Nasiru Zarummai Ya yi ban kwana da Gidan karya izuwa Gidan Gaskiya. Yanzu ya rage daga shi sai ayukkansa da ya gabatar a Gidan duniya.Sai da me kuma? Hakkinsa da ya rage a gareku abokansa da yaransa da matansa shine, Ku boye sharrinsa, ku yawaita fadin Alkherinsa a zamansa da ku.
Ku yawaita yi masa addu'ah a duk lokacin da kuka tuna shi (akan Allah ya gafarta masa kura kuransa ya kuma yi masa rahama). Abokanansa ku yawaita Ziyarar 'ya'yansa da ya bari da matasa domin jin abubuwanda suke ciki, idan na neman taimako ne ku taimakesu idan na shawara ne ku basu shawara.
Hakika muna kyautata zato na alkheri tare da samun Rahama ga Nasiru Zarummai domin Imamu Ahmad ya ruwaito cewa, Manzon Allah (saww) ya ce, “Babu wani mutum musulmi da zai mutu ranar juma'a ko yini Juma'a face Allah ya kare shi daga fitinar qabari. (Imamu Ahmad 6582-6646).
Marigayi Nasiru ya rasu a ranar Jumu'ah kafin rasuwar Marigayin Shine kwamisinan kimiya da Fasaha a wannan gwamnati mai ci yanzu ta Aminu Waziri Tambuwal. Manazarta suka ce, Tunda ake Mutuwa mutum biyu ne ke mutuwa, daga wanda ya mutu ya huta sai wanda ya mutu aka huta.
Ina rokon Allah jallah wa'Azzah da ya sanya Nasiru Zarummai da sauran mamatan Musulmi cikin wayanda Suka huta.
Jamilu Sani RARAH
Sat 05/03/2016.
No comments:
Post a Comment