Da farko Ya Halatta Idan Liman yayi Niyar yin Sallar Gawa yayi Kabbara Hudu, Biyar, Shidda, Bakwai ko Kuma Tara, a Lokacin Sallar Gawa, Sannan ya sallame, domin duka An samu wannan dalilai daga Sahabban Annabi (Saww) Sunyi hakan.
Kabbara Hudu, Sayyidina Abu Huraira (RTA) Yace, " Lokacinda labarin rasuwar Najashi (Sarkin Habasha) ya zowa Annabi (Saww), A wannan Rana sai Annabi (Saww) Ya fita da mu a Wani wuri da ake yin sallah, mukayi sahu Annabi (Saww) yayi Mana Sallar Janaiza Yana Mai yin Kabbara hudu.
(Sahih Al-Bukhari, littafe na 2, shafi na 227, Hadith na 404; ko Kuma Sahih Muslim, littafe ba 2, shafi na 452, Hadith na 2077).
Kabbara Biyar, Abdurrahman Ibn Abi Laylah (RTA) yace, Zayd Dan Arqam ya kasance Yana Yana yin kabbarori Hudu Idan Dayan mu ya rasu, wata Rana sai ya yi raka'a Biyar sai muka tambayeshi Dalilin yin Haka, sai Yace, Ma'aikin Allah (tsira da amincin Allah Su tabbata a gareshi) ya kanyi Haka.[
(Sahih Muslim, littafe na. 2, shafina 453 Zuwa 454, Hadith na 2089).
Kabbara Shidda, Abdul Khayr Yace, Ali Ibn Abi Talib Ya kasance Yana yin Kabbarori Shidda (Idan Yana Bada Sallar Gawa), ga wayanda suka halarci yakin Badar, Kabbarori Biyar ga sauran Sahabban Annabi (Saww) da Basu halarci yakin ba, Sannan Yana yin Kabbarori Hudu ga gama GARIN Al'umma.
(Imamu Al-Bayhaqi da Ad-Daraqutni suka fitar dashi hadisi ne Mai kyau a duba a Cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi na 113).
Kabbarori Bakwai, Musa Dan Abdullahi Dan Yazid yace, Sayyidina Aliyu ya yi Kabbarori guda Bakwai a lokacin da Yake sallatar gawar Qatadah, (Kuma Qatadah ya kasance daga Cikin wayanda suka halarci yakin Badar).
( Imamu Bayhaqi ya fitar dashi Kuma hadisi ne Mai kyau a duba a Cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi na 113 Zuwa 4).
Kabbarori Tara, Abdullahi Ibn Az Zubar ya ruwaito Cewa, Annabi (Saww), ya sallaci gawar Sayyidina Hamza Yana mai yin Kabbarori guda Tara.
(At-Tahawi da kuma At-Tabarani suka fitarda shi hadisi ne Mai kyau a duba a cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi na 114).
Ya Halatta Mutum ya daga hannayensa Biyu idan zaiyi Kabbara a kowace Kabbara ko Kuma Mutum ya daga hannayen a kabbarar farko kawai kowane Mutum yayi daidai ne.
(A duba a Sahih Al-Bukhari, littafe na 2, shafi na 228, 55).
Ana son Mutum ya karanta suratul fatiha da sauri a kabbarar farko.
(Sahih Bukhari, littafe na 2, shafi na 236, Hadith na 419; ko Kuma Sahih Al-Bukhari, littafe na 1, shafi na 397, Hadith na 710; Sahih Muslim, littafe na 1, shafi na 219, Hadith na 786).
A Kabbara ta Biyu Ana so ayi sauri ayiwa Annabi (Saww) Salati, duk salatin da Mutum yayi Amma salatin Ibrahimiyya Shine Wanda aka fiso a Yi domin shine salatin da ya zo a ingantattun hadisai.
A Kabbara ta ukku Ana so ne ayiwa Mamaci Addu'ar Samun Rahama, Tunda sallat anayinta ne ga Mamaci Ana so ayi Masa Addu'ah a Kabbara ta ukku, zuwa ta Hudu ko ta Biyar Zuwa Tara domin nema Masa rahamar Allah. (Abu Dawud, 2, shafi na 616-7, 2740).
Sallamewa, Akwai hanyoyi Biyu da Sunna ta amince A sallame Sallar kamar yadda Baihaqi da Tabaranj suka ruwaito a Cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi ba 127, #83).
1. Ko dai Mutum yayi sallama daya kawai ta hanyar sallamewa a Bangaren Dama. Kamar yanda Hadisin Abu Huraira (RTA) ya nuna.
2. Ko Kuma Mutum ya sallame a duka bangarori Biyu (Dama da hagu) kamar yanda yazo a Hadisin Ibn Mas'ud.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tue 13-08-219
No comments:
Post a Comment