SAKO ZUWA GA MATASAN AREWA.
*********
Dukkan Godiya ta tabbatta ga Allah Ubangijin halittu. Salati da sallama su kara tabbata ga shugaban Manzanni, Muhammadu 'dan Abdullahi tare da iyalanSa da sahabbanSa da duk wayanda suka bi tafarkinsu har ya zuwa ranar Sakamako.
Wannan Sako Nawa ya shafi dukkanin Matasa 'yan Arewa musamman ma masu kishi tare da kaunar Arewa a zukatansu.
Hakika abinda ke faruwa a Facebook, Instagram, Twitter yana daga cikin dubban abubuwan da ke kawo matsala tare da tawayar arzikin da muke fama da su a halin yanzu.
Hakika ina lura tare da kula da cewa, babu wata rana ko wani dare da zan hau social media ba tare da na tarar wani ya aibata Shugaba Buhari ko wani daga cikin 'yan adawa ba.
Hakika zagin juna da cin mutuncin juna na daga cikin abubuwan da ke kawo matsala a wannan rayuwa da muke ciki.
Wani daga ya hau Facebook ba zaka ji ya fadi wata kalma ta alkheri abakinsa ba kawai zaka ji yana kokarin ci mutuncin da zagin 'yan adawarsa ne tare da kirkiro wasu maganganu marar tushe ya saka a bayanan nasa.
Ta 'bangaren Masoya Shugaban kasa Buhari zaka ji suna fadin, Rusashsiyar jam'iyar PDP, ko kuma Jam'iya mai kashin Mutane, ko kai tsaye kaji mutum yace, Jam'iyar kafirai.
To meye amfanin wannan? Ta bangaren 'yan jam'iyar ta PDP kuma zakaji suna Cewa, Tsohon nan ya kawo talauci, Tshohon nan yawonsa yayi yawa, Tsohon nan bazai iya gyara ba. Da dai wasu zan tuka marar amfani.
Shin ko mun Manta Abinda Allah (swt) ke fadi a citkin Alqur'ani mai Girma? Cewa, "SHIN BAKA GANI BA, YADDA ALLAH YA BUGA WANI MISALI; KALMA MAI KYAU, KAMAR BISHIYA CE MAI KYAU; TUSHENTA YANA TABBATACCE, RESSANTA KUMA SUNA CIKIN SAMA* TANA BAYAR DA ABINCINTA, A KOWANI LOKACI DA IZNIN UBANGIJINTA" (Suratul Ibrahim aya ta 24 zuwa 25).
A wani hadisi kuma Manzon Allah (saww) Cewa yayi, Sadaka ta zama wajibi a kan kowani Musulmi, Sai aka ce: To idan bai samu abin sadakar ba fa? Sai ya ce: Yayi aiki da hannayensa; sai ya amfanar da kansa, ya kuma yi sadaka. Sai aka sake tambayarsa: To idan bai samu iko ba fa? Sai ya ce: Ya taimaki ma'abucin buqata; wanda aka zalunta. Sai aka ce masa: To idan bai samu iko ba fa? Sai yace: Ya yi umurni da kyakkyawa, ko da alkhairi. Sai aka tambaye shi: To idan bai aikata ba fa? Sai ya ce: Sai ya kame daga aikata sharri; don yin hakan sadaka ne ".
Shin me yasa muke aibata 'yan uwanmu maimakon muyi shiru ko dan yin hakan ya zama sadaka a garemu?
Kusani ya Matasa Manzon Allah (saww) ya zo ne don ya zama aminci da rahama; kuma don ya tsamar da Mutane daga duhu zuwa ga haske. kamar cika alqawari, hana zalunci tare da qetare iyaka, da tsayar da adalci, da tunkude zalunci.
Ya kai me kiran PDP da Rusasshiyar Jam'iya, Ya kai mai Kiran Shugaba Buhari ya kashe Nigeria muyiwa Allah mu daina ko abubuwa zasu mana sauki.
Allah (Swt) Yana Cewa, "AKWAI TSAMMANIN UBANGIJINKU YA HALAKA MAQIYANKU, SAI YA BAKU MAYEWA A DORON QASA, DON YA GA YAYA ZAKU AIKATAWA (Suratul A'araf aya ta 129).
Hakika dukkan 'yan adawarku su mutu a barku a cikin duniya ba zata karaku da komai ba hasalima babu wani abu da zaku karu da shi sai hasara da tabewa (Allah ya tsare mu).
Ya 'dan uwa matashi kada arude ka da siyasa kaje ka manta dalilin da yasa aka halicce ka a duniya.
Da wannan Nake Rokon Matasa akan mu daina aibata junan mu saboda wani banbanci na siyasa
Haka kuma ina kira ga Shuwagabannin da suyi qoqarin tabbatar da zaman lafiya; ta hanyar tsayar da adalci, tabbatar da gaskiya. Kuma shugabani yakama ta su san wajibi ne akansu su yi qoqari wajen aikata duk abinda zai amfani talakawa, da tunkude musu abinda zai cutar da su a cikin addininsu da duniyarsu.
Yana da kyau Malamai su san cewa, sune halifofin Manzanni, kuma magada Annabawa. Don haka wajibi ne akan ma'abuta ilimi su kare al'umma daga cutar jahilci, ko rugujewar aqidu da
lalacewansu. Sannan su riqa
haskaka hanyoyi ga Mutane ta
hanyar fada musu duk wasu abubuwan da suka shige musu
duhu.
Wajibine su tashi tsaye wajen ilmantar da Mutane lamuran addininsu da Siyasa; Saboda shi malami yana gyara abinda Mutane suka bata ne, yana! kuma fadakar da su zuwa ga alkhairi, tare da yin umurni da kyawawa, da kuma hani kan munana.
Ina Rokon Allah ya amfanar da mu Tare da Amintar damu aduk inda muke.
Allah (Swt) a cikin Alqur'ani Mai Girma yana Cewa, "Ya ku Mutane lallai ne alkawarin Allah gaskiya ne; kada rayuwar duniya ta rude ku, kuma kada mai rudi (wato Shedan) ya rude ku daga
Allah" (Suratul Luqman ayata 33).
Jamilu Sani RARAH
Sat 20/02/2016.