*************
Ku Gayawa Buhari kada ya gwada kama duk wani wanda yayi sata a cikin Gwamnatinsa a halin yanzu idan har ya kasance mai gaskiya ne.
Domin A lokacin khalifancin Sayyidina Umar (RA) ya taba tura Amru bin Aass kasar Misra (Egypt) don ya zama gwamna a cen.Lokacin tafiyar Amru bin Aass yayi Sai Sayyidina Umar (RA) ya tambaye shi, Idan aka zo maka da barawo da laifin sata wane irin hukunci zaka yi masa?
Sai Amru bin Aass (RA) yace: zan yanke masa hannunsa kamar yanda shari'a ta tanada wa masu irin wannan laifin. Sai Sayyidina Umar (RA) ya ce, masa haka ne amma kai ma idan aka sami wani daga masar ya zo min da kukan yunwa kaima zan yanke hannunka.Hakika Shugaba Buhari 'yan Nigeria Musamman talakawa na cikin garari da matsi da yunwa, yana da kyau a duba lamarin talakawa idan akwai abinda za'ayi.
Nayi imani akan cewa, tun ranar da ka shiga Villah bada aljihunka kake sayen Abincin da 'ya'yanka da matanka ke ci ba, haka kuma bada albashin ka suke ci suke sha ba. Duk da kuddin jama'ah suke yi.
Shugaba Buhari ka sani Yahudawa suna ganin cewa, Muddin aka Sanya jama'ah a cikin talauci to kuwa ko mai zasu iya aikatawa.
Wasu da dama suna cikin gararin yunwa da rashin abinci. Hakika bama cewa kai ka kawo talauci amma muna tunatar da kai akan cewa duk wanda ya mutu da yunwa kamar kisan kai ne kuma Sai Allah ya tambayi shuwagabanni a Gobe Qiyama.
A gwamnatin da ta gabata anyi fama da tashe-tashen Bom Babu shakkah dukkan wanda ya mutu a sanadiyar tashin Bom sai Allah (swt) ya isar masa tare da biye masa hakkinsa akan duk wani mai hannu a ciki. Haka kuma duk wanda ya mutu ta dalilin Yunwa ko matsi ko wahala sai Allah ya tambaye ku shuwagabannin mu.
Gyara kayanka.....
Jamilu Sani RARAH
Tue 23/02/2016.
No comments:
Post a Comment