Saturday, 12 March 2016

LADUBBAN CIN ABINCI A MUSULUNCI

 LADUBBAN CIN ABINCI YA KAMATA KOWA YA SANSU
**********
Addinin musulunci addini ne mai girma da tsari, addini ne da bai bar wani abu aboye ba face yayi bayani akansa domin musulmai ya ribantu da abin, lura da wannan, addinin Musulunci ya zo da ladduba masu yawa da kuma tarin amfani dangane da shiga makewayi da kuma fita daga makewayin. Haka ya sake bayani kan ladduban cin abinci, da sauran abubuwa da suka kama daga saduwa, sanya sutura, kwanciya da sauransu. Ga dai kadan daga cikin ladduban cin abinci, kamar haka:

1.  Fadin BISMILLAH a lokacin fara cin abinci: Babu ko shakkah fadin bisimillah shine ladabi na farko wajen cin abinci saboda an karbo hadisi daga Umar bin Abiy-salamah (RA) yace: Na kasance yaro qarqashin kulawar Manzon Allah (saww) kuma hanuna ya kasance yana yawo a cikin akwashin abinci, sai yace dani: Ya kai yaro! Ka ambaci sunan Allah (ma’ana kayi Bisimillah) , ka ci da hanunka na dama, ka kuma ci daga abinda ke gabanka.
Jabir yace:- Daga wannan lokacin ban gushe ba; wannan ne irin cin abincina.
(Imamu Bukhariy ya rawaito shi a hadisi mai lamba: 5376, da Imamu Muslim hadisi mai lamba: 2022).

2.   Cin abinci da hannun dama: Hakika cin abinci da hannun dama shine ladabi na biyu daga ladubban cin abinci, Wannan kuma sunna ne saboda hadisin da ya gabata.

3.   Mutum ya ci gabansa: Shima wannan sunna ne saboda hadisin da ya gabata. Sai dai idan mutum ya san cewa mutumin da suke cin abinci tare da shi ba zai cutu ko kyamaci yawo da hannu a cikin kwaryar abinci ba, to a nan babu laifi kan ya ci daga ko-ina na kwano; saboda hadisin Sayyidina Anas bin Malik (RA)  a qissar  wani tela da ya gayyaci Manzon Allah (Saww) zuwa cin abinci Anas yace: Sai na ganshi –yana nufin: Annabi (saww) yana bibiyan kabewa daga geffen kwano. Ko kuma idan mutum ya kasance yana cin abincin ne shi kadai; babu wani a tare da shi, ko kuma abincin akwai launukan abun ci da dama; a irin wannan halin ya halatta ya ci abincin da ke gaban waninsa; matuqar dai bai cutar da wani da hakan ba.

4.     Fadin "Alhamdu Lillah" a qarshen abinci: Yana daga cikin ladubban cin abinci Saboda hadisin Abu-umamah (RA) yace: Manzon Allah (Saww) ya kasance idan aka dauke akwashin abinci bayan kammala cinsa- daga gaba-gare shi sai yace:

Ma'ana: Yabo mai yawa daddada mai albarka sun tabbata ga Allah, Allah Ubangijinmu ba a barin yi masa da'a, ko kuma ace an wadata ga barinsa. (Imam Bukhariy ya rawaito shi a hadisi mai lamba: 5459).

Da kuma wani hadisi da Annabi (saww) ke cewa, Lallai Allah yana rubuta yardarsa ga bawa, idan ya ci abinci ya gode masa akanta, ko ya sha abun sha ya gode masa akansa. (Imamu Muslim ya rawaito shi a hadisi mai lamba: 2734).

5.    Makruhi ne cin abinci a kishingide: Cin abinci a kishingide makaruhine (ma’ana ba lad aba zunubi) Wannan kuma saboda hadisin uwar muminnai A'ishah (RA) tace, Nace: Ya ma'aikin Allah! Ka ci abinci Allah ya sanya ni na zamo fansarka a halin kishingida; saboda zai fiye maka sauqi, Sai manzon Allah (saww) ya karkata kansa har sai da goshinsa ya yi kusan taba qasa, sai yace: A'a! zan ci abinci ne kamar yadda bawa ke cin abinci, zan kuma zauna kamar yadda bawa ke zaunawa. (Albagawiy a cikin littafin "Sharhus sunnah" ya rawaito shi (11/286-287), da Ahmad a "Zuhdu" (5-6) kuma Shu'aibul Arna'ud ya inganta shi da "wani hadisi mursal da ya ke masa shaida", a cikin (Hashiyar sharhus sunnah)
Da kuma saboda hadisin Abu-juhaifah (RA) yace: Manzon Allah (Saww) yace: Lallai ni bana cin abinci a kishingide. (Imamu Bukhariy ya rawaito shi a hadisi mai lamba 5398).

6.    Mustahabbi ne hanuwa daga aibata abincin da mutum baya son cinsa: Hakika aibata abinci mustahabbine saboda hadisin Abu-hurairah (RA) yace: Manzon Allah (saww) bai taba aibanta abinci ba; idan ya yi sha'awarsa sai ya ci, in kuma bai yi ba, sai ya bari. (Imamu Bukhariy ya rawaito shi a hadisi mai lamba: 5409, da Imamu Muslim a hadisi mai lamba: 2064).

7.    Cin abinci daga geffan masaki, da kuma kasancewar cinsa daga tsakiyar kwarya makruhi ne: saboda hadisin Ibnu-abbas (RA), daga Annabi (Saww) lallai shi an zo masa da masaki da aka sanya kwababben alkubuz da nama mai suna (Sarid), Sai yace: Ku ci daga geffan masakin, kada ku ci daga tsakiyansa, saboda albarka tana sauka ne a tsakiyarsa.

8.     Cin abinci da yatsu guda uku, da kuma sude su bayan kammalawa, shima yana daga cikin ladubban cin abinci saboda hadisin Ka'ab dan Malik (RA) yace: Annabi (Saww) ya kasance yana cin abinci da 'yan yatsunsa guda uku, baya kuma wanke hannunsa har sai ya sude su.  (Imamu Ahmad ya rawaito shi (1/270), da At-tirmiziy (lamba: 1805), ya kuma ce: hadisi ne hasan ingantacce. Da Abu-dawud (lamba: 3772), da Ibnu-majah, (lamba: 3277), Albaniy ya inganta shi (Sahihu sunan Ibni-majah, lamba: 2650)).

9.  Cinye abin da ya zuba ana tsakiyar cin abinci, ko wanda ya warwatsu: Shima yana daga cikin ladubban cin abinci saboda fadinnsa (Saww): Idan lomar dayanku ta fadi to sai ya kade mata kura, sannan ya cinye ta, kada ya barta ga shedan.

10. Sude kwaryar da aka ci abinci a cikinta da lashe yatsu: Shima wannan na daga cikin manyan ladubban cikin abinci saboda fadin Sayyidina Anas (RA) a cikin hadisin da ya gabata, da yake cewa Kuma ya umurce mu yana nufin Annabi (saww) da mu katse kwaryar abinci. Ma'ana: mu sude ta, mu kuma bibiyi abinda ya rage a cikinta na abinci. A wata riwayar kuma aka ce: Annabi (saww) ya umurce mu da mu sude 'yan yatsu da kuma akwashi, yace: Saboda lallai ku ba ku san a ina ne daga cikin abincinku albarkar ta ke ba!.

Jamilu Sani RARAH

Sat 11/03/2016.

No comments:

Post a Comment