Monday, 11 July 2016

GAJERUN KALAMAN DR. BILAL PHILIPS GUDA 20



GAJERUN KALAMAN DR. BILAL PHILIPS GUDA 20 AKAN MANUFAR KARATUN ALQUR'ANI.


1. A cikin Watan Azumi Allah (SWT) ya saukarwa da Annabi Muhammad (SAWW) da Al-qur'ani mai Girma.

2. Hakika Allah (Swt) ya saukar da Alqur'ani ne don Ya zama rahama a gare mu (kamar yadda bayanin hakan yazo a cikin Suratul Al-Baqara).

3. Yawaita Karanta (Al-Qur'ani) a cikin Wannan wata (na Azumi) ba Karamar lada ake samu ba.

4. Daga cikin ladubban karatun Alqur'ani akwai buqatar tunani a kan ma’anoninsa yayin karatun
sa. Wannan kusan shi ne mafi muhimmancin ladaban karatun Alqur’ani gaba daya.

5. Al-Qur'ani gaba dayansa waraka ne, idan kana dauke da Cutukkan zamani kamarsu HIV, Cancer to ka dukufa wajen karanta shi Zaka samu waraka da Iznin Allah.

6. Allah (Swt) a cikin Alqur'ani Yana Gaya mana Cewa, "Al-Qur'ani Waraka ne amma ga muminnai". Don haka makawar mumini ya yawaita karanta (Al-Qur'ani) to Allah zai bashi lafiya.

7. Idan kana son ka samu labarai da sakonni daga Ubangijinka to ka nemi al-Qur'ani ka karanta.

8. Dukkan Wani Sako da yazo a Cikin Al-Qur'ani to zaka same shi a cikin Suratul-Al-bakara.

9. Ka tsaya ka Karanci suratul Bakara tare da Sanin sakonnin da take dauke da shi, shiya fiye ma da ka karance duka Al-Qur'ani amma baka san ma'anarsa ba.

10. Ko mu karanta Al-Qur'ani ko kada mu karanta, babu abinda zai rage ko kara Allah (SWT) da shi. Don haka 'dan Adam ya karanta (Al-qur'ani) domin ya samu albarkar da ke ciki.

11. Matan da ke dauke da Jinin Al'ada zasu iya karanta Al-Qur'ani da ka. Ba tare da sun dauki (Shi Al-Qur'anin) ba, domin su samu albarka da kariyar da ke cikin karanta shi.

12. Makawar Al'umma basu chanja halayensu ba to Allah ba zai fitar dasu daga kangin da suke ciki ba. Don haka mu cenja Rayuwar mu ta hanyar karanta Al-qur'ani.

13. Zaka samu musulmi masu kallon Kwallo (ball) Idan anyi abu mai kyau a cikin wasan zasu tafa da nuna jinjina amma basu cika damuwa da yin sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah) ba.

14. Idan har kana cikin tsanani to kafin ka koka kafara yin sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah).

15. Idan har ka tsinci kanka da samun wani alheri to ka gaggauta yin Sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah) domin nuna godiya akan wannan Ni'Imar.

16. Sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah) ana yin ta ba tare da Alwala ba.

17. Sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah) Mata zasu iya yin ta koda suna a cikin Jinin Al'ada. Don haka a kowane lokaci farin ciki ko bakin ciki ya same ka ka gaggauta yin ta.

18. Yaren larabci Shine yare na biyu ga kowane dan adam (musulmi da ma wanda ba musulmi ba), domin idan bahaushe yaje kasar chana ya tarar ana kiran sallah da yaren Chananci ba zai fahimci me suke yi ba, amma makawar akayi da larabci to, kowa ma yasan kiran Sallah ne.

19. Idan har ka samu damar karanta Al-Qur'ani ka qi kayi to babu makawa wahalhalu da matsaloli zasu dabai-baye ka.

20. Kada mu bari mu koma ga Allah (Swt) ba tare da Munyi Sujood al-shukur (Sujudar godiya ga Allah) ko sau daya ne a rayuwar mu ba.

Wayannan kalamai zamu iya kiran Su da gajerun Kalamai a baki ko a karance amma ta fuskar fahimta tarin tulin Ilmi ne a dunkule tattare a wuri daya.

Dr. Bilal phillips (Abu Ameena) ya gabatar da Wayannan Kalamai ne a muhadarar da ya gabatar a Usman Danfodio University Sokoto akan manufar dake cikin karanta Al-Qur'ani a jiya Laraba 15/6/06.

Jamilu Sani Rarah Sokoto.
Thu 16/06/2016

KARAMAR TAMBAYA TA HANASHI SAMUN MATA



KARAMAR TAMBAYA TA HANA SHI SAMUN MATAR DA YAKE SO.
***********************************************************
Wani Yaro dake Mutuwar So da kaunar wata Yariya ya Rasata saboda kasa amsa wata karamar tambaya da akayi masa. Yaron ya kasance dan masu fada aji a garine bayan haka kuma ya kammala karatunsa a matsayi na mastas kuma ya samu aiki wata babbar ma'aikata a kasashen larabawa.

Yazo wajen mahaifin yariyar da yake so aure, ya ce da mahaifin yarinyar,"Baba na kammala karatuna, Na mallaki mota biyu da gida daya sannan Ina da filaye guda 4 wayanda zanyi gini in sanya 'yan haya, domin bana son in dogara ga aikin gwamnati".

"Nazo ina son 'yarka da aure hakika zanyi farin ciki idan ka bani aurenta, kuma zan kula da ita. Kuma koda ace wani ya kashe mata kuddi hakika zan iya biyansa ko nawane domin ina sonta".

Mahaifin yarinyar yayi murmushi sannan ya dubi yaron daga bisani yace da shi, "Hakika babu wanda ya kawo kuddi balle ka biya, sai dai zan yima tambaya guda daya".

"Idan ka bani amsar tambayata zan yarde ma ka auri 'ya ta, ba ina bukatar kuddinka ko gida ko wani abu ba, a'a ina bukatar amsar wannan tambaya daya ce kawai".

Yaron yayi farin cikin da jin hakan tare da sonjin wacce irin tambya ce za'ayi masa.

Mahaifin yarinyar ya kalli Idanuwan yaron Sannan yace dashi, "Ka amsa min sau daya kawai, A karfe nawa Ladanin Unguwarku yake kiran Sallar Subahin?".

Nan da nan jikin yaron ya fara rawa, ya juya nan ya juya cen, bayan yayi dan tunani kadan sai yace, "Ina ganin Karfe 4 ake kira...a'a karfe 3:30...a gaskiya Baba ban sani ba".

Mahaifin yarinyar cikin Murmushi yace da yaron, ”I don’t care of your high status or your bank account! My daughter is so precious, she is like a princess to me with her Hijab and purity so she needs someone who treats her like a queen!

No one would make her happy more than a man who fears Allah and obeys Him. Only a righteous husband would give her an unlimited happiness by helping her to get closer to Allah”.

Nan take yaron yayi godiya ya tashi. a hanyarsa ta komawa gida ya rika tunanin a zuciyarsa cewa, ashe mahaifinta ma 'dan bokone? Wato a tunaninsa tunda yana riko da addini Shi ba d'an boko bane
 
Jamilu Sani Rarah Sokoto.

KYAKYKYAWAR MU'AMULA NA SA A KAUNACI MUSULUNCI


KYAKYKYWAR MU'AMULA NA SANYA A KAUNACI MUSULUNCI
************************************************************
A lokacin da aka fara yin sufuri da jirgin European Airline, da akwai wani musulmi mai tsoron Allah a zuciyar shi a cikin Jirgin. Shi Wannn bawan Allah yana zaune ne a wurin da masu fada aji suke zama (Wato first class section a turance).

A daidai lokacin da Jirgi ya fara tafiya sai ma'aikaciyar Jirgi (wato air hostes) ta gabatar masa da kyautar kofin giya wadda kamfanin Jirgin ya dauki nauyin bayarwa ga fasinjojin jirgin.

Cikin ladabi da girmamawa ya kalle ta yace, "Nagode aini bana shan Giya" ta kalle shi cikin natsuwa ta gyangyada kai (alamar mamaki).

Wannan matar ta damu ainun da Qin shan Wannan giya da yayi, nan take taje ta sanarda Manajan akan akwai wani da yaki karba "..Wai baya shan Giya".

Manaja yayi tattaki har wajen wannan bawan Allah, Shima dai dauke yake da Giyar Yace da wannan mutumen; "Shin ko akwai abinda kake tunani game da mune? Hakika ka karba kasha wannan kyauta ce ta musamamman daga kamfanin mu".

Bawan Allah Cikin Ladabi Ya kalli Manajan Yace da shi, "Ni Musulmi ne kuma musulmi basa shan Giya".

Manaja yace yaji amma yana son ya karba ya shan ko da sau daya ko biyu ne domin wannan rana ta yau ranar farin ciki ce.

Wannan bawan Allah yayi murmushi ya dubi manajan Yace da shi, yaji zai sha amma suje ya fara bawa direban Jirgin ya fara sha sannan shi ma yasha.

Cikin mamaki manajan Jirgin Yace; "taya Direba zai sha Giya Alhali yana aiki (na jan jirgi?) Ai da zarar ya sha giya wannan jirgin zai samu Hatsari".

Wannan bawan Allah ya kalli wannan Manajan Yace da shi, "Ni musulmi ne sannan akoda yaushe ina kan aikina na tsare Imani na Idan har na sha wannan barasar to kuwa zan sanya rayuwa ta cikin hatsari domin zan rasa Imani na".

Allahu Akbar, Wannan ta sa Wannan manaja da wannan matar duka suka girgiza suka shiga tunanin karbar Musulunci daga hannun Wannan Bawan Allah.

Hakika haka Ake Son Musulmi ya siffantu da kyawawan dabi'u da kuna iya zance kada ya mayarwa da musulmi da wanda ba musulmi ba magana cikin zafi ko jin haushi.


Jamilu Sani Rarah Sokoto
Fri 24/06/2016

SABON SALO MUSULMI DA BAUTAR SHAIDAN (LA)

SABON SALO MUSULMI DA BAUTAR IBLESS (L.A).
***********************************************



Masu Bautar Shaidan (LA) wato Illuminiti Sun rubuta a Cikin Coustitution dinsu cewa, "Mallakar Media kamar Mallakar Public ne" ma'ana Idan Suka Mallaki Hanyoyin Sadarwa (Kamarsu, TV, Facebook, Istagram, youtube) to kamar Sun mallaki gama garin al'umma ne.

Babu shakka Zancensu Yana so ya zama gaskiya koma In ce ya zama gaskiya muddin bamu tashi tsaye ba.
Akwai wata Sabuwar Rawa ko Kuma daukan Photo da ya fito Sabo Wanda ake Kira da DAB STYLE ko kuma DAB DANCE. Babu shakka wannan salo ne na bautar Ibless (LA) da masu bautarsa (LA) suka fito dashi a kokarinsu na jan ra'ayin jama'a game da wannan bauta.

Dab Dance ko kuma Dab Style ta samo asaline daga Wani mawaki da ake kira da Migos wanda shine Mawakin da ya fara yin wannan rawar har ya yi mata waka.
Ana haka sai dan wasan kwallon karfin nan wato Cam Newton ya watsa wannan rawa a duk lokacin da ya ci wasan sa na kwallon karfi.

Daga nan kuma sai wani mawaki mai suna Jay Z (Wanda kusan kowa yasan Cewa, Shine Shugaba na masu bautar Shaidan) yayi wannan rawa a cikin Wata Wakarsa mai suna “Fuck With Me You Know I Got It”.
Babu shakka daga nan Sai Sauran mawaka da 'yan Kwallon kafa suka dauki wannan dab dance din suka juyar da shi a zuwa dab Picture.

Ma'anar Dab dai shine, Rufe Fuska da hannun hagu ko dama sai hannu dayan a mikar dashi. Masu shan tabar Iblis wato Wiwi sun kasance Suna amfani da wannnan kalma ne a lokacin da suka zuqi taba wiwi din suka sha. Ma'ana idan ka zuqi tabar ta wiwi sai ka noke fuskarka a cikin hannunka daya shi kuma dayan ka rike tabar ta wiwi da shi.

Migos wanda ainahin Shine ya kawo wannan rawar ta Dab Dance Abinda yake Nufi da Dab Shine "Dimands are bright". Dimands kalmace da aka dauko daga yaren Greek adámas, wacce take nufin abinda baya karyewa ko kuma baya samun wani nakkaso ko baya samu wata tangarda.

"Dimands are bright". Ma'ana Lu'ulu'u Mai haske ne (a yanda suke nufi shine Shaidan Kenan) ku lura Dimands aka ce ba Diamonds ba, duk da Shima Lu'u'lu'u yake dauka amma wannan Shaidan Iblees Suke nufi. Don haka don Allah Mu guji Yin wannan Photo da Sunan Wayewa ko da Sunan Burgewa, ko kuma da sunan mun ga wani babban 'dan film ko mawaki ko dan kwallo yayi. Hakika da yawa daga Cikin Wayannan 'yan Film din Da 'yan Kwallo da Mawaka yaran Shaidan Ne masu bautarsa ke nema masa passenger.
Duk wani mawaki ko dan film ko dan kwallo da kuka ga yayi Dab to babu Shakka yana mika Bautarsa ne ga Mai Gardama Shaidan (LA).

 Zaku Iya Kallon Wata Wakarsu a nan https://m.youtube.com/watch?v=oet8spdBCtA Ina Fatan Duk Bawan Allah da Yaci Karo da Wannan Sako nawa Don Allah Ya sanarwa da 'yan Uwa domin Mu kula.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 11/07/2016

Thursday, 21 April 2016

MUTUWAR AURE A KASAR HAUSA INA MAFITA?

MUTUWAR AURE A KASAR HAUSA INA MAFITA?

Allah (SWT) da kansa ya kira 'ya macce da sunan Nutsuwa a gun mazaje, duk ilmi, kuddi ko Sunan da 'da namiji yayi bazai taba samun nutsuwa ba sai tare da 'ya mace.

Shi yasa Allah da kansa a wani wuri a cikin Alqur'ani ya kirayi 'ya'ya mata da lafazin Sutura a gun maza ba don komai ba domin anuna mana muhimmanci da kimar 'ya'ya mata a gidan duniya. Domin duk kuddinka ko Ilmin ka ba zaka iya tafiya tsirara ba.

To amma wani abin ban haushi a yanzu zaka tarar mazajen yanzu basa kula da wannan qima da martabar da Allah (Swt) Ya baiwa 'ya'ya mata. Wani babban abin haushi da ke faruwa a wannan kasa tamu, musamman a wannan bangaren namu na Hausa Fulani.

Tun ina Qidayawa har na gaji da kirgawa na zubawa sarautar Allah ido tare da addu'ar Allah ya kawo sauki game da wannan matsalar

Ko kunsan me nake kirgawa? Kananan 'Yan mata wayanda ake yawan saki ba tare da sun mayar da shekara da yin aure ba. Wannan abu ba karamin 'daga min hankali yake ba.

Wallahi nasan kusan macce 5 zuwa 6, 7 da suka fito daga gidan mijinsu ba tare da sun mayar da shekara a gidan na aurensu ba. Kuma galibi duk zaka same su yara 'yan kanana wayanda shekarunsu ba zasu haura 23 zuwa da 24 ba.

Duk lokacinda aka sanya muhawara akan me yake kawo sakin aure a kasar Hausa zakayi tajin bayanai daban-daban. Wasu zaka ji sunce rashin ladabin 'ya macce ne, Wasu kuma zaka ji sun ce rashin tsafta da kula da mai gida ne, Wasu kuma zaka ji sun dauki laifin gaba daya sun daura shi akan namiji suce rashin hakuri ne.

A iya bincike da nazarin da nayi game da mace-macen Aure da ke faruwa a yanzu na gano wasu daga cikin wayannan dalilai da ke sanya saurin rabuwa a tsakanin ma'aurata.

Da farko akwai rashin sanin ma'anar aure da kuma raahin sanin darajar da ke cikin aure, galibi maza da matanmu duka muna suna yin aure ne ba don zamansa ibada ba. A'a suna yine saboda dakushe sha'awar da ke damunsu. To da zarar akayi aure wannan sha'awar ta kau ko kuwa sai kowa yaji ya gaji da 'dan uwansa. Domin dama ita sha'awa kamar wutar karace saurin cenyewa take.

Abu na biyu kuma akwai rashin bin ka'idojin da musulunci ya sanya wajen yin aure. Yana daga cikin abinda Manzon Allah (Saww) ya karantar da musulmai Ya ce, Ku zabar wa 'ya'yanku uwa tagari.

Ta yaya zamu zabarwa 'ya'yanmu Uwa ta gari? Anan ma Annabi (Saww) bai barmu a kara zube ba sai da ya gaya mana yanda zamu zabe ta. Yana daga cikin hanyoyin zaben mata tagari yin istihara (addu’a ce manzon Allah (Saww) ya koyar da al’umarsa. Duk  wanda  ya tashi neman aure ya yi istihara.Ita wannan sallar raka’a biyu ake yi sannan a karanta addu’ar).

A addininmu musulunchi ba'a yarda mutum ya fara nemman aure ba, ba tare da ya yi istikara ba. Bayan ya yi istihara sai kuma ya shawarci mutanen kirki da wadanda suka santa.

Domin mace ita ce uwa ta farko ga ‘ya’yanka. Yara suna tasowa ne a kan dabi'unta da halayenta. Haka a addinance ba'a a lura da kyawon mace wajen aure, domin ba shi ne mazon Allah (Saww) ya ce a lura da shi ba.

Manzon Allah (Saww) ya ba da
labari yake cewa, Ana auren mata saboda abu hudu (4): Wasu suna auren mace saboda dukiyarta, wasu kuma suna auren mace
saboda kyawonta, wasu kuma suna auren mace saboda danginta, wasu kuma suna auren mace saboda addininta. Sai Annabi (Saww) ya ce na horeka da ka aure ma’abociya addini.

A Wani hadisin da ibn Maajah ya ruwaito Manzon Allah (Saww) ya ce, “Kada ku auri mata saboda kyawon su, kyawonsu yana iya
juyar da ita.( ta kasance mai girman kai.) Sai ya qara da cewa, “Kada ku auri mata saboda dukiyarsu: Ana sa ran dukiyarsu ta sanya su girman kai. Sai dai ku aure su saboda addini.

Wani mutumi ya je majalisin Safiyanu bn Uyaynah ya ce, “Ya Aba Muhammad ina fama da matata tana wulaqanta ni matuqar wukaqantawa. Sai Safiyanu bn Uyaynah ya yi shiru kadan sannan ya ce, “Me yiwuwa ka aure ta ne saboda ka samu daukaka.” Sai mutumin ya ce, “Lallai haka ne. Sai ya ce, “Duk wanda ya auri mace saboda neman daukaka, to Allah zai qasqantar da shi. Wanda kuma ya auri mace saboda dukiya Allah
zai jarabce shi da talauci. Wanda ya auri mace saboda addini to Allah zai hada masa daukaka da dukiya da addini.

Kunga kenan wannan duk yana nuna mana kada muyi aure don sha'awar macce tana fara ko tana da kyawo ko 'yar gidan masu kuddi ce da sauransu. A'a anan ana so ka dauki aure a matsayim ibada kuma ka auri macce ba dan komai ba sai don addininta

Ko kun san muhimmancin auren macce mai addini? Idan baku sani ba ku tsaya kuji. Imamu Shafi’i babansa ya rasu tun yana dan jariri amma da yake uwarsa mai addini ne a wajenta ya haddace Qur’ani mai girma.

Imam Ahmad bn Hambal ya ce shekaransa talatin da matarsa amma bata taba saba masa ba ko jayayya da shi bata taba yi da shi ba, Amfanin mai addini ke ne kenan.

Babu shakka rashin auren macce mai addini yana daga cikin manyan dalilan da suke kawo mutuwar aure a wannan zamani da muke ciki.

Don haka yana da kyau maza a ji tsoron Allah a rika yin Aure don Allah ba don Sha'awa ko daular gidansu yarinya ba yana da kyau a rika daukar aure a matsayin bauta babu shakka wannan zai rage mace-macen auren da ke faruwa a zamanin nan.

In shaa Allahu zan dakata anan a gaba zan kawo siffofin macce mai addini da kuma irin Suma mata mazan da ya kamata su aura da kuma yanda za'a rika walwale husuma da zarar ta faru tun ba'a kai ga saki ba. Dan uwanku a Musulunchi Jamilu Sani Rarah Sokoto Nigeria.

In da nayi dai-dai Allah ka bamu lada mu duka In da nayi Kuskure ba daga ni bane daga Shaidanne Allah ka yafe mana.

Tuesday, 19 April 2016

NIGERIA KASARMU TA GADO

Nigeria Kasarmu Ta Gado.
********
Shuwagabanninmu na Sayen Manyan Motoci domin hawa wasummu Suna Bukatar In da Zasu sami kuddin Sanyen Abinci. Wasunmu ma na kwana da Yunwa.

ShuwagabanninMu na Daukar Shatar Jirgin Sama Su tafi Kasashen Waje. Amma a koda yaushe suna gaya mana Cewa An sace Kuddin Kasa.

ShuwagabanninMu na Biyawa 'Ya'yansu Manyan Makarantu a kasashen waje amma kullum Sai Su ce mana an wargaza mana kasarmu.

Shuwagabanninmu na Cin abinci su koshe su kwana wuri mai kyau amma idan munyi magana ace mana mun cika Gajen Hakuri.

Shuwagabanni Ku sani Manzon Allah (Saww) yana cewa:

ﻣﻦ ﺍﺳﺘﻌﻤﻠﻨﺎﻩ ﻣﻨﻜﻢ ﻋﻠﻰ ﻋﻤﻞ ﻓﻜﺘﻤَﻨﺎ ﻣﺨﻴﻄًﺎ ﻓﻤﺎ ﻓﻮﻗﻪ, ﻛﺎﻥ ﻏُﻠﻮﻻً ﻳﺄﺗﻲ ﺑﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ.

Ma'ana: Duk wanda muka bashi wani aiki daga cikinku sai ya boye mana koda gwargwadon allura ko abinda ke sama da shi to wannan gululi ne da zai zo dashi a ranar tashin kiyama.

Imamu Abu dawud Ya Ruwaito Hadisin a Hadisi Mai lamba 2943.

MU DAI AIKIN MU GAYA MUKU KO KU DAUKA KO KUYI DARIYA, DARIYARKU TA ZAN KUKA GABA DA NADAMAR MAI QIN GASKIYA.

Da Muka Ce Kar Talakawa Suyi Sak wasu sun Kiramu da Maqiya. Yanzun ma idan mun hango mun fadi wasu na mana izgilanci.

A cikin Alqur'ani Mai Girma Suratu Yunus aya ta 58 Allah Yana Cewa;

ﻗﻞ ﺑﻔﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺑﺮﺣﻤﺘﻪ ﻓﺒﺬﻟﻚ ﻓﻠﻴﻔﺮﺣﻮﺍ ﻫﻮ ﺧﻴﺮ ﻣﻤﺎﻳﺠﻤﻌﻮﻥ.

Ma’ana: Ka ce: Ku yi farin ciki da falalar Allah da rahamarSa shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa.

Hakika mu bama bakin ciki da abinda wasu suka samu ko kuma suka tara. Mu ni'Imar da Allah ya mana ta Musulunchi ta Ishemu.

Alhamdul Lahi Ala Nee'Imatul Islam.

Jamilu Sani Rarah
Tue 19/04/2016.

Friday, 15 April 2016

BAYYANAR MADIGO A KASAR HAUSA LAIFINWA? KUMA INA MAFITA?

BAYYANAR MADIGO A KASAR HAUSA LAIFIN WA? INA MAFITA?
************
Sau da dama Idan na tuna halin da wasu daga cikin 'yan matan arewa suka fada na neman Jinsin Su, hakika na kan kasa samun Natsuwa a zuciya ta.

Daga cikin Kashi 100% na 'yan matan Arewa zaka iya samun Kashi 30 Suna wannan mummunar 'dabi'a ta Madigo (Wa'iyazu Billah).

Babban Abin tashin hankali a Yanzu har matan Aure ake samu suna aikata wannan mummunar 'dabi'a ta neman Jinsinsu.

Babban Abin tashin hankali a yanzu wai har aure suke daurawa tsakaninsu (domin biyan bukatar junansu).

Kwanan baya na samu wani labari wanda ya tadarmin da hankali ainun, wannan labari duk mai imanin da ya saurare shi ko ya ji shi to hankalinsa zai tashi matuka.

Wata matace Wacce Shekarunta Sun haura 45 zuwa sama, ta koyar da 'yar cikin ta wannan lalata ta Madigo bayan koyar da ita wai sai kuma ta sanya ta tana nemo mata kananan yara (sa'an 'yar tata) tana koyar da su wannan muguwar dabi'a (Wa'iyazubillah).

Dalilin da yasa asirinsu ya tonu shine, ita yarinyar ta nemo wata wacce take mutuwarso sai mahaifiyar ta ce ta bar mata ita to fa anan ne asiri ya tonu taje ta sanar da mahaifinsu duka sirrinsu da yanda akayi har ta koya mata wannan mummunar 'dabi'a.

Haka kuma Jaridar Leadership Hausa ta Ruwaito wani labari a shekarar 2015 wani magidanci ne matarsa ta tursasa masa kara auren wata aminiyarta.

Bayan ya auri aminiyar tata da 'yan watanni sai Allah ya tona musu asiri in da mijin ya kamasu suna wannan 'dabi'ar ta madigo.

Haka kuma wani magidanci ya kama 'ya'yansa biyu (Ya da Kanwa) sun auri juna. Suma suna biyawa kansu wannan bukatar.

To wannan da me yayi kama? Idan har Mahaifiya zata koyar da 'yarta wannan lalata? Haka Ya ta koyarda Kanwarta wannan lalatar?

Ina mafita Idan har kishiya da Kishiya zasu auri juna su rinka biyawa kansu bukata su manta da Mijinsu?

Babu shakka wannan Ba karamar Masifa bace ta kunno muna ai a Arewacin Nigeria, wanda idan bamu tashi tsaye ba to kuwa akwai babbar matsala wacce zata yi sanadiyar wargajewar wannan nahiya tamu.

Daga cikin Masu wannan laifi akwai iyaye maza domin Kabar 'yarka 'yar shekara 24 ko 25, 26, wani har 30 bata yi aure ba kuma ba tare da tana tattare da wata lalura ba babu shakka wannan na sanadiyar faruwar wanan abu.

Hakika akwai lalura domin akwai matan da Aljannune ke hana su aure wasu kuma kawai ganin duk abinda take nema tana samu yakan sanya takiyin auren.

Babu shakka wayannan Wayoyi da muke amfani dasu sune manyan musabbabin Wannan lalacewar da wasummu sukayi.

Hakika ya zama dole ga dukkaninMu mu rika kula da matanmu da Qannenmu shin da wa suke Hulda? Kuma wace Hulda suke yi a tsakaninsu? Kuma ya halayen Qawayensu da suke?

Babu shakka wannan ba karamar taimakwa zaiyi ba wajen magance wannan matsalar. Mu tuna a cikin Alqur'ani Allah yana Ce Mana; YA! KU WAYANDA KUKAYI IMAMI KU TSARE KANKU DA IYALANKU DAGA WUTA.

Hakika Duk masuyin wannan mummunar 'dabi'a suji tsoron Allah su tuba kuma su san cewa, Wallahi Duk mai yin Wannan 'dabi'ah kuma ta mutu tana aikatata wallahi Allah zai azabartarda ita sosai da sosai kuma zata hadu da mummunar makoma a cikin Qabarinta.

Jamilu Sani RARAH.
Fri 15/04/2016