Dukkan dangin Yabo da godiya da kirari su kara tabbata ga Allah (Swt),
Salati da Sallama su kara zuwa ga Shugaban Annabawa Fiyayyen dukkan
Halittu Muhammad 'dan Abdullahi (Saww).
Bayan haka Wannan rubutu zai haska ma akan Halaccin yin Mauludi ko kuma haramcin Yinsa a mahanga ta addini.
Farko hakika a cikin Qur'ani mai girma babu wuri daya In da Allah (Swt) yayi umurni da ayi Mauludi
Annabi (Saww) da kansa baiyi Mauludi ba kuma bai Umurci wani daga cikin Sahabbansa Suyi Mauludi ba.
Sai dai ma Annabi (Saww) ya Umurci Sahabbansa da kada su yi koyi da
Nasara Domin Sune ke yin Biki domin Annabi Isa (Alaihis Salam).
Yace, "Kada ku rike ni kamar Yadda Nasara suka riki d'an Maryam. Ni
bawa ne. Saboda haka kuce dani Bawan Allah kuma Manzon Allah (Saww)."
(Buhari).
Ya tabbata Manzon Allah (Saww) ya kan dauki ranar haihuwarsa Ranar Ibada ba ranar Biki ba kamar yanda yazo a hadisi.
An Tambaye shi (Saww) game da Azumin Litanin da yake yi, sai yace,
itace Ranar da aka haifeni kuma itace ranar da aka bijiromin da alkawali
(Muslim, al-Nisaa’i da kuma Abu Dawood).
Baya ga haka mun san Cewa, Sahabbai (RA) sun fimu So da Kaunar Annabi (Saww).
Sayyidina Abubakar (RA) Wanda Yafi kowa kusanci ga Annabi (Saww) ba'a samu yayi Mauludi ba.
Ko An samo a littafan Tarihi Cewa, Sayyidina Umar (RA) yayi Mauludi ko Sayyidina Usman ko Aliyu (RA)?
Ko an samu daga Cikin 'ya'yan Annabi (Saww) Wani yayi Mauludi? Shin
basu san da mauludin bane ko kuma Son Annabi (Saww) ne basayi?
Bayan Sahabbai Shin Imam Abu Haneefah, Maalik, Shaafi’i, Ahmad, al-Hasan al-Basri, Ibn Seereen an samu Waninsu yayi Mauludi?
An samo a hadisi Ingantacce daga Ma'aiki (Saww) Cewa, Annabi (Saww)
yace, Mafifitan mutane daga cikin Al'ummata sune Karni Na Farko
(Sahabbai Kenan), Sannan masu bi musu (tabi'ai Kenan), Sannan Masu bi
musu (Tabi'ut tabi'una Kenan)" (Bukhari, Muslim Da Tirmiziy Suka
Ruwaito).
Idan Zamuyi duba Kenan Wannan Karni Namu Yana Kasa Kwarai game da Samun fifiko kamar yadda Annabi (Saww) Ya Fada.
Shin Ba Akan soyayya bace ake yin mauludin ba? Shin munfi Sahabbai
Soyayyar Annabi (Saww) NE? Domin kuwa daga Cikin Sahabbai akwai Wanda
Manzon Allah (saww) ya kwanta barci akan cinyarsa lokacin da suke cikin
wani Kogo.. Sai Shi wannan sahabin ya rika yagar rigarsa yana tottoshe
ramukan da suke cikin kogon. Amma duk da haka akwai sauran wani rami
wanda bai samu abin tosheshi ba.
Chan sai ga wani Maciji ya
leko ta cikin wannan ramin yana so zai fito. Don haka sai ya sanya
Qafarsa ya toshe ramin don kar Macijin nan ya fito ya chutar da Manzon
Allah (saww). Macijin nan yayi ta cizonsa yana zuba masa dafi. Amma duk
da haka bai motsa ba, don kar ya tashi Manzon Allah (saww) daga Bacci.
Wannan Sahabi Shine Sayyidina Abubakar.
Shine Makusancin Manzon
Allah (Saww) na Kusa da Kusa Kai akwai ma Lokacin da Manzon Allah
(saww) yazo gidan Sayyiduna Abubakr (ra) yace masa “ALLAH YA UMURCENI
INYI HIJIRA”.
Sai Sayyiduna Abubakar yace “Ina fatan tare dani
zaka tafi?” Sai Ma’aiki yace masa “KWARAI KUWA. ALLAH YACE MIN IN TAFI
TARE DAKAI”. Sai Sayyiduna Abubakar ya fashe da kuka don murna Ganin
Allah ya zabe shi ya Raka Wanda Yafi so a Duniya Fiye da Komai.
Kai Hatta Annabi (Saww) An tambayeka Shi Duk Duniya Waka Fi so Yace,
Aisha, Aka sake Tambayar say Cikin Maza fa? Yace, "Mahaifinta (Wato
Abubakar)".
Amma Duk Irin Wannan Soyayyah dake Tsakanin
Sayyidina Abubakar da Manzon Allah Bai sa Sayyidina Abubakar Yayi
Mauludi Don tunawa Da Annabi (Saww) ba.
Bayan Sayyidina
Abubakar (rt), Sayyidina Umar (ra) na daya daga cikin zaratan mayaka
wadanda su kayi ruwa da tsaki wajen kare martabar Musulunci da ruguza
abokan fadansa.
Ya kusanci Manzon Allah (Saww) har ya kai
matsayin wazirinsa na biyu. Bayan tsabar Soyayyar da Sahabi Umar Ke yiwa
Annabi haka Allah ya karrama shi da surukuta da Manzon Allah (Saww)
inda Manzon Allah ya nemi auren 'yarsa Hafsah, aka ba shi ita, aka daura
aure, sai ta zama ita ce ta uku. Bayan Sayyidina Abubakar Yayi wafati
Sayyidina Umar NE Yayi khalifanci Amma Baiyi Mauludi ba Bai Kuma yi
Umurni da ayi Mauludi ba.
Sayyidina Usmanu Bayan zamansa Sahabi
a gun Annabi (Saww) Kuma surukine na Annbi (Saww) domin ya auri 'Ya'yan
Manzon Allah har Guda biyu Amma ba'a Taba samunsa ba dayi Mauludi ba.
Haka Dan baffansa Sayyidina Aliyu tun Yana karaminsa Ya Yarda da abinda
Annabi (Saww) Yazo dashi, domin tun Yana Dan Shekara Bakwai ko Tara ya
karbi Musulunchi Kuma surukin Annabi (Saww), Wanda ya auri Daya daga
Cikin 'ya'yan Annabi (Saww) (Kusan ma Wacce Annabi Yafi so a Cikin
'ya'yansa).
Sayyidina Aliyu Shine, Wanda ya yarda ya amince ya
kwanta akan Shimfidar Ma’aiki (saww) acikin daren da Mushrikai suke
nufin su kasheshi (Saww).
Sayyidina Aliyu ya yarda ya kwanta
amadadinsa, duk da yasan cewa zasu iya harbinsa da kibiya ko su kasheshi
tun kafin su gane cewa ba Ma’aikin bane awajen. (saww), Amma Duk da
Irin wanna So Annabi Ya yo wafati ya barshi Duniya baiyi Mauludiba Bai
Kuma yi Umurni da ayi mauludin ba.
Sayyidina Bilal Shine
Ladanin Manzon Allah (Saww) bayan Ma'aiki (Saww) Ya bar Duniya Saboda
Tsananin soyayyarsa ga Ma'aiki (Saww) Sayyidina Bilal dena kiran sallah
yayi!!
Bilalu (rta) bai Qara yin kiran sallah ba Sai rannan
Sayyiduna Umar (ra) yace masa yazo yayi (aranar da aka karbo Masallacin
Qudus).
Da Bilalu ya fara kiran sallah, yazo daidai wajen
“ASH-HADU ANNA MUHAMMADAR RASULULLAH!! Yana fada haka, sai ya fashe da
kuka, Sahabbai ma kowa sai kuka.
An ce ba’a ta’ba ganin ranar
da daruruwan Sahabbai sukayi kuka suka zubar da hawayesosai kamar wannan
ranar ba.. Sai sukaji Tamkar awannan lokacin ne Ma’aiki ya bar duniya!!
Amma Duk da Wannan Basuyi Mauludi ba.
Imamu Malik Saboda
Soyayyarsa ga Ma'aiki (Saww), Baya Fadin hadisi a Hanya, Idan Ka
tambayeshi hadisi a hanya sa Yake a dake Ka, Idan zai Bayyana hadisi sai
Yayi wanka ya Sanya Turare Saboda Tsananin Soyayyarsa ga Fiyayyen
Halitta (Saww).
Har an Ruwaito Cewa, Baya hawan Doki a Madina,
Baya saka takalma a Madina Da aka tbayeshi dalili Yace, Saboda Baya it's
takin Kasarda Annabi (Saww) Yake a Ciki, Amma Duk da Irin Wannan
Soyayyah da Yake yiwa Annabi (Saww) ba'a Samu Yayi Mauludi ba.
Shin kana tunanin duk sun Manta NE da Ranar haihuwar Annabi (Saww)? Ko
Kuma basa son shine? Ko Kuma Tunaninsu da fahimtarsu Bata Kai Cen ba?
'yan Uwana Masu Murnar Mauludi Kuyi Hakuri Dolene sai Mun Tunatarda kanmu abinda Yake daidai ko zamu Samu Rabo a Gobe Qiyama.
Muna Rokon Allah ya nuna Mana Gaskiya Kuma ya Bamu Ikon Binta, Ya Kuma Nuna Mana Karya Ya Kuma Bamu Ikon Kauce Mata.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tue 12-11-2019
Tuesday, 12 November 2019
Tuesday, 13 August 2019
KA TABA SALLAR GAWA?
Mutane da Yawa Sukanyi Sallar Janaiza (Sallar Gawa), Amma Kuma Basu San ya ake yin wannan Sallah ba (Ma'ana Basu San me ake fada a Sallar ba), ko Kuma Basu San hukunce hukuncen ta ba.
Da farko Ya Halatta Idan Liman yayi Niyar yin Sallar Gawa yayi Kabbara Hudu, Biyar, Shidda, Bakwai ko Kuma Tara, a Lokacin Sallar Gawa, Sannan ya sallame, domin duka An samu wannan dalilai daga Sahabban Annabi (Saww) Sunyi hakan.
Kabbara Hudu, Sayyidina Abu Huraira (RTA) Yace, " Lokacinda labarin rasuwar Najashi (Sarkin Habasha) ya zowa Annabi (Saww), A wannan Rana sai Annabi (Saww) Ya fita da mu a Wani wuri da ake yin sallah, mukayi sahu Annabi (Saww) yayi Mana Sallar Janaiza Yana Mai yin Kabbara hudu.
(Sahih Al-Bukhari, littafe na 2, shafi na 227, Hadith na 404; ko Kuma Sahih Muslim, littafe ba 2, shafi na 452, Hadith na 2077).
Kabbara Biyar, Abdurrahman Ibn Abi Laylah (RTA) yace, Zayd Dan Arqam ya kasance Yana Yana yin kabbarori Hudu Idan Dayan mu ya rasu, wata Rana sai ya yi raka'a Biyar sai muka tambayeshi Dalilin yin Haka, sai Yace, Ma'aikin Allah (tsira da amincin Allah Su tabbata a gareshi) ya kanyi Haka.[
(Sahih Muslim, littafe na. 2, shafina 453 Zuwa 454, Hadith na 2089).
Kabbara Shidda, Abdul Khayr Yace, Ali Ibn Abi Talib Ya kasance Yana yin Kabbarori Shidda (Idan Yana Bada Sallar Gawa), ga wayanda suka halarci yakin Badar, Kabbarori Biyar ga sauran Sahabban Annabi (Saww) da Basu halarci yakin ba, Sannan Yana yin Kabbarori Hudu ga gama GARIN Al'umma.
(Imamu Al-Bayhaqi da Ad-Daraqutni suka fitar dashi hadisi ne Mai kyau a duba a Cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi na 113).
Kabbarori Bakwai, Musa Dan Abdullahi Dan Yazid yace, Sayyidina Aliyu ya yi Kabbarori guda Bakwai a lokacin da Yake sallatar gawar Qatadah, (Kuma Qatadah ya kasance daga Cikin wayanda suka halarci yakin Badar).
( Imamu Bayhaqi ya fitar dashi Kuma hadisi ne Mai kyau a duba a Cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi na 113 Zuwa 4).
Kabbarori Tara, Abdullahi Ibn Az Zubar ya ruwaito Cewa, Annabi (Saww), ya sallaci gawar Sayyidina Hamza Yana mai yin Kabbarori guda Tara.
(At-Tahawi da kuma At-Tabarani suka fitarda shi hadisi ne Mai kyau a duba a cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi na 114).
Ya Halatta Mutum ya daga hannayensa Biyu idan zaiyi Kabbara a kowace Kabbara ko Kuma Mutum ya daga hannayen a kabbarar farko kawai kowane Mutum yayi daidai ne.
(A duba a Sahih Al-Bukhari, littafe na 2, shafi na 228, 55).
Ana son Mutum ya karanta suratul fatiha da sauri a kabbarar farko.
(Sahih Bukhari, littafe na 2, shafi na 236, Hadith na 419; ko Kuma Sahih Al-Bukhari, littafe na 1, shafi na 397, Hadith na 710; Sahih Muslim, littafe na 1, shafi na 219, Hadith na 786).
A Kabbara ta Biyu Ana so ayi sauri ayiwa Annabi (Saww) Salati, duk salatin da Mutum yayi Amma salatin Ibrahimiyya Shine Wanda aka fiso a Yi domin shine salatin da ya zo a ingantattun hadisai.
A Kabbara ta ukku Ana so ne ayiwa Mamaci Addu'ar Samun Rahama, Tunda sallat anayinta ne ga Mamaci Ana so ayi Masa Addu'ah a Kabbara ta ukku, zuwa ta Hudu ko ta Biyar Zuwa Tara domin nema Masa rahamar Allah. (Abu Dawud, 2, shafi na 616-7, 2740).
Sallamewa, Akwai hanyoyi Biyu da Sunna ta amince A sallame Sallar kamar yadda Baihaqi da Tabaranj suka ruwaito a Cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi ba 127, #83).
1. Ko dai Mutum yayi sallama daya kawai ta hanyar sallamewa a Bangaren Dama. Kamar yanda Hadisin Abu Huraira (RTA) ya nuna.
2. Ko Kuma Mutum ya sallame a duka bangarori Biyu (Dama da hagu) kamar yanda yazo a Hadisin Ibn Mas'ud.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tue 13-08-219
UNGUZOMA (MIDWIVES)
UNGOZOMA (MIDWIFE) BAIWAR ALLAH
Wasu suna ganin kalmar Ungozoma ta samo asali ne daga "ungo-tsoma ".Wai don Idan mace ta yanke cibin jariri, kuma mabiyya (mahaifa) ta fado, to sai a dauko ta fito da ita waje ta mika wa masu taimaka mata, ta ce da su "Ungo-tsoma " A cikin masaki mai cike da ruwa. Wai ta haka ne sabida yawan fadar kalmar "Ungo-tsoma ". Sai ta koma Ungotsoma. "Ungozoma ".
A Al'adar Hausawa Ungozoma ta na da muhimmanci kwarai da gaske, domin kuwa kusan kowanne Kauye ko Gari ko Unguwa Inda jama'a su ke zaune akwai Ungozoma, kamar dai yadda ake samun Ruwa don bukatar rayuwa.
Saboda sanin muhimmancin Ungozoma a al'umar Hausawa har kirari su ke mata da cewa " Ungozoma kin fi mai da son da ". Haka har cikin Karin magana an ambaci Ungozoma, misali : "Komai saurin Ungozoma ta jira a haihu ".da kuma "Ai ba a Kare haihuwa ba wai an baiwa Ungozoma tuwan suna a hannu". Dasauransu. wannan shi zai Kara tabbatarma da muhimmamchin Wannan Mata a Cikin al'umma.
Akwai ire-iren Ungozoma guda biyar. (5times) a kasar Hausa kamar haka :
1-Ungozomar Gado, Wasu Gidajen Attajirai Sukan Ajiye Ungozoma wacce duk matarda zata haihu Gidan itace zata Kula da wannan matar tun daga rainon Cikin har Zuwa Haihuwa Itace zata Rika Kula da matar.
2-Ungozomar Sana'a, Akan Samu Wasu Masu Aikin Karbar Nakuda (Ungozoma), wacce Ita Zaman Kuddi take, 'yan Unguwa sun San da zamanta, Duk Gidan da za'a haihu akan Kira Irin wannan matar a sanyata ta karbi bikin Idan an haihu sai a biyata ladan aikinta.
3-Ungozomar Dangi, Kamar Gidan Attajirai Haka A Dangi Idan an samu Macce wacce ta iya Karbar haihuwar to Tana iya Zama ta Dangi, duk wani wata 'yar uwa ko matar Dan uwa da zata haihu akan je anemo ta ta karbi haihuwar.
4-Ungozomar Masarauta, Duk Gidan sarauta akan samu Mai Karbar biki na matar Sarki ko Kuma 'ya'yan Sarki ko Kuma Matan 'ya'yan Sarki Dasauransu.
Ayyukan Ungozoma suna da yawa ga kadan daga ciki:
Akwai aikace -aikace da dama da Ungozoma ke gudanarwa kafin haihuwa, da kuma lokacin haihuwa, da bayan an haihuwa.
Sanin Lafiyar Abin da ke Ciki Tun kafin lokacin haihuwa Ungozoma takan je ta duba lafiyar jariri ,misali kwanciyarsa a ciki, motsinsa Dasauransu. Ta hanyar sunkuyawa ta kara kunnwanta kan cibiyar mai ciki, ta yadda Idan ta ji matsala ta gyara mata ta hanyar mulmula cikin a hankali da kuma yin amfani da wani dan karamin Koko wajan gyara Shi ta yadda lokacin haihuwa zai fito cikin sauki salamun -salamun.
Kula da mai Ciki Wani muhimmin aikin Ungozoma za taita kula da mai ciki wajan hanata yin wasu abubuwa ko sata ko hanata shan abu mai daci, da kuma bata magungunan rage Zaki, da kuma samun Karin karfin jiki a lokacin Nakuda.
Gyaran dakin Mai Ciki
Yanayin gyaran dakin mai ciki iri biyu ne kafin haihuwa da kuma bayan haihuwar. Ungozoma takan kawar da kayan dakin mai haihuwa gefe guda dan ta sami sararin da za ta haihu.
Gyaran daki na biyu Shi ne bayan an haihuwa Ungozoma zata gyara dakin tsaf ta maida Shi yadda yake.
Karbar Haihuwa Dazarar anga Nakuda ta kankama, haihuwa ta doso gadan -gadan sai Ungozoma da dangi masu taimaka wa mai haihuwa su shiga shiri Karbar haihuwar.
Ayyukan Ungozoma suna da yawa kamar bata taimako na abinda za ta sha lokacin Nakuda yankan cibi dss. Amma konan muka tsaya Ina ga za mu iya fahimtar Wacece Ungozoma da kuma Ire-irenta da Irin gudunmawar ta ga mai ciki da kuma abin haihuwa (Jariri).
Babu Shakka Babu Wani mutum a Duniyar Nan da Ungozoma Bata Yi Masa Rana ba.
Jinjina Ga Ungozoma (Midwives).
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tue 06-08-2019
Wasu suna ganin kalmar Ungozoma ta samo asali ne daga "ungo-tsoma ".Wai don Idan mace ta yanke cibin jariri, kuma mabiyya (mahaifa) ta fado, to sai a dauko ta fito da ita waje ta mika wa masu taimaka mata, ta ce da su "Ungo-tsoma " A cikin masaki mai cike da ruwa. Wai ta haka ne sabida yawan fadar kalmar "Ungo-tsoma ". Sai ta koma Ungotsoma. "Ungozoma ".
A Al'adar Hausawa Ungozoma ta na da muhimmanci kwarai da gaske, domin kuwa kusan kowanne Kauye ko Gari ko Unguwa Inda jama'a su ke zaune akwai Ungozoma, kamar dai yadda ake samun Ruwa don bukatar rayuwa.
Saboda sanin muhimmancin Ungozoma a al'umar Hausawa har kirari su ke mata da cewa " Ungozoma kin fi mai da son da ". Haka har cikin Karin magana an ambaci Ungozoma, misali : "Komai saurin Ungozoma ta jira a haihu ".da kuma "Ai ba a Kare haihuwa ba wai an baiwa Ungozoma tuwan suna a hannu". Dasauransu. wannan shi zai Kara tabbatarma da muhimmamchin Wannan Mata a Cikin al'umma.
Akwai ire-iren Ungozoma guda biyar. (5times) a kasar Hausa kamar haka :
1-Ungozomar Gado, Wasu Gidajen Attajirai Sukan Ajiye Ungozoma wacce duk matarda zata haihu Gidan itace zata Kula da wannan matar tun daga rainon Cikin har Zuwa Haihuwa Itace zata Rika Kula da matar.
2-Ungozomar Sana'a, Akan Samu Wasu Masu Aikin Karbar Nakuda (Ungozoma), wacce Ita Zaman Kuddi take, 'yan Unguwa sun San da zamanta, Duk Gidan da za'a haihu akan Kira Irin wannan matar a sanyata ta karbi bikin Idan an haihu sai a biyata ladan aikinta.
3-Ungozomar Dangi, Kamar Gidan Attajirai Haka A Dangi Idan an samu Macce wacce ta iya Karbar haihuwar to Tana iya Zama ta Dangi, duk wani wata 'yar uwa ko matar Dan uwa da zata haihu akan je anemo ta ta karbi haihuwar.
4-Ungozomar Masarauta, Duk Gidan sarauta akan samu Mai Karbar biki na matar Sarki ko Kuma 'ya'yan Sarki ko Kuma Matan 'ya'yan Sarki Dasauransu.
Ayyukan Ungozoma suna da yawa ga kadan daga ciki:
Akwai aikace -aikace da dama da Ungozoma ke gudanarwa kafin haihuwa, da kuma lokacin haihuwa, da bayan an haihuwa.
Sanin Lafiyar Abin da ke Ciki Tun kafin lokacin haihuwa Ungozoma takan je ta duba lafiyar jariri ,misali kwanciyarsa a ciki, motsinsa Dasauransu. Ta hanyar sunkuyawa ta kara kunnwanta kan cibiyar mai ciki, ta yadda Idan ta ji matsala ta gyara mata ta hanyar mulmula cikin a hankali da kuma yin amfani da wani dan karamin Koko wajan gyara Shi ta yadda lokacin haihuwa zai fito cikin sauki salamun -salamun.
Kula da mai Ciki Wani muhimmin aikin Ungozoma za taita kula da mai ciki wajan hanata yin wasu abubuwa ko sata ko hanata shan abu mai daci, da kuma bata magungunan rage Zaki, da kuma samun Karin karfin jiki a lokacin Nakuda.
Gyaran dakin Mai Ciki
Yanayin gyaran dakin mai ciki iri biyu ne kafin haihuwa da kuma bayan haihuwar. Ungozoma takan kawar da kayan dakin mai haihuwa gefe guda dan ta sami sararin da za ta haihu.
Gyaran daki na biyu Shi ne bayan an haihuwa Ungozoma zata gyara dakin tsaf ta maida Shi yadda yake.
Karbar Haihuwa Dazarar anga Nakuda ta kankama, haihuwa ta doso gadan -gadan sai Ungozoma da dangi masu taimaka wa mai haihuwa su shiga shiri Karbar haihuwar.
Ayyukan Ungozoma suna da yawa kamar bata taimako na abinda za ta sha lokacin Nakuda yankan cibi dss. Amma konan muka tsaya Ina ga za mu iya fahimtar Wacece Ungozoma da kuma Ire-irenta da Irin gudunmawar ta ga mai ciki da kuma abin haihuwa (Jariri).
Babu Shakka Babu Wani mutum a Duniyar Nan da Ungozoma Bata Yi Masa Rana ba.
Jinjina Ga Ungozoma (Midwives).
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tue 06-08-2019
Sunday, 2 June 2019
ZAKKAR FIDDA KAI DA HUKUNCE HUKKUNCENTA
ZAKKAR
FIDDA KAI (ZAKKATUL FITIR)
Zakkar Fidda Kai Sadaka ce da Manzon
Allah ya farlanta ta yayin da aka gama azumi, An kiran ta zakkar fidda kai ne
saboda tana wajaba ne idan an gama Azumin Ramadan gabadaya. Da Larabci ana
kiranta da Zakkatul Fitr Kalmar Fitr an ciro tane daga Iftar (Wanda yake nufin
Buda baki), Haka Ita ma Kalmar Iftar an samo tane daga Kalmar Futoo (Wacce ake
nufi da Karin Kumallo) (Wato Breakfast).
Hukuncin
Zakkar Fidda Kai
Zakkar Fidda kai wajibi ce akan
dukkan musulmi, wanda ya mallaki sa'i daya na abinci (kamar kwano daya kenan)
wanda ya fi yawan abin da zai ciyar da iyalansa. Mai ba da zakkar zai fitar wa da
kansa, matarsa, da duk wanda ciyar da shi take kansa, har ma dan jaririn da
yake cikin ciki.
Dalilin wajabcinta shi ne abin da
aka rawaito daga Dan Umar (RTA) ya ce, “Manzon Allah (Saww) ya wajabta
zakkar fidda kai, sa'i daya na dabino, ko sa'i dayan da sha'ir, an wajabta ta a
kan bawa, da da, namiji da mace, babba da yaro daga cikin musulmi. Manzon Allah
ya yi umarni a bayar da ita zakkar kafin mutane su fita sallar idi”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Lokacin
Da Ake Fitar Da Zakkar Fidda Kai
An fi son a fitar da zakkar fidda kai
ranar Idi, bayan alfijir ya bullo kafin sallar Idi. Kuma ya halatta a gabatar da
ita kafin ranar idi da kwana daya ko biyu, saboda sahabbai sun yi haka.
Ba ya halatta a jinkirta ta har
bayan idi, saboda hadisin Dan Umar wanda ya gabata in da yake cewa : “Manzon
Allah (Saww) ya yi umarnin a ba da ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi”.
Haka ma a cikin hadisin Abdullahi dan
Abbas, Manzon Allah (Saww) ya ce, “Wanda ya bayar da ita kafin sallar idi,
to zakka ce karbabbiya, wanda kuwa ya bayar da ita bayan sallah, to sadaka ce
daga cikin sadakoki”[Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Gwargwadon
Abin Da Ake Fitarwa A Zakkar Fidda Kai
Kowane mutum sa'i [Sa'i Dayan na
Alkama yana daidai da kilo biyu da giram arba'in.] daya ne, daga cikin abincin
da dan mutane suke ci, kamar shinkafa, dabino, alkama, saboda hadisin Abu Sa'id
Al-khuduriy – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun kasance muna fitar da
zakkar fidda kai daga abinci a zamanin Manzon Allah (Saww) ranar qaramar
sallah”
Abu Sa'id ya ce, “Abincinmu a
wannan lokaci kuwa shi ne Sha'ir da zabibi da cukwi [Cukwi : Shi ne nonon da ya
bushe, a na girki da shi.], da dabino " [Bukhari
ne ya rawaito shi].
Wadanda
Ake Bawa Zakkar Fidda Kai
Ana bawa wadannan mutanen guda
takwas zakkar fidda kai, saboda sun shiga cikin fadin Allah Madaukakin Sarki “Kadai
Sadaka a bawa faqirai …”. (Attauba :
60).
Abin lura a wajen wanda za’a bawa
har wayau shine, Za a bawa miskini ne ko fakiri wanda ba ya da hali, kamar dai
yadda Annabi (SAW) ya ambaci lafazin Miskini, to shi ne za a ba shi, ba lallai
sai an rarraba ga wadanda aka ambace su a cikin Ayar Zakka ba cikin suratul
Taubah, amma wani yana iya hawa tudu biyu, a ba shi don ya cancanta, sannan sai
ya bayar don ya samu wadatuwa.
Hikimar
Zakkar Fidda Kai
1- Tsarkake mai azumi daga
maganganun wofi da na batsa, saboda abin da aka rawaito daga Abdullahi Dan
Abbas (RTA) ya ce, “Zakkar fidda kai tsarki ce ga mai azumi daga maganganun
banza da ayyukan batsa, kuma ciyarwa ce ga miskinai”[Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Saboda mafi yawanci mai azumi ba ya
rabuwa da maganganun da basu da amfani da wasannin shirme, da maganar da ba ta da
fa'ida, to wannan sadakar sai ta zamar masa tsarki daga irin wadanncan maganganun
haramun da ya yi, wadanda suke rage ladan ayyuka, suna rage azumi
2- Yalwatawa miskinai da talakawa,
da wadatar da su ranar idi daga roqon mutane, roqon da yake dauke da qasqanci
da wulaqanci a ranar idi, wadda take rana ce ta farin ciki da murna, sai su yi
tarayya da mutane cikin farin cikin ranar idi.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 03-06-2019
Mon 03-06-2019
Sunday, 7 April 2019
SUWA KE BADA KWANGILA DOMIN TABA DARAJAR SARKIN MUSULMI
Wannan Rubutu zanyi shine zuwa ga
kalar mutane guda biyu, Na farko sune, Wayanda ke karbar kwangila domin shiga
kafafen yada labarai domin wargaza hadinkan Al’ummar musulmi. Mutane na biyu
kuma masu bayarda kwangilar (daga baya kuma su fito suce ba su sukace ayi ba).
To duk muna sane da ku da kulle kullenku na wargaza hadin kan musulmi da Allah
(Swt) ya umurcemu da yi, domin hadin kai Allah ne ya kwadaitarda yinsa a
tsakanin Al’umma. Haka kuma zagin Shugaban Musulmi (Wanda ke da Ikon fadar anga
wata ko ba’a gani ba shima wargaje zaman lafiya ne), Idan zaka dubi Alqur’ani
gaba daya zaka tarar yana karantarda hadin kai tare da biyayya ga shuwagabanni.
Misali, a cikin suratul Fatiha Allah (Swt) Yana cewa, “Ihdinas-Siraat-Al-Mustaqeem” (Ma’ana, Ya Allah ka shiryar damu ga hanya madaidaiciya), To meyasa Idan zakazo wajen karanta wannan ayar ta Ihdinas-Siraat-Al-Mustaqeem meyasa baka ce, Ihdinis-Siraat-Al-Mustaqeem ba (Ma’ana Ya Allah ka shiryarda ni ga hanya madaidaiciya) Saboda a nuna mana muhimmacin hadin kai.
Haka kuma a wajen fadin “Iyyaka na'aboudou wa iyyaka nasta'in” (Kai muke bauta kuma kai muke neman taimakonka) Meyasa bakace, ” Iyyaka a'aboudou wa iyyaka asta'in” (Kai nake bauta kuma kai nake neman taimakonka) ba? Ubangiji (SWT) Ya sanya wannan ne domin ya kara nuna mana muhimmanchin hadin kai. Babu shakka Idan kaje yin sallah ko kai kadaine (kuma ko a ina ne dole lamirin mutane na biye da kai) domin a nuna maka muhimmanchin hadin kai.
Bayan wannan ma Saboda Ubangiji ya kara nuna mana muhimmancin zaman lafiya ya sanya mana Sallah biyar a wuni, Sallar ma ba’a amince ka rufe daki kai kadai kayi ba in banda Uzuri, dole sai ka fito a masallachin Unguwa kayi sallar, Wannan kai tsaye kowa ma yana iya fahimtar karatun cewa, ana so a nuna mana hadin kai ne.
Haka a duk sati zamu hadu kusan yan Unguwanni da
yawa muyi sallar jumu’ah wannan ma hadin kai ne ake nuna mana, Kai k ace wannan
bai Isa ba Ubangiji ya sake sanya mana Wasu salloli biyu a shekara domin kawai
a Kara nuna mana muhimmanchin hadin kai.
Duk dai domin Ubangiji ya nuna mana Muhimmanchi tare da Soyuwarsa akan mu hada
kai, Ubangiji ya sanya mana Haduwa a saman dutse guda kwaya daya tal (Dutsin
Arfa) tare da sanya Lada mai tsoka ga duk wanda ya samu damar halartar wannan
tsayuwa a wannan dutse (na Arfa), Da zaka je ka samu Tsauni a garinku ko
kasarku kaje a wannan rana kayi tsaye da zummar kayi tsayuwar arfa to wannan
tsayuwar batayi ba, ba saboda komai ba sai don Allah (SWT) Ya nuna mana
muhimmanchin hadin kai (Musamman na Musulmi).
Akan haka ne ma Allah (SWT) Yayi shuwagabanni (Annabawa) kuma yace a bi bayansu kuma yayi shuwagabanni na Al’umma ya kuma bada umurnin abisu a wurare daban-daban,
Misali, Idan Kuka zo zakuyi Sallah Dole ne ku sanya dayanku a matsayin liman kuma dole ne duk abinda yayi shi zakuyi a matsayinsa na shugaba a wajenku a wajen sallah. Bayan ya fara karatun fatiha duk zakuyi shiru kuna saurarensa, Bayan y agama yace, Amin Sannan kuma kuce. Wannan kai tsaye yana nuni da yin biyayya ga Shugaba (Akan abinda yake halat).
Amma yau Saboda lalaci na neman duniya wasu bata gari wayanda basu son ganin musulunchi yaci gaba suna so su kawo suka ga wayannan shuwagabanni. (Ya Allah ka shiryesu), Bazan Manta ba a Shekarar da ta gabata Shiekh Ahmad Gummi Yaje wajen Shirya Atiku da Obasanjo Nan da nan gari ya kaurace ana zaginsa tare da tsinuwa wanda kuma sam Abokan zaman mu ba haka suke ba.
Misali a wannan tafiyar da Shiekh Ahmad Gummi yayi yaje wajen wannan shiri a tare da shi akwai shugaban Kiristoci Rev. Hassan Maku Kuka wanda har yaje ya dawo baka ji Kiristan ko daya ba daya gaya masa Magana marar dadi. Wannan kai tsaye zai nuna mana kura kuran da mukeyi. Na yarda da wasu bata garin Mutane suna Amfani damu domin mu rika batanci ga shuwagabannin mu.
Ina wannan rubutun ne Ya’Allah Allah yasa su masu bada kwangilar suji tsoron Allah su daina, domin babu shakka Mun sansu kuma Idan muma muka ari Jahilcinsu muka fara bazasuji dadinmu ba ko kadan, Domin muna nasane da ko suwaye masu bada kwangilar (Akwai Mai Gida Yamma akwai Mai Gida Gabas) don haka Larabawa suna KARIN MAGANA Cewa, “MAN ANZARAKA FAQAD A’A ZARAKA” (Ma’ana Wanda ya Gargadeka Hakika ya gama shiryarda kai).
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mataimaki na Musamman ga Sarkin Musulmi akan Sababbin kafofin yada labarai
Sun 07/04/2019
Monday, 4 March 2019
WANENE SARKIN YAKIN DAULAR USMANIYYA
Daga cikin Malaman Da Shehu Usmanu Danfodiyo ya Tarar a
Wannan Kasa Akwai Muhammad Alamin Alkanemi (Wanda yake Zaune a Borno yana
Sarauta) Shi wannan Malamin Mahaifinsa Balarabe ne daga gari da ake kira
Fazzana (dake cen Cikin Croatia).
Kamar Yadda Tarihi yazo Cewa, Wannan Malamin Kafin Zuwan
Shehu yaje Makkah domin yin aikin hajji daga cen kuma sai ya wuce garin
Mahaifinsa Fazzana domin ya ziyarci dangin Mahaifinsa daga baya kuma sai ya
dawo kasarsa borno.
Kasancewar Tafiya a wancen lokacin tana da wuya, (domin mutum
yakan shekara da shekaru bai samu yaje garin da zaije ba), wannan yasa Bayan
dawowarsa sai ya tarar da Daawar Shehu ta mamaye ko Ina a fadin wannan kasa ko
kuma Daula a wancen lokaci. Inda Shehu da Almajiransa suka yi waazi suka
shiryarda mutane zuwa ga hanyar gaskiya, wayanda kuma suka ki jin wa’azi Shehu
ya yakesu (A cikin wayanda aka yaka kuwa harda Jama’are da Hadeja) da sauran
wasu garuruwa wayanda suke cikin Rikon
Borno.
Wannan dalili shiyasa Muhammad Alamin Alkanemi Ya zargi
jihadin Shehu Usmanu Bin Fodio Inda ya nuna Jahdin na Shehu bai dace ba (Ma’ana
bai dace ya yaki wasu garuruwa ba), a cikin wayannan garuruwa da bai dace a yaka
ba akwai mutanen da Borno ke riko, Dominsu Mutanen Borno da wayanda suke riko
Musulmi ne.
Wannan daliline ya sanya Alkanemi ya rubuta wasika Ga Shehu
yana zargin Jahadinsa, Bayan Wasikar Alkanemi ta zowa Shehu da Almajiransa, nan
take Shehu ya Umurci da Muhammad Bello Dansa da ya mayarwa da Alkanemi amsar
wasikarsa.
A haka Alkanemi ya rika turo wasika inda shi kuma Shehu yana
sanya Bello yana maida martani. A Wannan yanayine Allah (Swt) ya karbi ran
Shehu Usmanu (Allah ya jikansa da Rahama), Har bayan Mutuwar Shehu Aminu
Alkanemi bai daina turo wasika bag a Sarakunan Daular Usmaniya, Inda daga
karshe dai Alkanemi ya Rubutowa da Muhammad Bello wasika akan Cewa, Zaizo ya
yaki Daular Usmaniyya. Kuma zai fara yakar Kano (tunda tana daga rikon Daular
Usmaniyya dake da Hedkwata a Sokoto).
Bayan Samun wasikar Alkanemi Sai Sarkin Musulmi Muhammad
Bello ya rubutawa da Yakubun Bauchi (Sarkin Bauchi), Akan Cewa, Ya tari
Alkanami da yaki (Wanda a lokacin (Kai harma a yanzu ) Sarkin Bauchi yana
karbar Umurni ne daga Sarkin Musulmi dake Sokoto).
Inda nan take Yakubun Bauchi ya shirya Rundunar yaki yaje ya
tari Aminu Alkanami (Suka gwabza yaki mai yawa a tsakaninsu), daga karshe
Yakubun Bauchi ya samu nasara ga Alkanami, Nan take Alkaname ya gudu, Shi kuma
Yakubun Bauchi ya bishi har tsawon kwana ukku bai kama shi ba.
Wannan Dalili yasa aka Bawa YAKUBUN BAUCHI (SARKIN YAKIN
YAKIN SARKIN MUSULMI MUHAMMADU BELLO), Wanda har yanzu Jikokinsa (Wayanda suke
rike da Sarautar Bauchi suke, Rike da Sarautar Sarkin Yaki).
Don haka duk mai tunanin Ayi masa Sarautar Sarkin Yakin
Sokoto to yanama daina wahalar da kansa domin Sarauta ce mai tarihi ba Sarauta
ce ta Cuwa-cuwa ba.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 04-03-3019
Mon 04-03-3019
Subscribe to:
Posts (Atom)