TARIHIN DAULAR MUSLUNCI TA ANDALUS (Spain) Fitowa ta 2
*******************************************************
Ga wayanda Basu samu damar karanta Fitowa ta Farko ba Su latsa nan domin karantawa; jamilrara.blogspot.com/…/…/tarihin-kasar-andalus-spain.html…
Ci Gaban Tarihin;
Kasar Andalus Sai da ta Shekara 800 a cikin musulunci kuma daular
musulunci. Amma a Ranar da Yahudawa sunka saka Andalus a gaba sai da
wannnan kasa ta fita daga hannun Musulmi (ta tashi daga daular
musulunci).
kasan cewa duka ka'idodin musulunci da ake bi a kasar
da kewaye har sai da ta kai kafirai basa sha'awan shiga kasar, amma
randa yahudawa suka bulla a kasar ba'a dauki shekaru 50 ba saida suka
juyar da musuluncin. sunka rushe duk wani abu na musulunci akasar suka
cenja Sunayen garin (daga na musulunci zuwa nasu na kafirci).
Har sai da ta kai ta kawo Gaba daya kasar ba'a yarda ayi addinin musulunci ba.
Babban abinda ya kawo haka a kasar kuwa rashin hadin kan da yahudawa
suka sanya a tsakanin 'yan kasar. Wato babu hadin kai tsakanin kiristoci
na asali da musulman da aka tilasta masu shiga adinin kirista. Haka ma
tsakanin musulmin su kansu babu hadin kai.
To daga nan Sai tattalin arzikin kasar ya rika fadawa cikin nakaso da samun matsala tare da tabarbarewa.
Sakamakon ganin Tattalin Arzikin na tabarbarewa sai aka yi wani zaman
tattaunawa (Metting) a Ingila don idan har aka bari tattalin arzikin
kasar yana rushewa to mutanan kasar zasu watsar da kiristiyaniti zasu
koma musulmai.
A zaman tattaunawar ne sunka yanke shawarar cewa
za'a kirkiro da wani abu wanda zai hada kan 'yan kasar. A cikin
tattaunawar akayi ta kawo abubuwan da ake ganin zasu karbu ga musulmi da
kafirai amma duk wanda aka kawo aga bayayi. Anan ne wani ya bada
shawara akan a kirkiro da gasar kwallon kafa a kasar domin zata karbu
(musamman ga matasa musulmi da Kirista).
To anan ne aka kirkiro
da kwallon kafa akasar ta spain. Wannan ne yasa aka debi dalibai akaje
dasu kasar Ingila aka karantar dasu kwallon kafa da dabarunta tare da
yanda zasu sanyawa mutane Sha'awarta.
Bayan sun kware sai aka turosu kasar ta spain don su karantar da matasan kasar kwallon ta kafa.
Anan ne aka kirkiro da wani kulob na kwallon kafa mai suna sevilla
(Wanda asalin sunan wani garine na musulunci da ke cikin kasar ta Spain
mai suna Ishbiliya).
Sevilla shine kulob na farko da aka kirkiro
akasar ta Spain. (Wannan yafaru ne a shekarar 1890 zuwa 1899). daga baya
aka kirkiro da spanish king cup. Wato copa del ray, Shi wannan kofin an kirkiroshi ne wajan bikin bada sanda ga sarkin kasar.
Haka a Shekarar 1905 aka samar da kulob din real madrid. sai kum kulob din Barcalona Sai Espenyol da ganan sai visaya. Wayannan kulob kulob din su sunka maye madadin musulunci a kasar. har
sai da ya kasance musulmi yafi son kirista dan kulob dinsu da musulmi
wanda ba dan kulob dinsu ba.
Haka sarkin spain mai suna king
alfanso yace suna da wata kalma ta kiristoci wadda su sunka san sirrin
dake cikinta (Wannan kalmar).kalmar tana da wani sirri.wanda sai dan
kungiyar yahudawa yasan sirrinta.
Wannan kalmar itace real.
wannan kalmar sarkin ya bada ita a shekarar 1927 yace duk kulob din dake
son kalmar ya dauki wannan kalmar yabashi aronta.
Nan take kulob
fiye da 10 sunka dauketa anan ne anka samu real zaragoza wanda ainihin
sunan garin musulunci ne wanda ake kira saraqusda.
Sai Real
betis, Real soceida, Real valadolid wanda shima asalin sunan garin
musulunci ne mai suna valadu walid, Sai Real murcia, Real union, Real
sporting gijon sai Real madrid. (In shaa Allahu zan kawo bayanin ma'anar
Real anan gaba).
Haka ma a can baya akwai wani bayahude makiyin
musulunci na gaske wanda yana cikin wayanda sunka yaki musulunci akasar
ta Spain sunan sa santiago to shine aka sakama stadium din Real Madrid
domin Girmamawa gareshi da girmama kwazonsa.
To ta hakane akaci musulunci da yaki akasar. yanzu yawan musulmai akasar ta spain akalla akwai musulmai dubu 500 kacal. Yayin da mutanan kasar kuma yawansu ya kai miliyan 36. wanda tarihi ya
nuna kasar ta spain tayi zama kashi 95 cikin 100 musulmai ne kamar yadda
na fada a baya
Kuma a cikin yawan musulmin a kasar dubu 500 to dubu 400 ba ainahin 'yan kasar bane bakine (wato ba yan asalin kasar bane).
Daga cikin Musulmi Mutum Dubu 100 kacal sune 'yan kasa. cikin dubu 100
din mutum dubu 20 sabbin musulmai ne dubu 80 ne kawai tsofaffin
musulmai. Hakika da kwallo aka Shiga Kasar Spain aka Karya Kashin gadon bayan Musulunci a kasar ta Spain. Kuma dama yahudawa sunce kwallo addini ne mai zaman kanshi. kuma duk
wanda ya shiga cikinta yau da gobe sai ya aje addininshi ya rungumeta
don zai samu tarin kudin da ba zai iya samun kwatan-kwacinsu a addininsa
ba. Haka kuma zai kashe mata kuddin da ba zai iya kashewa a addininsa
ba. Kuma Zai bada lokacinsa lokacin da bazai iya ba addininsa ba.
Akwai wata waka da akayi a 2008 mai suna "Football is religion". haka
ma shugaban fifa a lokacin Sep Blater yace Football is more than sport
is a religing.
Kuma Wannan Gadkiya ne Saboda kiyasin da akayi a akwai masu sha'awar kwallon kafa sama da mutum biliyan 5. Yayin da yawan mutanan duniya gaba daya biliyan 7 ne. yayin da musulmai
yawan mu be kai biliyan 2 ba. kunga masu kwallo da sha'awarta sun lunka
yawan musulmai aduniya. Haka yanzu yan kwallo sune masu kudi a duniya.
Dan wasan Real madrid duk minti yana amsar sama da naira dubu 9 koda yana baccine. A duniya Bayan Bill gate 'dan Kasar America da yafi kowa Kuddi a duniya
Sai Mutumen Spain mai suna Amancio Ortega shine na Biyu da kuddi a
duniya wannan mutumen a talaka ya tashi amma ta dalilin yin tufafe wa
'yan kallo yanzu ya zama shine yafi kowa kuddi a kasar ta Spain kuma
shine mai kuddi na biyu a duniya. (Shima zuwa gaba zan kawo tarihinsa da
kuma yanda ya samu kuddinsa In shaa Allahu).
Mutane da yawa suna tambayar wai ina kulob kulob din nan ke samun wayannan makuddan kudade ne?
Watakila in na samu dama nan gaba zan kawo bayanai game da haka tare da
kawo mutu wasu abubuwan da suka Shafi Daular musulunci ta kasar Andalus
(Spain a yanzu In shaa Allahu).
Jamilu Sani Rarah Sokoto.
Mon 25/07/2016.
Tuesday, 2 August 2016
SOYAYYAH DA DADI
SOYAYYA DA DADI GA MA IYANTA
********************************
Wata Mata Ce ta yanke Shawarar tsokanar mijinta akan ta gwada shi ta gani ko yanda yake sonta
Wata Rana ya fita aiki, Cen kusan lokacin da zai dawo sai ta Janyo Biro da takarda ta fara rubutu kamar haka; "BA ZAN IYA YI MAKA SALLAMA BA A CIKIN WANNAN RUBUTUN, SABODA RAINA A BACE, KAI TSAYE INA SON IN GAYA MA NE CEWA, NI NA GAJI DA ZAMA DA KAI KUMA DAGA YAU BA ZAKA SAKE GANI NA BA, INA FATAN ZAKA CIRE NI DAGA RANKA"
Bayan ta gama Sai ta nemi Wuri ta zauna tana jiran Isowarsa, Cen Sai taji Sallamar Sa ya Shigo gidan.
Ta ajiye takardar a kan gado, Tayi maza ta buya a bayan dirowa a cikin dakin domin taga yanda zai yi idan ya karanta wannan takarda.
Ya shigo falo yayi Sallama amma shiru ba kowa (ba'a amsa ba), kai tsaye ya shiga cikin daki.
Anan ma yayi Sallama amma shiru ba'a amsa ba, Sai takarda da Biron da ya hanga saman Gado.
Ya dauki takardar ya karanta tsaf. Cikin farin cikin ya dauko wayarsa daga Aljihu ya latsa kiran wata number. Cen sai yace; "Hello my Sweet heart. Albishirinki matata ta tafiyarta yanzu ke ga mun huta da boyo don haka yanzu ma ki shirya gani nan zuwa in dauki ki." Bayan ya gama wayar ya ajiye wayar. Sai yace, kai Yau gaskiya ina cikin farin ciki da annashuwa, bari ma in dan taka rawa. Anan yayi rawa bayan ya gama sai ya juya takardar yayi wani rubutu akai.
Daga nan sai ya kama hanya ya fita ya bar dakin. Wannan mata cikin tsananin kishi da jin haushi ta fito daga in da ta buya. Tayi Sauri don ta same shi amma ina ya riga yayi nisa har ya bar gidan. Sai tace; "Ai kuwa yau ana yin ta domin sai nayi maganin wannan shegiyar karuwa."
Nan take ta dauko karamar tukunya ta zuba ruwa ta daura ruwan zafi. Tazo daki ta zauna tana cika da batsewa. Cen Sai ta tuna da ai taga yayi rubutu a takardar cen ta janyo takardar ta fara karanta rubutun da yayi akan takardar. "NI BARI IN FARA DA YI MIKI SALLAMA ASSALAMU ALAIKUM, AI NA GANKI KIN BUYA A BAYAN DIROWA KUMA KO BAN GANKI BA NA SAN KINA NAN A BOYE DOMIN KAMSHIN TURARENKI MA BA ZAI BARKI KI BUYA BA."
"DON HAKA NI DAI NA TAFI NA SAYO BURODI DA FATAN KAFIN IN DAWO KI DAURA RUWAN ZAFI DOMIN YUNWA NAKE JI. NA BARKA LAFIYA SAI NA DAWO MATATA ABIN ALFHARINA."
Jamilu Sani Rarah Yace; Kenan Ruwan da aka daura domin antayawa wacce zata shigo, Buredi Za'a antayawa su. Hahahah.
Jamilu Sani Rarah Sokoto.
Sun 17/07/2016

ME YASA AKE SON AYI JUYIN MULKI A TURKIYA?

**********************************************
Tayyip Erdogan Shine Prime Ministan Kasar ta Turkiya tun Shekarar 2002 ko kuma 2003, Tayyip ya kasance Musulmi mai son Ci gaban musulunci da Musulmi a kasar ta Turkiya.
Babu Shakka kasar turkiya kasace ta Musulunci, amma a gaskiya wasu musulmin kasar a yanzu basa kula da hakkokin musulunci.
Idan nace basa kula da hakkokin Musulunci Ina nufin, wasunsu basa bin koyarwar ta addinin musulunci.
Domin wani marubucin Kafiri 'dan kasar ta turkiya ya taba rubuta wa a cikin Littafensa Cewa, "Da ace yanda musulmin Turkiya suke haka Sauran Al-ummar musulmin duniya suke da an zauna lafiya a Duniya."
Dalilin da yasa ya fadi haka kuwa shine, Musulmin Turkiya zai iya jan Kafiri su je cikin masallachi suyi fira har da kyakkewa, wanda ni a ganina sam ba koyarwar addinin musulunchi bace.
Wannan shiyasa ma wasu daga cikin kafirrai basa daukar wasu daga cikin musulmin turkiya na yanzu a matsayin musulmi. Amma zaman Tayyip Shugaban kasa a Shekarar 2013 sai ya fara sauya halin musulmin kasar izuwa turbar Addinin musulunchi.
Daga cikin wannan juyarwa akwai lokacin Majalisar Dinkin duniya suka bada umurnin fara yin tsarin hana haihuwa a kasar. Daga jin haka nan take Tayyip ya fito a kafafen watsa labarai yake cewa; "Daga yau daga Rana mai kamar ta yau kada gidan musulmin da naji ance suna amfani da tsarin kayyade Iyali."
"Hakika addinin musulunci yana bukatar al'umma masu yawan gaske don haka kada wata macce ta kuskura ta ajiye haihuwa ba tare da dalilin musulunci ba". "Musulmi dole ne mu bi Allah da Manzonsa domin Annabin mu Mai girma yace, Mu haifafa domin yayi alfhari damu."
Baya ga wannan Shugaba Tayyip na daga cikin Shugabanin da basa tsoron Isra'il hasalima adawarsa a garesu tafi ta sauran shuwagaanni tsanani. Ko wane taro ake yi ko mai muhimmancin taron idan lokacin Sallah yayi Tayyip yakan Fita yaje yayi Sallah. Haka ma akwai wani 'dan majalisarsa mai suna Huseyin Sahin yake Cewa, "Mu musulmi hakika Shugaba Tayyip ya zamar mana wani babban Jigo domin duk zaman da muke idan lokacin Sallah yayi yakan tashi tare da umurtarmu mu je muma muyi sallah."
Tayyip Erdogan shugaba ne adili mai son Ci gaban kasarsa da addinin musulunchi don haka yana da kyau taya shi addu'ah ta samun cikakken samun kariya daga makiya masu son hanbarar da Mulkinsa.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 16/07/2016

DAB PICTURE SAI MAHAUKACI KO DABBA
DAB PICTURE SAI MAHAUKACI KO JAKI
******
Hausawa Suna karin Magna Suka Ce, "Idan Baka San Gari Ba Saurari daka." Ga dai abinda wasu turawa ke cewa game da "Dab Dance" ko "Dab Picture."
BOO WOO Yace; "Dab hanya Ce da Mashaya tabar Iblees (Wiwi) ke amfani da Ita a duk lokacin da Kwakwalwarsu ta karbi mayen tabar ta (marjuana)."
AVANT Yace; "Naje hutun karshen sati a calfonia, ina cen Sai Matata ta turomin fiye da photo guda ashirin (20 pic) na kanwarta tayi Irin daukar Wannan photo, Sai nace da matata, itama tana daga Cikin wayanda Ibless ke juya tunaninsu?"
J.ZAY Yace; "Mu Iblees ne ya bamu daukaka da Arziki da dukiya kuma shi ke karemu don haka dole ne Muyi dab a gareshi"
CAM NEWTON Yace; "Idan har ba zamu yi Dab zuwa ga Ibless ba ai mun nuna bama son Gode masa."
MIGOS Yace; "A rayuwata Iblees ya bani komai shi yasa na kirkiro da yanda zan gode masa, amma ba da nufin wasu su kwaikwaya daga gareni"
Zaku Iya Bincika wa a nan bossip.com/1260484/bow-wow-dab-origin/
Ni kuma Nace; Duk Wanda Ya san da cewa dab dance ko Picture Bautar Ibless ce kuma Yaci gaba da yi babu Shakka Zai hadu da hasara da tabewa duniya da lahira.
Hakika duk lokacin da kayi wannan dab din to kana yiwa Ibless Sujada ne, kuma sanin kowa ne ya dauki alkawari tun Wajen Allah (Swt) akan Cewa, Sai ya batar 'yan Adam.
Da Fatan Zamu Sanarda 'yan Uwan mu game da Wannan matsala da kuma kalaman da su wayannan mutane da suka kawo wannan dabi'a suka ce.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Thu 14/07/2016

Monday, 11 July 2016
GYARAN MOTAR MALAM AUDU
WAJEN NEMAN GIRA AN RASA IDO. GYARAN MOTAR MAL AUDU.
***************************************************************
Gidansu malam Audu gidane na talakawa, Gidane da basu mallaki komai ba face tufan sanyawa, gidane da basu da wani abu da zasu nuna su yi bugun gaba da shi.
Gidan na su Malam Audu ya tara mutane maza da mata (kama daga kananan yara matasa, budare da zawarawa).
Ganin irin talaucin da Su malam Audu da yayyansa da kannensa suke ciki ya sa Alh. Musa (wani makwafcinsu malam Audu). Ya sayi sabuwar mota ya ba su malam Audu domin su rika yin jigilar mutane gari-gari domin su samu kuddin da zasu rika ciyarda kansu da tufantarda 'ya'yansu.
Bayan su malam Audu sun karbo motar suka zauna domin a tsara yanda abin zai kasance. A gidan akwai dakuna guda ukku ne.
Dakinsu Mal. Audu sun kasance Su biyar ne macce ukku da kuma yayan Malam Audu wato Idi sai malam Audu din.
Sai daki na biyu mai dauke da Mutane 4 Namiji biyu macce biyu. Daki da ukku kuma duka maza ne.
Bayan an zauna anyi shawarar za'a rika yin karba-karba na tsawon Shekara daya-daya. Idan ta shekara hannun wannan ta shekara hannun wancen.
Duk wanda yake shi zai rika ciyarda yaran da kuma tufatan dasu. Haka kuwa akayi kowa ya rika yana yin nashi kokari amma Mal. AUDU kullum fadin yake yayyen nan nasa basa yin dai-dai.
Akwana a tsahi mota tayi shekara ukku, yanzu lokacine da za'a bawa Malam Audu mota domin shima ya Taimakawa gida da wannan motar.
Mazan gidansu Malam Audu dama sun dade suna son suga wannan ranar domin suga irin kokarin da malam Audu zaiyi ganin yadda ake cewa basu yi abin azo a gabi ba.
Matan Gidan kuwa Sai Murna Suke ganin Cewa, Wanda Ke ta ganin ba'a kyautata musu mota ta kai hannunsa (Alhamdulillahi).
Ashe kai Malam Audu Motar da Ya Iya Automatic Ce ba Manual ba. Kuma gashi motar ta tsufa tana bukatar cenjen Tayoyi da Shokshovers.
Nan take aka bawa Malam Audu Makullin Mota domin ya kai ta Gareji a cenja wayannan abubuwa masu neman Cenji.
Malam Audu na Shiga Mota ya tarar da Ita Manual ba Automatic ba nan take ya rude tare da tunanin mafita. Yayi statar mota ta tashi nana take Qannensa mata Suka Hau sowa da tafi (matsalarsu tazo Qarshe).
Ai kuwa yana saka Giya Sai mota ta mutu (domin bai rike kuloch ba). Nan wasu suka fara tantamar ko dai malam Audu bai iya motar ba.
Da Malam Audu ya fahimci haka sai ya leko ta merrow Yace; "KADA FA KU MANTA SUN RIKA SUN TSUDAR DA MOTAR DUK TA LALACE", Malam Audu ya Sake tayar da Motar tare da Rike kulochi.
Allah ya bada sa'ah mota ta tashi Malam Audu ya fara tafiya da ita, amma fa idan tayi nan mota tayi cen (sai ya tabo karshen titi ya tabo karshen titi).
Yanzu dai mota na hannun Malam Audu ya kama hanyar wajen gyara ko dai yakai lafiya ko kuma motar ta ida lalacewa (Imma bai ture wasu suka mutum ba). Kar wajen neman gira a rasa Ido.
Jamilu Sani Rarah.
Sat 14/05/2016.

KASHE-KASHEN KUNGIYOYIN ADDINI
KASHE-KASHEN KUNGIYOYIN ADDINI TARE DA BAYANIN SU.
***********************************************************
Wannan Rubutu da Zan Fara gabatarwa ba yana nufin yin Suka ga wata akida ba ko kuma nufin munana matsalar wata akida ba.
A'a rubutune da zai taimaka kwarai da gaske domin fahimtar kowacce akida da kuma tsare-tsaren ta da kuma banbancin ta da saura domin ganin An Samu fahimtar juna.
Yana da kyau mutum ya tsaya da kyau ya karanci wannan rubutun tare da fahimtarsa domin ganin an daina samun sabanin da ake samu a cikin musulmi.
KASHE-KASHEN KUNGIYOYIN ADDININ DA KE AKWAI.
1. Izala.
2. Wahahiyyah.
3. Salafuyyah.
4. Diyobandiyya.
5. Bareliyya.
6. 'Yan Islama.
7. Kur'aniyyah.
8. Shi'ah.
9. Shi'ah Ashriyyah.
10. Shi'ah Nizariyyah.
11. Shi'ah Musta'aliyyah
12. Shi'ah Shi'ah Alebiyyah.
13. Shaykiyyah.
14. Shi'ah Usuliyyah.
15. Shi'ah Akhbariyyah.
16. Shi'ah Isma'iliyyah.
17. Shi'ah Zaidiyyah.
18. Sufanci.
19. Darika.
20. Darikar Kadiriyyah.
21. Nasiriyyah-Kaduriyyah.
22. Tijjaniyyah.
23. Ibrahimiyyah-Tijjaniyyah.
24. Chishtiyyah
25. Suhrawardiyyah.
26. Bektashiyyah.
27. Nakshibandiyya.
28. Uwaisiyyah.
29. Mu'utazilawa.
30. Kalamanci.
31. Kadiriyyah.
32. Jabariyyah.
33. Ash'Ariyyah.
34. Maturidiyya.
35. Athariyyah.
36. Murjiyyah.
37. Khwarij.
38. Ibadiyya.
39. Surfriyya.
Abin da Zamu lura da shi anan shine, Kowacce kungiyya a cikin wadannan kungiyoyi dana zayyano suna da magoya baya dai-dai nasu, kuma addinin da kowacce cikinsu ke taqama da shi shine musulunci.
Musulunci kuma shine tafarki madaidaici wato addinin da Allah ya ambace shi da addini.
Allah (Swt) a Cikin Suratul Al'imran yana Cewa; "LALLE NE ADDINI A WURIN ALLAH, SHINE MUSULUNCI" (suratul Al'Imaran Aya ta 19).
Kowane daga cikin wayannan kungiyoyin yana ikrari ne akan cewa, shi mabiyin addinin Islama ne. In shaa Allahu kowannensu zan kokarta kawo bayannan su tare da hujjojinsu domin kokarin fadintar sabanin da yake tsakani.
Jamilu Sani Rarah
Fri 13/05/2016.

YA ZAMU KOYAWA 'YA'YAN MU SALLAH?
YA ZAMU KOYAWA 'YA'YAN MU SALLAH?
*************************************
'Ya ta Shekaranta 12 amma sallah ta zamar mata kamar wasu kaya a ka (domin duk yanda nayi da ita bata yin Sallah).
Wata Rana na Umurce ta da taje tayi Sallah. Na tsura mata ido har ta tafi taje ta dau sallaya ta shiga 'daki bata yi wani dogon dadewa ba ta fito a zuwan tayi sallah din amma ni na san bata yi sallar ba.
Na tambayeta ko ta gabatar da Sallar ta kuwa? Ta amsa min da "Eh", amma ni na san bata yi sallar ba. Cikin tsananin fushi na wanke ta da mari har sai da ta kife a kasa.
Daga baya kuma sai tausayin ta ya kamani, amma ba yanda zanyi domin saboda na gaji da halinta (na rashin yin Sallah). Nayi nadamar marinta da nayi na dauki alkawarin ba zan kara marin ta haka ba.Domin na san wannan ba zai amfani 'yata da komai ba.
Wata rana wata Qawata ta gaya min Cewa, takai ziyara wajen wata Qawarta, kuma Qawarta ta ba wata mai kula da addini ba ce sosai, amma a duk lokacin da aka kira sallah takan lura da 'ya'yan Qawartata sukan yi sauri su ta shi suje Sallah ba tare da an tsawatar musu ko tunatar musu ba.
Qawar tawa taci gaba da gayamin cewa, tayi mamaki kwarai a lokacin da ta ga yanda yaran nan ke lura tare da kula da Sallah. Sai ta tabbayi Qawartata Cewa, "Ko me yasa na ga yaranki daga zarar an kirayi sallah suke tashi ba tare da ke tsawatar musu ba?"
"Sirrin abin tun kafin Inyi aure na kasance Ina karanta Wannan addu'ar kowace rana kuma har yau ban daina karantawa ba". Haka ta gayawa Qawata.
Qawar tawa ta bani shawarar ni ma idan ina son 'ya'yana su kasance haka to nima In dukufa wajen karanta wannan addu'ar a koyaushe.
Tun lokacin da na dukufa wajen karanta wannan addu'ar 'yata ita ce ta farko wajen gabatar da sallah a gidan mu ba tare da an tsawatar mata ba.
Takan kuma tashi sallar asuba ba tare da ta saka alam ba. Haka ma duka 'yan uwanta da aka haifa daga baya suna sallah a lokaci.
Har ma dai aka kai itace ke tayar da mu sallar asuba kuma ita ke gaya mana lokacin sallah idan yayi Na san kun Matsu kuji Wace addu'ah ce nake karantawa to aya ta 40 ce a cikin Suratul Ibraheem
ِ
Wato, "Rabbi-Ajal'ni muqeema salaati, wa min Dhurriyyati, rabbana wataqabbal duaa" Hakika duka baya shiryar da 'ya'ya addu'ah ce ke shiryar dasu. Da fatan za'ah rika karanta wannan ayar da niya.
Jamilu Sani Rarah
Thu 19/05/2016

Subscribe to:
Posts (Atom)