Dukkan dangin Yabo da godiya da kirari su kara tabbata ga Allah (Swt),
Salati da Sallama su kara zuwa ga Shugaban Annabawa Fiyayyen dukkan
Halittu Muhammad 'dan Abdullahi (Saww).
Bayan haka Wannan rubutu zai haska ma akan Halaccin yin Mauludi ko kuma haramcin Yinsa a mahanga ta addini.
Farko hakika a cikin Qur'ani mai girma babu wuri daya In da Allah (Swt) yayi umurni da ayi Mauludi
Annabi (Saww) da kansa baiyi Mauludi ba kuma bai Umurci wani daga cikin Sahabbansa Suyi Mauludi ba.
Sai dai ma Annabi (Saww) ya Umurci Sahabbansa da kada su yi koyi da
Nasara Domin Sune ke yin Biki domin Annabi Isa (Alaihis Salam).
Yace, "Kada ku rike ni kamar Yadda Nasara suka riki d'an Maryam. Ni
bawa ne. Saboda haka kuce dani Bawan Allah kuma Manzon Allah (Saww)."
(Buhari).
Ya tabbata Manzon Allah (Saww) ya kan dauki ranar haihuwarsa Ranar Ibada ba ranar Biki ba kamar yanda yazo a hadisi.
An Tambaye shi (Saww) game da Azumin Litanin da yake yi, sai yace,
itace Ranar da aka haifeni kuma itace ranar da aka bijiromin da alkawali
(Muslim, al-Nisaa’i da kuma Abu Dawood).
Baya ga haka mun san Cewa, Sahabbai (RA) sun fimu So da Kaunar Annabi (Saww).
Sayyidina Abubakar (RA) Wanda Yafi kowa kusanci ga Annabi (Saww) ba'a samu yayi Mauludi ba.
Ko An samo a littafan Tarihi Cewa, Sayyidina Umar (RA) yayi Mauludi ko Sayyidina Usman ko Aliyu (RA)?
Ko an samu daga Cikin 'ya'yan Annabi (Saww) Wani yayi Mauludi? Shin
basu san da mauludin bane ko kuma Son Annabi (Saww) ne basayi?
Bayan Sahabbai Shin Imam Abu Haneefah, Maalik, Shaafi’i, Ahmad, al-Hasan al-Basri, Ibn Seereen an samu Waninsu yayi Mauludi?
An samo a hadisi Ingantacce daga Ma'aiki (Saww) Cewa, Annabi (Saww)
yace, Mafifitan mutane daga cikin Al'ummata sune Karni Na Farko
(Sahabbai Kenan), Sannan masu bi musu (tabi'ai Kenan), Sannan Masu bi
musu (Tabi'ut tabi'una Kenan)" (Bukhari, Muslim Da Tirmiziy Suka
Ruwaito).
Idan Zamuyi duba Kenan Wannan Karni Namu Yana Kasa Kwarai game da Samun fifiko kamar yadda Annabi (Saww) Ya Fada.
Shin Ba Akan soyayya bace ake yin mauludin ba? Shin munfi Sahabbai
Soyayyar Annabi (Saww) NE? Domin kuwa daga Cikin Sahabbai akwai Wanda
Manzon Allah (saww) ya kwanta barci akan cinyarsa lokacin da suke cikin
wani Kogo.. Sai Shi wannan sahabin ya rika yagar rigarsa yana tottoshe
ramukan da suke cikin kogon. Amma duk da haka akwai sauran wani rami
wanda bai samu abin tosheshi ba.
Chan sai ga wani Maciji ya
leko ta cikin wannan ramin yana so zai fito. Don haka sai ya sanya
Qafarsa ya toshe ramin don kar Macijin nan ya fito ya chutar da Manzon
Allah (saww). Macijin nan yayi ta cizonsa yana zuba masa dafi. Amma duk
da haka bai motsa ba, don kar ya tashi Manzon Allah (saww) daga Bacci.
Wannan Sahabi Shine Sayyidina Abubakar.
Shine Makusancin Manzon
Allah (Saww) na Kusa da Kusa Kai akwai ma Lokacin da Manzon Allah
(saww) yazo gidan Sayyiduna Abubakr (ra) yace masa “ALLAH YA UMURCENI
INYI HIJIRA”.
Sai Sayyiduna Abubakar yace “Ina fatan tare dani
zaka tafi?” Sai Ma’aiki yace masa “KWARAI KUWA. ALLAH YACE MIN IN TAFI
TARE DAKAI”. Sai Sayyiduna Abubakar ya fashe da kuka don murna Ganin
Allah ya zabe shi ya Raka Wanda Yafi so a Duniya Fiye da Komai.
Kai Hatta Annabi (Saww) An tambayeka Shi Duk Duniya Waka Fi so Yace,
Aisha, Aka sake Tambayar say Cikin Maza fa? Yace, "Mahaifinta (Wato
Abubakar)".
Amma Duk Irin Wannan Soyayyah dake Tsakanin
Sayyidina Abubakar da Manzon Allah Bai sa Sayyidina Abubakar Yayi
Mauludi Don tunawa Da Annabi (Saww) ba.
Bayan Sayyidina
Abubakar (rt), Sayyidina Umar (ra) na daya daga cikin zaratan mayaka
wadanda su kayi ruwa da tsaki wajen kare martabar Musulunci da ruguza
abokan fadansa.
Ya kusanci Manzon Allah (Saww) har ya kai
matsayin wazirinsa na biyu. Bayan tsabar Soyayyar da Sahabi Umar Ke yiwa
Annabi haka Allah ya karrama shi da surukuta da Manzon Allah (Saww)
inda Manzon Allah ya nemi auren 'yarsa Hafsah, aka ba shi ita, aka daura
aure, sai ta zama ita ce ta uku. Bayan Sayyidina Abubakar Yayi wafati
Sayyidina Umar NE Yayi khalifanci Amma Baiyi Mauludi ba Bai Kuma yi
Umurni da ayi Mauludi ba.
Sayyidina Usmanu Bayan zamansa Sahabi
a gun Annabi (Saww) Kuma surukine na Annbi (Saww) domin ya auri 'Ya'yan
Manzon Allah har Guda biyu Amma ba'a Taba samunsa ba dayi Mauludi ba.
Haka Dan baffansa Sayyidina Aliyu tun Yana karaminsa Ya Yarda da abinda
Annabi (Saww) Yazo dashi, domin tun Yana Dan Shekara Bakwai ko Tara ya
karbi Musulunchi Kuma surukin Annabi (Saww), Wanda ya auri Daya daga
Cikin 'ya'yan Annabi (Saww) (Kusan ma Wacce Annabi Yafi so a Cikin
'ya'yansa).
Sayyidina Aliyu Shine, Wanda ya yarda ya amince ya
kwanta akan Shimfidar Ma’aiki (saww) acikin daren da Mushrikai suke
nufin su kasheshi (Saww).
Sayyidina Aliyu ya yarda ya kwanta
amadadinsa, duk da yasan cewa zasu iya harbinsa da kibiya ko su kasheshi
tun kafin su gane cewa ba Ma’aikin bane awajen. (saww), Amma Duk da
Irin wanna So Annabi Ya yo wafati ya barshi Duniya baiyi Mauludiba Bai
Kuma yi Umurni da ayi mauludin ba.
Sayyidina Bilal Shine
Ladanin Manzon Allah (Saww) bayan Ma'aiki (Saww) Ya bar Duniya Saboda
Tsananin soyayyarsa ga Ma'aiki (Saww) Sayyidina Bilal dena kiran sallah
yayi!!
Bilalu (rta) bai Qara yin kiran sallah ba Sai rannan
Sayyiduna Umar (ra) yace masa yazo yayi (aranar da aka karbo Masallacin
Qudus).
Da Bilalu ya fara kiran sallah, yazo daidai wajen
“ASH-HADU ANNA MUHAMMADAR RASULULLAH!! Yana fada haka, sai ya fashe da
kuka, Sahabbai ma kowa sai kuka.
An ce ba’a ta’ba ganin ranar
da daruruwan Sahabbai sukayi kuka suka zubar da hawayesosai kamar wannan
ranar ba.. Sai sukaji Tamkar awannan lokacin ne Ma’aiki ya bar duniya!!
Amma Duk da Wannan Basuyi Mauludi ba.
Imamu Malik Saboda
Soyayyarsa ga Ma'aiki (Saww), Baya Fadin hadisi a Hanya, Idan Ka
tambayeshi hadisi a hanya sa Yake a dake Ka, Idan zai Bayyana hadisi sai
Yayi wanka ya Sanya Turare Saboda Tsananin Soyayyarsa ga Fiyayyen
Halitta (Saww).
Har an Ruwaito Cewa, Baya hawan Doki a Madina,
Baya saka takalma a Madina Da aka tbayeshi dalili Yace, Saboda Baya it's
takin Kasarda Annabi (Saww) Yake a Ciki, Amma Duk da Irin Wannan
Soyayyah da Yake yiwa Annabi (Saww) ba'a Samu Yayi Mauludi ba.
Shin kana tunanin duk sun Manta NE da Ranar haihuwar Annabi (Saww)? Ko
Kuma basa son shine? Ko Kuma Tunaninsu da fahimtarsu Bata Kai Cen ba?
'yan Uwana Masu Murnar Mauludi Kuyi Hakuri Dolene sai Mun Tunatarda kanmu abinda Yake daidai ko zamu Samu Rabo a Gobe Qiyama.
Muna Rokon Allah ya nuna Mana Gaskiya Kuma ya Bamu Ikon Binta, Ya Kuma Nuna Mana Karya Ya Kuma Bamu Ikon Kauce Mata.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tue 12-11-2019
No comments:
Post a Comment