shi'ah, idan har ka yarda da abu daya anan na 'yan Shi'ah to kaima 'dan Shi'ah ne, Allah ya shiryeka.

Allah ka datar damu a duk inda muke.
Jamilu Sani RARAH 
Thu 17/12/2015.

NAGERIA KASARMU A GADO

NIGERIAR KENAN
*****************
Wani Bawan Allah ne a karamar Hukumar Sabon Birni dake nan Sokoto yayi noma ya tara kuddi kusan dubu saba'in (70,000), bayan ya tarasu sai ya je ya nemi daya daga cikin Clark (masu bada albashi) na local Govnt dinsu, ya bashi wayannan kuddi dubu Saba'in ya sayi opper ta aiki wacce za'a rik'a bashi dubu takwas (8,000) a kowane wata.
 
 Wannan bawan Allah yaci gaba da karbar albashinsa dubu takwas a kowane wata, yana karbar wayannan kuddi kwatsam sai aka kori wannan Clark din daga local Govtmt din.

Wata ya cika, wannan bawan Allah yaje karbar kuddinsa na albashi kamar yanda ya saba (ba tare da ya san an cenja Clark ba).

Lokacin da yazo karbar wayannan Kuddi sai Sabon Clark din yace, Shi sam ba zai bashi kuddi ba, saboda dalilai Guda 2, Na farko baya zuwa aiki, na biyu kuma bai yi karatun boko ba.

Wannan bawan Allah yace, Shi ba'a yi dashi akan Cewa, ya rika zuwa aiki ba, haka kuma ba'a gaya masa sai 'yan boko ake bawa albashi ba shi dai ya san cewa, Sayen Opper yayi da kuddinsa.

Sun dauki lokaci suna wannan Rigima Cen dai Clack din ya amince zai bashi albashin amma da sharadi sai ya yi masa turanci.

Wannan bawan Allah yayi akan ya bashi albashinsa ya wuce, shi ma clarck dinsa ya matsa akan sai ya masa turanci sannan zai bashi albashin.

Lokacin da Wannan bawan Allah ya fahimci wannan Clack din da gaske yake, Sai ya d'anja nunfashi Sannan YaCe, "...HUMMIMM TOH! FINAL"

Sai wannan Clack din maimakon dubu takwas (8,000), sai ya bashi dubu hudu (4,000).

Shin Turancin wannan bawan Allah yayi kuwa?

A karshe Ina neman Alfarma ga Malam, Shiaek, Dr. Muhammad Sanib Umar Rijiyar Lemu akan ya warware mana wannan mas'ala, Shin Su masu Sayen Wannan Opper ta aiki halal suke ci? Shin Dole ne Sai 'dan Boko kadai ke da hakki akan Albashi?

A karshe Ina Jan hankalin Ma'aikata da su san Hakki tare da Amanonin da ke kansu, domin Allah (swt) Yana Cewa,

ﺇﻥَّ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺄﻣﺮُﻛﻢ ﺃﻥْ ﺗُﺆﺩُّﺍ ﺍﻷﻣﺎﻧﺎﺕ ﺇﻟﻰ ﺃﻫﻠﻬﺎ ﻭﺇﺫﺍ ﺣﻜﻤﺘﻢ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﻥْ ﺗﺤﻜﻤﻮﺍ ﺑﺎﻟﻌﺪﻝ ﺇﻥَّ ﺍﻟﻠﻪ ﻧﻌﻤّﺎ ﻳﻌِﻈﻜﻢ ﺑﻪ ﺇﻥَّ ﺍﻟﻠﻪ ﻛﺎﻥ ﺳﻤﻴﻌًﺎ ﺑﺼﻴﺮًﺍ
 
 Ma'ana: "Lallai Allah yana umurtarku da ku bada amanoni zuwa ga ma'abotansu, kuma idan za kuyi hukunci tsakanin mutane ku yi hukunci da adalci, lallai Allah Madalla da abinda yake muku umurni da shi, lallai Allah ya kasance mai ji ne mai gani" (Suratul Nisa'i ayata 58).

Allah yasa mu dace.
Jamilu Sani RARAH
Wed 16/12/2015.

Tuesday, 12 January 2016

KUSKUREN MU A 2009

KUSKUREN MU A SHEKARAR 2009
*******
Shekaru biyar da Suka gabata, Sitayrin Motar wani Aminina ya kulle a daidai lokacinda ya juya Sitayrin domin Shiga kwana, bai an kara ba kawai Sai jin motar yayi ta mazgi wani katon Iccen Darbejiya (Neem Tree).

Wanda wannan yayi Sanadiiyar lalacewar Gaban motar Sosai da sosai, muka ja motar muka kai wajen gyara.

Wannan daliline yasa muka Ari Mashin hannun wani Abokin mu domin yin Zirga-Zirga zuwa wajen gyaran motar. Ai kuwa ashe rabon ayine.

Domin Wannan Mashin din bai kwana biyu a hannun mu ba aka dauke shi, ganin an dauke shi a hannun mu sai wasu suka bamu shawara akan kada
mu bayyana bacewar Mashin din kowa yaji muyi neman sa a boye.

Haka kuwa akayi mukayi ta neman wannan mashi lungu da sako amma ba labari, a haka har muka kai wajen masu gyaran mashin a tunanin mu ko za'a kai shi wajen a cenja masa fasali.

Nan dai muka duba ko ina amma bamu samu ganin mashin din ba, mun fito zamu wuce kenan Sai muka hadu da wani yaro (ga alamu Gyaran mashin yake).
Anan dai Muka gaisa da shi, Sai ya dubi wanda muka ari mashin dinsa yace masa, "ALMUSTAPHA INA MASHI?"

Almustapha Wanda Shi ke da mashin din da aka dauke Yace da Shi, "MASHIN YANA HANNUN WANI" (Ba tare da ya gaya masa 'dauke mashin din aka yi ba).

Anan dai Mukayi sallama da yaron Muka wuce, bayan mun wuce ne muka tambayarsa ina yasan wannan yaro? Shine yake gaya mana cewa, ai shike masa gyaran mashi din.

Muka ce ai kuwa irinsa bai kamata ka boye masa da'uke mashin din akayi ba, anan muka juya domin a gaya masa abinda ke faruwa, domin yas
ganshi.

Ai kuwa Muna zuwa Sai yake gaya mana cewa, Yanzu ko ya ga Mashin din an wuce da shi, nan muka bi hanyar da aka bi da mashin din tare da shi ko zamu samu ganin mashin din.

Amma ina mashin yayi nisa, har muka gaji da nema a karshe dai muka dauki hukunci Muka saya masa wani mashin din, har yanzu dai babu zancen ganin mashin din.
Shekaran Jiya da Rana Wata 'yar Uwata ta fita kasuwa da motar mahaifiyarta.

Kwatsam tana fitowa daga kasuwa sai ta tarar an dauke motar (anyi awon gaba da motar).

Nan take aka gayawa dukkan makusanta (ma'ana 'yan uwa na nesa dana kusa) akan sace wannan motar da akayi.

Ai kuwa da Allah yasa raboce cikhn awoyi Shida (6 hours) aka ga motar a hanyar Sheme (dake Jahar Katsina).
Babu Shakkah Saurin bayyana 'bacewar abu ga 'yan uwa kan taimaka ainun domin kabke 'barawon abin.

Hakika da Allah ya kaddaremu da gayawa Mai gyaran mashin din 'bacewar mashin din da Mun samu kama 'barawon da hannun mu, amma a tunanin mu kar aga mun cika raki muka boyewa jama'ah sace Mashin sai muka yi rashin sa'ar kama 'barawon mu.

A karshe ina bamu shawarar idan abinn mu ya 'bata to mu gaggauta shelantawa makusantan mu wayanda ke gari da ma wayanda basa gari.

Babu shakka wannan hanyar zata taimaka mana sosai waj
kame 'barayin mu.

Ya Allah ka Shiryarda mu akan gaskia.

Jamilu Sani RARAH
Mon 11/01/2016.

BUHARI YA RAINA HANKALIN MU DA SUNAN BINCIKE

BUHARI YA RAINA HANKALIN MU DA BINCIKE
**********
Aka Ce Idan kanada Gaskia to kar kaji tsoron Magana ko a gaban waye ko waye shi.

Labari Ya Isheni Cewa, Hukumar EFCC ta sallami Lawal Jafar Isah wai don ya bada kaso 60 cikin 100 na kuddin da ake tunanin ya handame da Jama'ar Nigeria.

Lalle Idan hakane ta tabbata Nigeria ba zata gyaru ba a hannun Shugaba Buhari domin kuwa Sam ba Adalci yake nufi ba a wannnan Lamari.Hakika duk Mulkin da Ba'a adalci a cikinsa to Mulkin Baza'a samu nasara a cikinsa ba, ko da kuwa Shugaban Cikakken Musulmi ne.

Ina da Tabbaci akan Duk Mulkin da ake adalci a cikinsa Za'a dade ana cin moriyar Mulkin koda na kafiri ne, mu dau darasi daga America.

Na san baku da bukatar Sanin Waye Lawal Jafar Isah, du da haka zan karaa aska muku domin ku kara sanin waye Shi.

Lawal Jafar Abokin Shugaba Buhari ne na Kud da kud, kuma tare suke Siyasa tun tali-tali, hakika idan har an Sake Lawal Jafarr to Kuwa Babu Sauran "MAGANAR CHANGE A NIGERIA" tabbas nageria an gama yaudarar ku da Fuskar Salihan Bayi domin ayi Ramuwar gayya ga 'yan adawa.

Allah ya taimaki duk Mai Gaskia ya bayyanar da duk Mai karya.

Jamilu Sani RARAH
Mon 11/01/2016.

Saturday, 9 January 2016

HANKALINA YA TASHI DANA GA JAHILCI KARARA

HANKALINA YA TASHI DANA GA JAHILCI KARARA
**********
Sako Zuwa Ga Dalibban Ilmi (Almajirai masu neman Ilmi), Kuma Wannan Sakone Ga Malamai (Masu karartarwa).
.
Hakika An turomin Wani Vedio a Whatsapp, babu shakkah Hankalina ya tashi dana kalli vedion.
.
A Vedion an nuna wani Zindikin Malami a saman Kujera yana Alwala, wasu almajiransa Suna kewaye da shi suna jiran ya idar da Alwalar.
.
Bayan yakai wajen wankin Kafafuwa (ya zuba ruwa yana wanke wa), kawai sai Wayannan Almajiran nasa suka tara hannayensu suka shanye ruwan tare da shafe ragowar Ruwan a jikinsu (da sunan Neman Albarka). Wa'iyazubillah.
.
Kirana ga Dalibban Ilmi shine, Hakika Duk duniya ba'a ta6a Malami masani Mai albarka ba kamar Annabi (saww).
.
Hakika Fitsarin Ma'aiki (saww), Maganine, Zufan Jikinsa yafi Miski Kamshi, hakika Yawun Bakinsa (saww) Maganine.
.
Amma duk Irin Wannan Baiwar ta Fiyayyen Halitta (saww), Ya hana SahabbanSa (RA) tashi tsaye idan Suka ganshi.
.
Hakika yana Mu'amula da su ta aminci tare da Shiryar da su bisa hanya madaidaiciya.
.
Hakika yana da matukar kyau Girmama Malami, amma Sam ba irin wannan ba.
.
KUSANI NI JAMILU SANI RARAH BANA DURKUSAWA MUTUM KOMAI ILMINSA KO KUDDINSA KO MATSAYINSA.
.
Hakika Ina Rusunawa In gaida mai kuddi ko Ilmi amma ba na kaiwa har kas, don haka Kaima Ina so kaima mai karatun wannan rubutu ka zamo haka (kamarni).
.
Nima kuwa na Kwaikwayi Wannan ne daga Babban Shahabin Manzon Allah (saww), wato Abdullahi Bin Abbas (RA).
.
IBN ABBAS (RA) shine wanda a lokacin aikin Hajji ya Sumbaci HAJRUL ASWAD (bakin dutsin da ke dakin Ka'aba), Wanda Sumbatarsa na daya daga cikin Farillan aikin hajji.
.
Bayan Ya Sumbaci Dutsin Sai Yace, NA SUMBACE KA NE KAWAI DON ALLAH YAYI UMURNI A YI, AMMA NI NA SAN BAKA CUTARWA KUMA BAKA DA WANI TAIMAKO DA ZAKA IYA MINI.
.
Hakika wannan ya nuna mana Girmama abu Fiye da Kima na da Matsala.
.
Sannan Ku kuma malamai Kuji tsoron Allah jallah wa Azzah, domin Allah zai tambayeku akan Abinda Kuka koyar tare da Aikatawa.
.
Allah ya ganar damu Gaskiya Ya kuma bamu ikon Binta, Ya nuna mana Karya ya bamu ikon kauce mata.
.
Jamilu Sani RARAH.
Fri 08/01/2016.