Sunday, 2 June 2019

ZAKKAR FIDDA KAI DA HUKUNCE HUKKUNCENTA

ZAKKAR FIDDA KAI (ZAKKATUL FITIR)
Zakkar Fidda Kai Sadaka ce da Manzon Allah ya farlanta ta yayin da aka gama azumi, An kiran ta zakkar fidda kai ne saboda tana wajaba ne idan an gama Azumin Ramadan gabadaya. Da Larabci ana kiranta da Zakkatul Fitr Kalmar Fitr an ciro tane daga Iftar (Wanda yake nufin Buda baki), Haka Ita ma Kalmar Iftar an samo tane daga Kalmar Futoo (Wacce ake nufi da Karin Kumallo) (Wato Breakfast).

Hukuncin Zakkar Fidda Kai
Zakkar Fidda kai wajibi ce akan dukkan musulmi, wanda ya mallaki sa'i daya na abinci (kamar kwano daya kenan) wanda ya fi yawan abin da zai ciyar da iyalansa. Mai ba da zakkar zai fitar wa da kansa, matarsa, da duk wanda ciyar da shi take kansa, har ma dan jaririn da yake cikin ciki.
Dalilin wajabcinta shi ne abin da aka rawaito daga Dan Umar (RTA) ya ce, “Manzon Allah (Saww) ya wajabta zakkar fidda kai, sa'i daya na dabino, ko sa'i dayan da sha'ir, an wajabta ta a kan bawa, da da, namiji da mace, babba da yaro daga cikin musulmi. Manzon Allah ya yi umarni a bayar da ita zakkar kafin mutane su fita sallar idi”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Lokacin Da Ake Fitar Da Zakkar Fidda Kai
An fi son a fitar da zakkar fidda kai ranar Idi, bayan alfijir ya bullo kafin sallar Idi. Kuma ya halatta a gabatar da ita kafin ranar idi da kwana daya ko biyu, saboda sahabbai sun yi haka.
Ba ya halatta a jinkirta ta har bayan idi, saboda hadisin Dan Umar wanda ya gabata in da yake cewa : “Manzon Allah (Saww) ya yi umarnin a ba da ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi”.
Haka ma a cikin hadisin Abdullahi dan Abbas, Manzon Allah (Saww) ya ce, “Wanda ya bayar da ita kafin sallar idi, to zakka ce karbabbiya, wanda kuwa ya bayar da ita bayan sallah, to sadaka ce daga cikin sadakoki”[Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Gwargwadon Abin Da Ake Fitarwa A Zakkar Fidda Kai
Kowane mutum sa'i [Sa'i Dayan na Alkama yana daidai da kilo biyu da giram arba'in.] daya ne, daga cikin abincin da dan mutane suke ci, kamar shinkafa, dabino, alkama, saboda hadisin Abu Sa'id Al-khuduriy – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai daga abinci a zamanin Manzon Allah (Saww) ranar qaramar sallah”
Abu Sa'id ya ce, “Abincinmu a wannan lokaci kuwa shi ne Sha'ir da zabibi da cukwi [Cukwi : Shi ne nonon da ya bushe, a na girki da shi.], da dabino " [Bukhari ne ya rawaito shi].

Wadanda Ake Bawa Zakkar Fidda Kai
Ana bawa wadannan mutanen guda takwas zakkar fidda kai, saboda sun shiga cikin fadin Allah Madaukakin Sarki “Kadai Sadaka a bawa faqirai …”. (Attauba : 60).
Abin lura a wajen wanda za’a bawa har wayau shine, Za a bawa miskini ne ko fakiri wanda ba ya da hali, kamar dai yadda Annabi (SAW) ya ambaci lafazin Miskini, to shi ne za a ba shi, ba lallai sai an rarraba ga wadanda aka ambace su a cikin Ayar Zakka ba cikin suratul Taubah, amma wani yana iya hawa tudu biyu, a ba shi don ya cancanta, sannan sai ya bayar don ya samu wadatuwa.

Hikimar Zakkar Fidda Kai
1- Tsarkake mai azumi daga maganganun wofi da na batsa, saboda abin da aka rawaito daga Abdullahi Dan Abbas (RTA) ya ce, “Zakkar fidda kai tsarki ce ga mai azumi daga maganganun banza da ayyukan batsa, kuma ciyarwa ce ga miskinai”[Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Saboda mafi yawanci mai azumi ba ya rabuwa da maganganun da basu da amfani da wasannin shirme, da maganar da ba ta da fa'ida, to wannan sadakar sai ta zamar masa tsarki daga irin wadanncan maganganun haramun da ya yi, wadanda suke rage ladan ayyuka, suna rage azumi
2- Yalwatawa miskinai da talakawa, da wadatar da su ranar idi daga roqon mutane, roqon da yake dauke da qasqanci da wulaqanci a ranar idi, wadda take rana ce ta farin ciki da murna, sai su yi tarayya da mutane cikin farin cikin ranar idi.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 03-06-2019

No comments:

Post a Comment