Saturday, 12 March 2016
LADUBBAN CIN ABINCI A MUSULUNCI
LADUBBAN CIN ABINCI
Monday, 7 March 2016
NASIRU ZARUMMAI YAYI BAN KWANA
Ina rokon Allah jallah wa'Azzah da ya sanya Nasiru Zarummai da sauran mamatan Musulmi cikin wayanda Suka huta.
Jamilu Sani RARAH
Sat 05/03/2016.
Wednesday, 2 March 2016
MASOYAN BUHARI NA GASKIYA KU GAYA MASA
*************
Ku Gayawa Buhari kada ya gwada kama duk wani wanda yayi sata a cikin Gwamnatinsa a halin yanzu idan har ya kasance mai gaskiya ne.
Domin A lokacin khalifancin Sayyidina Umar (RA) ya taba tura Amru bin Aass kasar Misra (Egypt) don ya zama gwamna a cen.Lokacin tafiyar Amru bin Aass yayi Sai Sayyidina Umar (RA) ya tambaye shi, Idan aka zo maka da barawo da laifin sata wane irin hukunci zaka yi masa?
Sai Amru bin Aass (RA) yace: zan yanke masa hannunsa kamar yanda shari'a ta tanada wa masu irin wannan laifin. Sai Sayyidina Umar (RA) ya ce, masa haka ne amma kai ma idan aka sami wani daga masar ya zo min da kukan yunwa kaima zan yanke hannunka.Hakika Shugaba Buhari 'yan Nigeria Musamman talakawa na cikin garari da matsi da yunwa, yana da kyau a duba lamarin talakawa idan akwai abinda za'ayi.
Nayi imani akan cewa, tun ranar da ka shiga Villah bada aljihunka kake sayen Abincin da 'ya'yanka da matanka ke ci ba, haka kuma bada albashin ka suke ci suke sha ba. Duk da kuddin jama'ah suke yi.
Shugaba Buhari ka sani Yahudawa suna ganin cewa, Muddin aka Sanya jama'ah a cikin talauci to kuwa ko mai zasu iya aikatawa.
Wasu da dama suna cikin gararin yunwa da rashin abinci. Hakika bama cewa kai ka kawo talauci amma muna tunatar da kai akan cewa duk wanda ya mutu da yunwa kamar kisan kai ne kuma Sai Allah ya tambayi shuwagabanni a Gobe Qiyama.
A gwamnatin da ta gabata anyi fama da tashe-tashen Bom Babu shakkah dukkan wanda ya mutu a sanadiyar tashin Bom sai Allah (swt) ya isar masa tare da biye masa hakkinsa akan duk wani mai hannu a ciki. Haka kuma duk wanda ya mutu ta dalilin Yunwa ko matsi ko wahala sai Allah ya tambaye ku shuwagabannin mu.
Gyara kayanka.....
Jamilu Sani RARAH
Tue 23/02/2016.
TARIHIN KASAR ANDALUS (SPAIN)
GABATARWA
Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabi (saww), da Iyalansa da Sahabbansa da duk wayanda suka bi hanyarsu har ya zuwa ranar sakamako.
Bayan haka Ganin irin yanda al'ummar mu suka yi watsi ko wurgi da tarihin kasa mai matukar muhimmanci ga musulmi naga dacewar in bayar da wannan tarihi na Kasar Andalus ko Ince Spain a yanzu.
Andalus kasa ce mai tarihin gaske wanda ban isa in iya bada tarihnta duka ba sai dai in dan tsakuro wani abu in gabatar muku da shi, Kasar Andalus tayi zama kashi 95 cikin 100 na cikinta musulmi ne kashi 5 ne ba musulmi ba. Daga baya ne Yahudawa suka shiga kasar suka hada rikici tsakanin musulman kasar suka mamaye kasar suka kashe manyan malaman kasar suka cenja sunan garin da sunan garuruwan zuwa wasu suna na daban daga karshe ma sai da takai kafiran garin sune da kaso 95 musulmai kuma sune da kashi 5 daga cikin 100.
Kasar Andulus wadda a yau ake kira spain kasa ce wadda ta tara manyan-manyan malaman musulunci. kasa ce wadda ta tara gine-ginen musulunci na tarihi.
Akwai wani masallaci da ke garin Qurdaba a cikin kasar ta Andalus. a lokacin idan an debe masallacin ka'aba da masallacin Annabi dake madina duk duniya ba masallacin dake bada abin mamaki irin masallacin na qurdaba dake kasar ta Andalus.
Garin na Qurdab na daga cikin garuruwan da yahudawa suka cenjawa suna yanzu haka ana kiran garin da suna cordoba.
Massallachin Qurdab
Masallacin garin na Qurdab tarihi ya nuna manyan-manyan malamai ne suke karantar da hadisi ba dare ba rana a cikinsa Malaman tarihi sunce babu Ranar da ba'a karanta hadisin Annabi (saww) kasa da dubu 10 a cikin masallacin. Baya ga haka masallacin na game da labrary wacce akwai littafai daban-daban acikinsa (babu kalar littafen da zaka nema a ciki baka same shi ba).
Manya-manyan daliban Imamu malik sune suke rike da masallacin. irinsu Yahaya bin Yahaya an andulusiy (Mutumen andalus) wanda shine mutumen da ya ruwaito muwadda na Imamu Malik daga Imamu Malik bin Anas.Baya ga shi akwai malamai da yawa da sunka fito daga sassa daban-daban na kasar.
Kasar ta Andalus tafara kasancewa Cibiyar musulunci hijirar Annabi (Saww) nada shekara 163. shekaru 16 gabanin rasuwar Imamu Malik bin Anas. kuma shekaru 69 da rasuwar Anas bin Malik daya daga cikin manyan sahabban Annabi (Saww).
Akwai malamai da yawa a kasar ta Andalus irinsu Ibn Hazbin Al-andalusiy da Imamu Qurdabi wanda yayi tafsirin aljam'un li ahakamun qur'an, wanda ankafi sani da tafsirin qurdabi. Akwai irinsu Ibn Rushidin al-Andulusi. akwai Ibn Al-Arabi wanda yayi tafsirin Ahakamu Qur'an.
Wayannan kadan kenan daga malaman da sunka fito daga kasar ta Andalus. Kasar taci gaba da zama Cibiyar musulunci har sai da ankayi shekaru sama da 800 musulunci.
Ranar da Yahudawa sunka saka Andalus a gaba kasan cewa duka ka'idodin musulunci ake bi a kasar da kewaye har kafirai basa sha'awan shiga kasa, amma randa suka kularwa kasar ba'a dauki shekaru 50 ba saida suka juyar da musuluncin.sunka rushe duk wani abu na musulunci akasar. In shaa Allahu tarihi ya kan kama. Zan ci gaba.
Jamilu Sani RARAH
Tue 01/03/2016.
Saturday, 20 February 2016
SAKO ZUWA GA MATASA
SAKO ZUWA GA MATASAN AREWA.
*********
Dukkan Godiya ta tabbatta ga Allah Ubangijin halittu. Salati da sallama su kara tabbata ga shugaban Manzanni, Muhammadu 'dan Abdullahi tare da iyalanSa da sahabbanSa da duk wayanda suka bi tafarkinsu har ya zuwa ranar Sakamako.
Wannan Sako Nawa ya shafi dukkanin Matasa 'yan Arewa musamman ma masu kishi tare da kaunar Arewa a zukatansu.
Hakika abinda ke faruwa a Facebook, Instagram, Twitter yana daga cikin dubban abubuwan da ke kawo matsala tare da tawayar arzikin da muke fama da su a halin yanzu.
Hakika ina lura tare da kula da cewa, babu wata rana ko wani dare da zan hau social media ba tare da na tarar wani ya aibata Shugaba Buhari ko wani daga cikin 'yan adawa ba.
Hakika zagin juna da cin mutuncin juna na daga cikin abubuwan da ke kawo matsala a wannan rayuwa da muke ciki.
Wani daga ya hau Facebook ba zaka ji ya fadi wata kalma ta alkheri abakinsa ba kawai zaka ji yana kokarin ci mutuncin da zagin 'yan adawarsa ne tare da kirkiro wasu maganganu marar tushe ya saka a bayanan nasa.
Ta 'bangaren Masoya Shugaban kasa Buhari zaka ji suna fadin, Rusashsiyar jam'iyar PDP, ko kuma Jam'iya mai kashin Mutane, ko kai tsaye kaji mutum yace, Jam'iyar kafirai.
To meye amfanin wannan? Ta bangaren 'yan jam'iyar ta PDP kuma zakaji suna Cewa, Tsohon nan ya kawo talauci, Tshohon nan yawonsa yayi yawa, Tsohon nan bazai iya gyara ba. Da dai wasu zan tuka marar amfani.
Shin ko mun Manta Abinda Allah (swt) ke fadi a citkin Alqur'ani mai Girma? Cewa, "SHIN BAKA GANI BA, YADDA ALLAH YA BUGA WANI MISALI; KALMA MAI KYAU, KAMAR BISHIYA CE MAI KYAU; TUSHENTA YANA TABBATACCE, RESSANTA KUMA SUNA CIKIN SAMA* TANA BAYAR DA ABINCINTA, A KOWANI LOKACI DA IZNIN UBANGIJINTA" (Suratul Ibrahim aya ta 24 zuwa 25).
A wani hadisi kuma Manzon Allah (saww) Cewa yayi, Sadaka ta zama wajibi a kan kowani Musulmi, Sai aka ce: To idan bai samu abin sadakar ba fa? Sai ya ce: Yayi aiki da hannayensa; sai ya amfanar da kansa, ya kuma yi sadaka. Sai aka sake tambayarsa: To idan bai samu iko ba fa? Sai ya ce: Ya taimaki ma'abucin buqata; wanda aka zalunta. Sai aka ce masa: To idan bai samu iko ba fa? Sai yace: Ya yi umurni da kyakkyawa, ko da alkhairi. Sai aka tambaye shi: To idan bai aikata ba fa? Sai ya ce: Sai ya kame daga aikata sharri; don yin hakan sadaka ne ".
Shin me yasa muke aibata 'yan uwanmu maimakon muyi shiru ko dan yin hakan ya zama sadaka a garemu?
Kusani ya Matasa Manzon Allah (saww) ya zo ne don ya zama aminci da rahama; kuma don ya tsamar da Mutane daga duhu zuwa ga haske. kamar cika alqawari, hana zalunci tare da qetare iyaka, da tsayar da adalci, da tunkude zalunci.
Ya kai me kiran PDP da Rusasshiyar Jam'iya, Ya kai mai Kiran Shugaba Buhari ya kashe Nigeria muyiwa Allah mu daina ko abubuwa zasu mana sauki.
Allah (Swt) Yana Cewa, "AKWAI TSAMMANIN UBANGIJINKU YA HALAKA MAQIYANKU, SAI YA BAKU MAYEWA A DORON QASA, DON YA GA YAYA ZAKU AIKATAWA (Suratul A'araf aya ta 129).
Hakika dukkan 'yan adawarku su mutu a barku a cikin duniya ba zata karaku da komai ba hasalima babu wani abu da zaku karu da shi sai hasara da tabewa (Allah ya tsare mu).
Ya 'dan uwa matashi kada arude ka da siyasa kaje ka manta dalilin da yasa aka halicce ka a duniya.
Da wannan Nake Rokon Matasa akan mu daina aibata junan mu saboda wani banbanci na siyasa
Haka kuma ina kira ga Shuwagabannin da suyi qoqarin tabbatar da zaman lafiya; ta hanyar tsayar da adalci, tabbatar da gaskiya. Kuma shugabani yakama ta su san wajibi ne akansu su yi qoqari wajen aikata duk abinda zai amfani talakawa, da tunkude musu abinda zai cutar da su a cikin addininsu da duniyarsu.
Yana da kyau Malamai su san cewa, sune halifofin Manzanni, kuma magada Annabawa. Don haka wajibi ne akan ma'abuta ilimi su kare al'umma daga cutar jahilci, ko rugujewar aqidu da
lalacewansu. Sannan su riqa
haskaka hanyoyi ga Mutane ta
hanyar fada musu duk wasu abubuwan da suka shige musu
duhu.
Wajibine su tashi tsaye wajen ilmantar da Mutane lamuran addininsu da Siyasa; Saboda shi malami yana gyara abinda Mutane suka bata ne, yana! kuma fadakar da su zuwa ga alkhairi, tare da yin umurni da kyawawa, da kuma hani kan munana.
Ina Rokon Allah ya amfanar da mu Tare da Amintar damu aduk inda muke.
Allah (Swt) a cikin Alqur'ani Mai Girma yana Cewa, "Ya ku Mutane lallai ne alkawarin Allah gaskiya ne; kada rayuwar duniya ta rude ku, kuma kada mai rudi (wato Shedan) ya rude ku daga
Allah" (Suratul Luqman ayata 33).
Jamilu Sani RARAH
Sat 20/02/2016.
Friday, 19 February 2016
MAHAIFIYA MAI ABIN MAMAKI
MAHAIFIYA MAI ABIN MAMAKI
**********
Na tsaneta. tsana ta hakika har bana son naganta, aikinta shine dafa abinci ga malamai da dalibbai .domin ta tallafawa karatuna.
Akwai wata rana da ta je har ajin mu (Class) saboda ta ganni ta tabbatar da lafiya ta, "YA ZA'AYI TA MIN HAKA TAZO WAJENA BAYAN TA SAN YANDA NA TSANETA?" haka na fa'da a zuciya ta.
Lokacin da tazo ajin namu ta min magana amma nayi kamar banganta ba. Ta dage da yi min magana anan ne na juyo a fusace, na gaggaya mata ba'kaken maganganu masu zafi, Na fita ajin da gudu raina a 'bace.
Washe gari na shigo makaranta kenan sai na hadu da wani 'dan Class din mu nan take ya bu'da baki yana cemin, "Eeey Mahaifiyarsa ido 'daya ne da ita"
Anan naji kamar in yiwa kaina kabari saboda bakin cikin wannan magana da yayi min, nan take na juya na koma gida wajen Mahaifiyata nace da ita, "IDAN DAI DON KI SAKA ANA YIMIN DARIYA NE ME ZAI HANA MA KI MUTU IN HUTA DA KE"
Mahaifiyata dai bata ce min uffan ba, har na gama gaggaya mata magana na wuce abina.
Allah ya yini mai basira sosai da sosai kuma na dage da karatu babu kama hannun yaro.
Ana haka kawai sai Allah ya kawo wata kungiya a makarantar mu masu bawa yara masu basira scholar ship zuwa kasar waje domin yin karatu.
Aka yi jarabawa Allah ya bani sa'a naci jarabawar, anan ne aka 'dauke ni aka kaini kasar Singapore domin yin karatun nawa.
Da yake ni mutum ne mai basira da hikima Allah ya taimake ni har na samu kammala karatuna ban dawo ba, cikin taimakon Allah na samu aiki a cen Singapore din.
Topa daga nan ne na samu sa'a domin bada dadewa ba na mallaki gida nawa na kaina a kasar ta Singapore daga bisani na nemi mata a cen aka daura mana aure da ita.
Na 'dau shekaru da aure har Allah ya albarkace ni da 'ya'ya ina jin dadin rayuwa cikin iyalin nawa, kwatsam wata rana mahaifiyata tazo ziyarata a Singapore.
Ina zaune a falo 'dana na fari (my fist born) yana wasa, mata ta tana kitchin tare da 'dana na biyu, kawai sai naji mutum a kofar gida ma'ana yana so a bashi umurni ya shigo.
Nan take 'dana na fari ya ruga da gudu yaje ya bude kofar ai kuwa yana budewa sai ya fara kuka, nan da nan na iso kofar bada shiri ba (domin) in gani meke faruwa yake kuka.
Me zan gani kawai sai naga mahaifiyata a tsaye (ashe abinda ya saka 'dan nawa kuka ganinta da yayi da ido dayane).
Anan na fara yi mata kururuwa tare da ce mata, "YA ZA'AYI KIZO GIDANA KI TSORATA MIN 'DANA? MAZA KI 'BACE MIN DA GANI".
Mahaifiyar tawa cikin sanyin hali tace dani, "YI HAKURI A SHE NAYI KUSKUREN GIDA NE. ( MA'ANA, BA NAN NE NAKE NEMA BA)". ta fita ta yi waje. Ban san ya akayi tazo Singapore ba, ban kuma tambaye ta ya akayi ba bare har in bata ruwa da abinci.
Wata rana an shirya taro a makarantar da na fara karatu, sai aka gayyaceni.
Na tashi na shirya tsaf na yanki tacket din jirgi na sauka kasar mu, bayan sauka ta a kasar sai na yanke shawarar bari in tafi tsohuwar unguwar tamu.
Bayan naje unguwar sai na samu gidan namu a rufe, ba tare da bata lokaci ba na tambayi makwaftanmu labarin mahaifiyar tawa.
Sai suka gaya min cewa ai ta mutu tun kusan wata 2 da suka wuce. Banji wani ciwo ba lokacin da suka gayamin bare inyi hawaye.
Na juya haka sai suka ce min, ga wata takarda da tasa a rubuta mata a lokacin da take cikin rashin lafiya.
Na karbi takardar na fara warware wa a hankali, nan take na fara karanta rubutun da ke cikin takardar.
YA 'DANA!
A KO DA YAUSHE TUNANINKA NAKE, INA MAI BAKA HAKURI DA NAJE GIDAN KA A Singapore KUMA NA BAWA 'YA'YANKA TSORO, NAJI DADI KWARAI DA GASKE LOKACIN DA SHUGABAN MAKARANTARKU YA GAYA MIN ZAKA ZO TARO, SAI DAI KUMA KASH! BANDA LAFIYAR DA ZAN IYA ZUWA DOMIN IN GANKA.
INA BAKA HAKURI AKAN DARIYAR DA ABOKANANKA SUKE MA SABODA NI. HAKIKA ZAN GAYA MAKA WANI SIRRI WANDA BAKA SANI BA.
A LOKACIN DA KANA YARO KARAMI BAKA MALLAKI HANKALINKA BA KA SAMU HATSARI WANDA YA KAI HAR KA RASA IDO DAYA.
KASAN CEWA LIKITAN YACE ANA IYA SAKA MA WATA TAYI LAFIYA QALAU, NI KUMA A MATSAYINA NA MAHAIFIYA SHINE NA BAKA TAWA NI NA ZAUNA DA IDON 'DAYA.
INA FATAN ZAKA KULA DA JIKOKINA, ALLAH YA YIMA ALBARKA.
NOTE:-
﹏﹏﹏
Wannan Labarin ya faru da gaske a Kasar Nepal, Ina fatan Zamu kula da irin Soyayyar da iyayen mu suke mana.
Jamilu Sani RARAH
TUE 16/02/2016.



