Tuesday, 13 August 2019

UNGUZOMA (MIDWIVES)

UNGOZOMA (MIDWIFE) BAIWAR ALLAH

Wasu suna ganin kalmar Ungozoma ta samo asali ne daga "ungo-tsoma ".Wai don Idan mace ta yanke cibin jariri, kuma mabiyya (mahaifa) ta fado, to sai a dauko ta fito da ita waje ta mika wa masu taimaka mata, ta ce da su "Ungo-tsoma " A cikin masaki mai cike da ruwa. Wai ta haka ne sabida yawan fadar kalmar "Ungo-tsoma ". Sai ta koma Ungotsoma. "Ungozoma ".

A Al'adar Hausawa Ungozoma ta na da muhimmanci kwarai da gaske, domin kuwa kusan kowanne Kauye ko Gari ko Unguwa Inda jama'a su ke zaune akwai Ungozoma, kamar dai yadda ake samun Ruwa don bukatar rayuwa.

Saboda sanin muhimmancin Ungozoma a al'umar Hausawa har kirari su ke mata da cewa " Ungozoma kin fi mai da son da ". Haka har cikin Karin magana an ambaci Ungozoma, misali : "Komai saurin Ungozoma ta jira a haihu ".da kuma "Ai ba a Kare haihuwa ba wai an baiwa Ungozoma tuwan suna a hannu". Dasauransu. wannan shi zai Kara tabbatarma da muhimmamchin Wannan Mata a Cikin al'umma.

Akwai ire-iren Ungozoma guda biyar. (5times) a kasar Hausa kamar haka :

1-Ungozomar Gado, Wasu Gidajen Attajirai Sukan Ajiye Ungozoma wacce duk matarda zata haihu Gidan itace zata Kula da wannan matar tun daga rainon Cikin har Zuwa Haihuwa Itace zata Rika Kula da matar.

2-Ungozomar Sana'a, Akan Samu Wasu Masu Aikin Karbar Nakuda (Ungozoma), wacce Ita Zaman Kuddi take, 'yan Unguwa sun San da zamanta, Duk Gidan da za'a haihu akan Kira Irin wannan matar a sanyata ta karbi bikin Idan an haihu sai a biyata ladan aikinta.

3-Ungozomar Dangi, Kamar Gidan Attajirai Haka A Dangi Idan an samu Macce wacce ta iya Karbar haihuwar to Tana iya Zama ta Dangi, duk wani wata 'yar uwa ko matar Dan uwa da zata haihu akan je anemo ta ta karbi haihuwar.

4-Ungozomar Masarauta, Duk Gidan sarauta akan samu Mai Karbar biki na matar Sarki ko Kuma 'ya'yan Sarki ko Kuma Matan 'ya'yan Sarki Dasauransu.

Ayyukan Ungozoma suna da yawa ga kadan daga ciki:

Akwai aikace -aikace da dama da Ungozoma ke gudanarwa kafin haihuwa, da kuma lokacin haihuwa, da bayan an haihuwa.

Sanin Lafiyar Abin da ke Ciki Tun kafin lokacin haihuwa Ungozoma takan je ta duba lafiyar jariri ,misali kwanciyarsa a ciki, motsinsa Dasauransu. Ta hanyar sunkuyawa ta kara kunnwanta kan cibiyar mai ciki, ta yadda Idan ta ji matsala ta gyara mata ta hanyar mulmula cikin a hankali da kuma yin amfani da wani dan karamin Koko wajan gyara Shi ta yadda lokacin haihuwa zai fito cikin sauki salamun -salamun.

Kula da mai Ciki Wani muhimmin aikin Ungozoma za taita kula da mai ciki wajan hanata yin wasu abubuwa ko sata ko hanata shan abu mai daci, da kuma bata magungunan rage Zaki, da kuma samun Karin karfin jiki a lokacin Nakuda.

Gyaran dakin Mai Ciki
Yanayin gyaran dakin mai ciki iri biyu ne kafin haihuwa da kuma bayan haihuwar. Ungozoma takan kawar da kayan dakin mai haihuwa gefe guda dan ta sami sararin da za ta haihu.

Gyaran daki na biyu Shi ne bayan an haihuwa Ungozoma zata gyara dakin tsaf ta maida Shi yadda yake.

Karbar Haihuwa  Dazarar anga Nakuda ta kankama, haihuwa ta doso gadan -gadan sai Ungozoma da dangi masu taimaka wa mai haihuwa su shiga shiri Karbar haihuwar.

Ayyukan Ungozoma suna da yawa kamar bata taimako na abinda za ta sha lokacin Nakuda yankan cibi dss. Amma konan muka tsaya Ina ga za mu iya fahimtar Wacece Ungozoma da kuma Ire-irenta da Irin gudunmawar ta ga mai ciki da kuma abin haihuwa (Jariri).

Babu Shakka Babu Wani mutum a Duniyar Nan da Ungozoma Bata Yi Masa Rana ba.

Jinjina Ga Ungozoma (Midwives).

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tue 06-08-2019

No comments:

Post a Comment