Tuesday, 2 August 2016

SOYAYYAH DA DADI

SOYAYYA DA DADI GA MA IYANTA
********************************

Wata Mata Ce ta yanke Shawarar tsokanar mijinta akan ta gwada shi ta gani ko yanda yake sonta
Wata Rana ya fita aiki, Cen kusan lokacin da zai dawo sai ta Janyo Biro da takarda ta fara rubutu kamar haka; "BA ZAN IYA YI MAKA SALLAMA BA A CIKIN WANNAN RUBUTUN, SABODA RAINA A BACE, KAI TSAYE INA SON IN GAYA MA NE CEWA, NI NA GAJI DA ZAMA DA KAI KUMA DAGA YAU BA ZAKA SAKE GANI NA BA, INA FATAN ZAKA CIRE NI DAGA RANKA"

Bayan ta gama Sai ta nemi Wuri ta zauna tana jiran Isowarsa, Cen Sai taji Sallamar Sa ya Shigo gidan.
Ta ajiye takardar a kan gado, Tayi maza ta buya a bayan dirowa a cikin dakin domin taga yanda zai yi idan ya karanta wannan takarda.

Ya shigo falo yayi Sallama amma shiru ba kowa (ba'a amsa ba), kai tsaye ya shiga cikin daki.
Anan ma yayi Sallama amma shiru ba'a amsa ba, Sai takarda da Biron da ya hanga saman Gado.
Ya dauki takardar ya karanta tsaf. Cikin farin cikin ya dauko wayarsa daga Aljihu ya latsa kiran wata number. Cen sai yace; "Hello my Sweet heart. Albishirinki matata ta tafiyarta yanzu ke ga mun huta da boyo don haka yanzu ma ki shirya gani nan zuwa in dauki ki." Bayan ya gama wayar ya ajiye wayar. Sai yace, kai Yau gaskiya ina cikin farin ciki da annashuwa, bari ma in dan taka rawa. Anan yayi rawa bayan ya gama sai ya juya takardar yayi wani rubutu akai.

Daga nan sai ya kama hanya ya fita ya bar dakin. Wannan mata cikin tsananin kishi da jin haushi ta fito daga in da ta buya. Tayi Sauri don ta same shi amma ina ya riga yayi nisa har ya bar gidan. Sai tace; "Ai kuwa yau ana yin ta domin sai nayi maganin wannan shegiyar karuwa."

Nan take ta dauko karamar tukunya ta zuba ruwa ta daura ruwan zafi. Tazo daki ta zauna tana cika da batsewa. Cen Sai ta tuna da ai taga yayi rubutu a takardar cen ta janyo takardar ta fara karanta rubutun da yayi akan takardar. "NI BARI IN FARA DA YI MIKI SALLAMA ASSALAMU ALAIKUM, AI NA GANKI KIN BUYA A BAYAN DIROWA KUMA KO BAN GANKI BA NA SAN KINA NAN A BOYE DOMIN KAMSHIN TURARENKI MA BA ZAI BARKI KI BUYA BA."
"DON HAKA NI DAI NA TAFI NA SAYO BURODI DA FATAN KAFIN IN DAWO KI DAURA RUWAN ZAFI DOMIN YUNWA NAKE JI. NA BARKA LAFIYA SAI NA DAWO MATATA ABIN ALFHARINA."

Jamilu Sani Rarah Yace; Kenan Ruwan da aka daura domin antayawa wacce zata shigo, Buredi Za'a antayawa su. Hahahah.

Jamilu Sani Rarah Sokoto.
Sun 17/07/2016

No comments:

Post a Comment