BAYYANAR MADIGO A KASAR HAUSA LAIFIN WA? INA MAFITA?
************
Sau da dama Idan na tuna halin da wasu daga cikin 'yan matan arewa suka fada na neman Jinsin Su, hakika na kan kasa samun Natsuwa a zuciya ta.
Daga cikin Kashi 100% na 'yan matan Arewa zaka iya samun Kashi 30 Suna wannan mummunar 'dabi'a ta Madigo (Wa'iyazu Billah).
Babban Abin tashin hankali a Yanzu har matan Aure ake samu suna aikata wannan mummunar 'dabi'a ta neman Jinsinsu.
Babban Abin tashin hankali a yanzu wai har aure suke daurawa tsakaninsu (domin biyan bukatar junansu).
Kwanan baya na samu wani labari wanda ya tadarmin da hankali ainun, wannan labari duk mai imanin da ya saurare shi ko ya ji shi to hankalinsa zai tashi matuka.
Wata matace Wacce Shekarunta Sun haura 45 zuwa sama, ta koyar da 'yar cikin ta wannan lalata ta Madigo bayan koyar da ita wai sai kuma ta sanya ta tana nemo mata kananan yara (sa'an 'yar tata) tana koyar da su wannan muguwar dabi'a (Wa'iyazubillah).
Dalilin da yasa asirinsu ya tonu shine, ita yarinyar ta nemo wata wacce take mutuwarso sai mahaifiyar ta ce ta bar mata ita to fa anan ne asiri ya tonu taje ta sanar da mahaifinsu duka sirrinsu da yanda akayi har ta koya mata wannan mummunar 'dabi'a.
Haka kuma Jaridar Leadership Hausa ta Ruwaito wani labari a shekarar 2015 wani magidanci ne matarsa ta tursasa masa kara auren wata aminiyarta.
Bayan ya auri aminiyar tata da 'yan watanni sai Allah ya tona musu asiri in da mijin ya kamasu suna wannan 'dabi'ar ta madigo.
Haka kuma wani magidanci ya kama 'ya'yansa biyu (Ya da Kanwa) sun auri juna. Suma suna biyawa kansu wannan bukatar.
To wannan da me yayi kama? Idan har Mahaifiya zata koyar da 'yarta wannan lalata? Haka Ya ta koyarda Kanwarta wannan lalatar?
Ina mafita Idan har kishiya da Kishiya zasu auri juna su rinka biyawa kansu bukata su manta da Mijinsu?
Babu shakka wannan Ba karamar Masifa bace ta kunno muna ai a Arewacin Nigeria, wanda idan bamu tashi tsaye ba to kuwa akwai babbar matsala wacce zata yi sanadiyar wargajewar wannan nahiya tamu.
Daga cikin Masu wannan laifi akwai iyaye maza domin Kabar 'yarka 'yar shekara 24 ko 25, 26, wani har 30 bata yi aure ba kuma ba tare da tana tattare da wata lalura ba babu shakka wannan na sanadiyar faruwar wanan abu.
Hakika akwai lalura domin akwai matan da Aljannune ke hana su aure wasu kuma kawai ganin duk abinda take nema tana samu yakan sanya takiyin auren.
Babu shakka wayannan Wayoyi da muke amfani dasu sune manyan musabbabin Wannan lalacewar da wasummu sukayi.
Hakika ya zama dole ga dukkaninMu mu rika kula da matanmu da Qannenmu shin da wa suke Hulda? Kuma wace Hulda suke yi a tsakaninsu? Kuma ya halayen Qawayensu da suke?
Babu shakka wannan ba karamar taimakwa zaiyi ba wajen magance wannan matsalar. Mu tuna a cikin Alqur'ani Allah yana Ce Mana; YA! KU WAYANDA KUKAYI IMAMI KU TSARE KANKU DA IYALANKU DAGA WUTA.
Hakika Duk masuyin wannan mummunar 'dabi'a suji tsoron Allah su tuba kuma su san cewa, Wallahi Duk mai yin Wannan 'dabi'ah kuma ta mutu tana aikatata wallahi Allah zai azabartarda ita sosai da sosai kuma zata hadu da mummunar makoma a cikin Qabarinta.
Jamilu Sani RARAH.
Fri 15/04/2016
No comments:
Post a Comment