Masu iya Magana sunce, Kowace Magana da lokacinta, haka kuma Kowane Lokaci da
maganar da ta dace dashi, akan haka naga dacewar inyi irin wannan rubutu a
wannan lokaci domin kowama (wanda ya sani da wanda bai sani ba duka) su san
cewa, Jemage Ba Tsuntsu bane, Domin da yawa zaka samu wasu daga cikin mutane na
kallon jemage a matsayin tsuntsu Alhali kuwa ba tsuntsu bane.
Wannan Rubutu zanyi shine zuwa ga
kalar mutane guda biyu, Na farko sune, Wayanda ke karbar kwangila domin shiga
kafafen yada labarai domin wargaza hadinkan Al’ummar musulmi. Mutane na biyu
kuma masu bayarda kwangilar (daga baya kuma su fito suce ba su sukace ayi ba).
To duk muna sane da ku da kulle kullenku na wargaza hadin kan musulmi da Allah
(Swt) ya umurcemu da yi, domin hadin kai Allah ne ya kwadaitarda yinsa a
tsakanin Al’umma. Haka kuma zagin Shugaban Musulmi (Wanda ke da Ikon fadar anga
wata ko ba’a gani ba shima wargaje zaman lafiya ne), Idan zaka dubi Alqur’ani
gaba daya zaka tarar yana karantarda hadin kai tare da biyayya ga shuwagabanni.
Misali, a cikin suratul Fatiha Allah (Swt) Yana
cewa, “Ihdinas-Siraat-Al-Mustaqeem” (Ma’ana, Ya Allah ka shiryar damu ga hanya
madaidaiciya), To meyasa Idan zakazo wajen karanta wannan ayar ta Ihdinas-Siraat-Al-Mustaqeem
meyasa baka ce, Ihdinis-Siraat-Al-Mustaqeem ba (Ma’ana Ya Allah ka shiryarda ni
ga hanya madaidaiciya) Saboda a nuna mana muhimmacin hadin kai.
Haka kuma a wajen fadin “Iyyaka na'aboudou wa iyyaka
nasta'in” (Kai muke bauta kuma kai muke neman taimakonka) Meyasa bakace, ” Iyyaka a'aboudou wa iyyaka asta'in”
(Kai nake bauta kuma kai nake neman taimakonka) ba? Ubangiji (SWT) Ya sanya
wannan ne domin ya kara nuna mana muhimmanchin hadin kai. Babu shakka Idan kaje
yin sallah ko kai kadaine (kuma ko a ina ne dole lamirin mutane na biye da kai)
domin a nuna maka muhimmanchin hadin kai.
Bayan wannan ma Saboda Ubangiji ya kara nuna mana
muhimmancin zaman lafiya ya sanya mana Sallah biyar a wuni, Sallar ma ba’a
amince ka rufe daki kai kadai kayi ba in banda Uzuri, dole sai ka fito a
masallachin Unguwa kayi sallar, Wannan kai tsaye kowa ma yana iya fahimtar
karatun cewa, ana so a nuna mana hadin kai ne.
Haka a duk sati zamu hadu kusan yan Unguwanni da
yawa muyi sallar jumu’ah wannan ma hadin kai ne ake nuna mana, Kai k ace wannan
bai Isa ba Ubangiji ya sake sanya mana Wasu salloli biyu a shekara domin kawai
a Kara nuna mana muhimmanchin hadin kai.
Duk dai domin Ubangiji ya nuna mana Muhimmanchi tare da Soyuwarsa akan mu hada
kai, Ubangiji ya sanya mana Haduwa a saman dutse guda kwaya daya tal (Dutsin
Arfa) tare da sanya Lada mai tsoka ga duk wanda ya samu damar halartar wannan
tsayuwa a wannan dutse (na Arfa), Da zaka je ka samu Tsauni a garinku ko
kasarku kaje a wannan rana kayi tsaye da zummar kayi tsayuwar arfa to wannan
tsayuwar batayi ba, ba saboda komai ba sai don Allah (SWT) Ya nuna mana
muhimmanchin hadin kai (Musamman na Musulmi).
Akan haka ne ma Allah (SWT) Yayi shuwagabanni
(Annabawa) kuma yace a bi bayansu kuma yayi shuwagabanni na Al’umma ya kuma
bada umurnin abisu a wurare daban-daban,
Misali, Idan Kuka zo zakuyi Sallah Dole ne ku sanya
dayanku a matsayin liman kuma dole ne duk abinda yayi shi zakuyi a matsayinsa
na shugaba a wajenku a wajen sallah. Bayan ya fara karatun fatiha duk zakuyi
shiru kuna saurarensa, Bayan y agama yace, Amin Sannan kuma kuce. Wannan kai
tsaye yana nuni da yin biyayya ga Shugaba (Akan abinda yake halat).
Amma yau Saboda lalaci na neman duniya wasu bata
gari wayanda basu son ganin musulunchi yaci gaba suna so su kawo suka ga wayannan
shuwagabanni. (Ya Allah ka shiryesu), Bazan Manta ba a Shekarar da ta gabata
Shiekh Ahmad Gummi Yaje wajen Shirya Atiku da Obasanjo Nan da nan gari ya
kaurace ana zaginsa tare da tsinuwa wanda kuma sam Abokan zaman mu ba haka suke
ba.
Misali a wannan tafiyar da Shiekh Ahmad Gummi yayi
yaje wajen wannan shiri a tare da shi akwai shugaban Kiristoci Rev. Hassan Maku
Kuka wanda har yaje ya dawo baka ji Kiristan ko daya ba daya gaya masa Magana
marar dadi. Wannan kai tsaye zai nuna mana kura kuran da mukeyi. Na yarda da
wasu bata garin Mutane suna Amfani damu domin mu rika batanci ga shuwagabannin
mu.
Ina wannan rubutun ne Ya’Allah Allah yasa su masu
bada kwangilar suji tsoron Allah su daina, domin babu shakka Mun sansu kuma
Idan muma muka ari Jahilcinsu muka fara bazasuji dadinmu ba ko kadan, Domin
muna nasane da ko suwaye masu bada kwangilar (Akwai Mai Gida Yamma akwai Mai
Gida Gabas) don haka Larabawa suna KARIN MAGANA Cewa, “MAN ANZARAKA FAQAD A’A
ZARAKA” (Ma’ana Wanda ya Gargadeka Hakika ya gama shiryarda kai).
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mataimaki na Musamman ga Sarkin Musulmi akan Sababbin kafofin yada labarai
Sun 07/04/2019
No comments:
Post a Comment