Tuesday, 2 August 2016

ME YASA AKE SON AYI JUYIN MULKI A TURKIYA?

ME YASA AKE SON AYI JUYIN MULKI A TURKIYA?
**********************************************

Tayyip Erdogan Shine Prime Ministan Kasar ta Turkiya tun Shekarar 2002 ko kuma 2003, Tayyip ya kasance Musulmi mai son Ci gaban musulunci da Musulmi a kasar ta Turkiya.
Babu Shakka kasar turkiya kasace ta Musulunci, amma a gaskiya wasu musulmin kasar a yanzu basa kula da hakkokin musulunci.

Idan nace basa kula da hakkokin Musulunci Ina nufin, wasunsu basa bin koyarwar ta addinin musulunci.
Domin wani marubucin Kafiri 'dan kasar ta turkiya ya taba rubuta wa a cikin Littafensa Cewa, "Da ace yanda musulmin Turkiya suke haka Sauran Al-ummar musulmin duniya suke da an zauna lafiya a Duniya."
Dalilin da yasa ya fadi haka kuwa shine, Musulmin Turkiya zai iya jan Kafiri su je cikin masallachi suyi fira har da kyakkewa, wanda ni a ganina sam ba koyarwar addinin musulunchi bace.

Wannan shiyasa ma wasu daga cikin kafirrai basa daukar wasu daga cikin musulmin turkiya na yanzu a matsayin musulmi. Amma zaman Tayyip Shugaban kasa a Shekarar 2013 sai ya fara sauya halin musulmin kasar izuwa turbar Addinin musulunchi.

Daga cikin wannan juyarwa akwai lokacin Majalisar Dinkin duniya suka bada umurnin fara yin tsarin hana haihuwa a kasar. Daga jin haka nan take Tayyip ya fito a kafafen watsa labarai yake cewa; "Daga yau daga Rana mai kamar ta yau kada gidan musulmin da naji ance suna amfani da tsarin kayyade Iyali."
"Hakika addinin musulunci yana bukatar al'umma masu yawan gaske don haka kada wata macce ta kuskura ta ajiye haihuwa ba tare da dalilin musulunci ba". "Musulmi dole ne mu bi Allah da Manzonsa domin Annabin mu Mai girma yace, Mu haifafa domin yayi alfhari damu."

Baya ga wannan Shugaba Tayyip na daga cikin Shugabanin da basa tsoron Isra'il hasalima adawarsa a garesu tafi ta sauran shuwagaanni tsanani. Ko wane taro ake yi ko mai muhimmancin taron idan lokacin Sallah yayi Tayyip yakan Fita yaje yayi Sallah. Haka ma akwai wani 'dan majalisarsa mai suna Huseyin Sahin yake Cewa, "Mu musulmi hakika Shugaba Tayyip ya zamar mana wani babban Jigo domin duk zaman da muke idan lokacin Sallah yayi yakan tashi tare da umurtarmu mu je muma muyi sallah."

Tayyip Erdogan shugaba ne adili mai son Ci gaban kasarsa da addinin musulunchi don haka yana da kyau taya shi addu'ah ta samun cikakken samun kariya daga makiya masu son hanbarar da Mulkinsa.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 16/07/2016

No comments:

Post a Comment