Tuesday, 13 August 2019

UNGUZOMA (MIDWIVES)

UNGOZOMA (MIDWIFE) BAIWAR ALLAH

Wasu suna ganin kalmar Ungozoma ta samo asali ne daga "ungo-tsoma ".Wai don Idan mace ta yanke cibin jariri, kuma mabiyya (mahaifa) ta fado, to sai a dauko ta fito da ita waje ta mika wa masu taimaka mata, ta ce da su "Ungo-tsoma " A cikin masaki mai cike da ruwa. Wai ta haka ne sabida yawan fadar kalmar "Ungo-tsoma ". Sai ta koma Ungotsoma. "Ungozoma ".

A Al'adar Hausawa Ungozoma ta na da muhimmanci kwarai da gaske, domin kuwa kusan kowanne Kauye ko Gari ko Unguwa Inda jama'a su ke zaune akwai Ungozoma, kamar dai yadda ake samun Ruwa don bukatar rayuwa.

Saboda sanin muhimmancin Ungozoma a al'umar Hausawa har kirari su ke mata da cewa " Ungozoma kin fi mai da son da ". Haka har cikin Karin magana an ambaci Ungozoma, misali : "Komai saurin Ungozoma ta jira a haihu ".da kuma "Ai ba a Kare haihuwa ba wai an baiwa Ungozoma tuwan suna a hannu". Dasauransu. wannan shi zai Kara tabbatarma da muhimmamchin Wannan Mata a Cikin al'umma.

Akwai ire-iren Ungozoma guda biyar. (5times) a kasar Hausa kamar haka :

1-Ungozomar Gado, Wasu Gidajen Attajirai Sukan Ajiye Ungozoma wacce duk matarda zata haihu Gidan itace zata Kula da wannan matar tun daga rainon Cikin har Zuwa Haihuwa Itace zata Rika Kula da matar.

2-Ungozomar Sana'a, Akan Samu Wasu Masu Aikin Karbar Nakuda (Ungozoma), wacce Ita Zaman Kuddi take, 'yan Unguwa sun San da zamanta, Duk Gidan da za'a haihu akan Kira Irin wannan matar a sanyata ta karbi bikin Idan an haihu sai a biyata ladan aikinta.

3-Ungozomar Dangi, Kamar Gidan Attajirai Haka A Dangi Idan an samu Macce wacce ta iya Karbar haihuwar to Tana iya Zama ta Dangi, duk wani wata 'yar uwa ko matar Dan uwa da zata haihu akan je anemo ta ta karbi haihuwar.

4-Ungozomar Masarauta, Duk Gidan sarauta akan samu Mai Karbar biki na matar Sarki ko Kuma 'ya'yan Sarki ko Kuma Matan 'ya'yan Sarki Dasauransu.

Ayyukan Ungozoma suna da yawa ga kadan daga ciki:

Akwai aikace -aikace da dama da Ungozoma ke gudanarwa kafin haihuwa, da kuma lokacin haihuwa, da bayan an haihuwa.

Sanin Lafiyar Abin da ke Ciki Tun kafin lokacin haihuwa Ungozoma takan je ta duba lafiyar jariri ,misali kwanciyarsa a ciki, motsinsa Dasauransu. Ta hanyar sunkuyawa ta kara kunnwanta kan cibiyar mai ciki, ta yadda Idan ta ji matsala ta gyara mata ta hanyar mulmula cikin a hankali da kuma yin amfani da wani dan karamin Koko wajan gyara Shi ta yadda lokacin haihuwa zai fito cikin sauki salamun -salamun.

Kula da mai Ciki Wani muhimmin aikin Ungozoma za taita kula da mai ciki wajan hanata yin wasu abubuwa ko sata ko hanata shan abu mai daci, da kuma bata magungunan rage Zaki, da kuma samun Karin karfin jiki a lokacin Nakuda.

Gyaran dakin Mai Ciki
Yanayin gyaran dakin mai ciki iri biyu ne kafin haihuwa da kuma bayan haihuwar. Ungozoma takan kawar da kayan dakin mai haihuwa gefe guda dan ta sami sararin da za ta haihu.

Gyaran daki na biyu Shi ne bayan an haihuwa Ungozoma zata gyara dakin tsaf ta maida Shi yadda yake.

Karbar Haihuwa  Dazarar anga Nakuda ta kankama, haihuwa ta doso gadan -gadan sai Ungozoma da dangi masu taimaka wa mai haihuwa su shiga shiri Karbar haihuwar.

Ayyukan Ungozoma suna da yawa kamar bata taimako na abinda za ta sha lokacin Nakuda yankan cibi dss. Amma konan muka tsaya Ina ga za mu iya fahimtar Wacece Ungozoma da kuma Ire-irenta da Irin gudunmawar ta ga mai ciki da kuma abin haihuwa (Jariri).

Babu Shakka Babu Wani mutum a Duniyar Nan da Ungozoma Bata Yi Masa Rana ba.

Jinjina Ga Ungozoma (Midwives).

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tue 06-08-2019

Sunday, 2 June 2019

ZAKKAR FIDDA KAI DA HUKUNCE HUKKUNCENTA

ZAKKAR FIDDA KAI (ZAKKATUL FITIR)
Zakkar Fidda Kai Sadaka ce da Manzon Allah ya farlanta ta yayin da aka gama azumi, An kiran ta zakkar fidda kai ne saboda tana wajaba ne idan an gama Azumin Ramadan gabadaya. Da Larabci ana kiranta da Zakkatul Fitr Kalmar Fitr an ciro tane daga Iftar (Wanda yake nufin Buda baki), Haka Ita ma Kalmar Iftar an samo tane daga Kalmar Futoo (Wacce ake nufi da Karin Kumallo) (Wato Breakfast).

Hukuncin Zakkar Fidda Kai
Zakkar Fidda kai wajibi ce akan dukkan musulmi, wanda ya mallaki sa'i daya na abinci (kamar kwano daya kenan) wanda ya fi yawan abin da zai ciyar da iyalansa. Mai ba da zakkar zai fitar wa da kansa, matarsa, da duk wanda ciyar da shi take kansa, har ma dan jaririn da yake cikin ciki.
Dalilin wajabcinta shi ne abin da aka rawaito daga Dan Umar (RTA) ya ce, “Manzon Allah (Saww) ya wajabta zakkar fidda kai, sa'i daya na dabino, ko sa'i dayan da sha'ir, an wajabta ta a kan bawa, da da, namiji da mace, babba da yaro daga cikin musulmi. Manzon Allah ya yi umarni a bayar da ita zakkar kafin mutane su fita sallar idi”[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Lokacin Da Ake Fitar Da Zakkar Fidda Kai
An fi son a fitar da zakkar fidda kai ranar Idi, bayan alfijir ya bullo kafin sallar Idi. Kuma ya halatta a gabatar da ita kafin ranar idi da kwana daya ko biyu, saboda sahabbai sun yi haka.
Ba ya halatta a jinkirta ta har bayan idi, saboda hadisin Dan Umar wanda ya gabata in da yake cewa : “Manzon Allah (Saww) ya yi umarnin a ba da ita kafin fitar mutane zuwa sallar idi”.
Haka ma a cikin hadisin Abdullahi dan Abbas, Manzon Allah (Saww) ya ce, “Wanda ya bayar da ita kafin sallar idi, to zakka ce karbabbiya, wanda kuwa ya bayar da ita bayan sallah, to sadaka ce daga cikin sadakoki”[Abu Dawud ne ya rawaito shi].

Gwargwadon Abin Da Ake Fitarwa A Zakkar Fidda Kai
Kowane mutum sa'i [Sa'i Dayan na Alkama yana daidai da kilo biyu da giram arba'in.] daya ne, daga cikin abincin da dan mutane suke ci, kamar shinkafa, dabino, alkama, saboda hadisin Abu Sa'id Al-khuduriy – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai daga abinci a zamanin Manzon Allah (Saww) ranar qaramar sallah”
Abu Sa'id ya ce, “Abincinmu a wannan lokaci kuwa shi ne Sha'ir da zabibi da cukwi [Cukwi : Shi ne nonon da ya bushe, a na girki da shi.], da dabino " [Bukhari ne ya rawaito shi].

Wadanda Ake Bawa Zakkar Fidda Kai
Ana bawa wadannan mutanen guda takwas zakkar fidda kai, saboda sun shiga cikin fadin Allah Madaukakin Sarki “Kadai Sadaka a bawa faqirai …”. (Attauba : 60).
Abin lura a wajen wanda za’a bawa har wayau shine, Za a bawa miskini ne ko fakiri wanda ba ya da hali, kamar dai yadda Annabi (SAW) ya ambaci lafazin Miskini, to shi ne za a ba shi, ba lallai sai an rarraba ga wadanda aka ambace su a cikin Ayar Zakka ba cikin suratul Taubah, amma wani yana iya hawa tudu biyu, a ba shi don ya cancanta, sannan sai ya bayar don ya samu wadatuwa.

Hikimar Zakkar Fidda Kai
1- Tsarkake mai azumi daga maganganun wofi da na batsa, saboda abin da aka rawaito daga Abdullahi Dan Abbas (RTA) ya ce, “Zakkar fidda kai tsarki ce ga mai azumi daga maganganun banza da ayyukan batsa, kuma ciyarwa ce ga miskinai”[Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Saboda mafi yawanci mai azumi ba ya rabuwa da maganganun da basu da amfani da wasannin shirme, da maganar da ba ta da fa'ida, to wannan sadakar sai ta zamar masa tsarki daga irin wadanncan maganganun haramun da ya yi, wadanda suke rage ladan ayyuka, suna rage azumi
2- Yalwatawa miskinai da talakawa, da wadatar da su ranar idi daga roqon mutane, roqon da yake dauke da qasqanci da wulaqanci a ranar idi, wadda take rana ce ta farin ciki da murna, sai su yi tarayya da mutane cikin farin cikin ranar idi.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 03-06-2019

Sunday, 7 April 2019

SUWA KE BADA KWANGILA DOMIN TABA DARAJAR SARKIN MUSULMI

Masu iya Magana sunce, Kowace Magana da lokacinta, haka kuma Kowane Lokaci da maganar da ta dace dashi, akan haka naga dacewar inyi irin wannan rubutu a wannan lokaci domin kowama (wanda ya sani da wanda bai sani ba duka) su san cewa, Jemage Ba Tsuntsu bane, Domin da yawa zaka samu wasu daga cikin mutane na kallon jemage a matsayin tsuntsu Alhali kuwa ba tsuntsu bane.
Wannan Rubutu zanyi shine zuwa ga kalar mutane guda biyu, Na farko sune, Wayanda ke karbar kwangila domin shiga kafafen yada labarai domin wargaza hadinkan Al’ummar musulmi. Mutane na biyu kuma masu bayarda kwangilar (daga baya kuma su fito suce ba su sukace ayi ba). To duk muna sane da ku da kulle kullenku na wargaza hadin kan musulmi da Allah (Swt) ya umurcemu da yi, domin hadin kai Allah ne ya kwadaitarda yinsa a tsakanin Al’umma. Haka kuma zagin Shugaban Musulmi (Wanda ke da Ikon fadar anga wata ko ba’a gani ba shima wargaje zaman lafiya ne), Idan zaka dubi Alqur’ani gaba daya zaka tarar yana karantarda hadin kai tare da biyayya ga shuwagabanni.

Misali, a cikin suratul Fatiha Allah (Swt) Yana cewa, “Ihdinas-Siraat-Al-Mustaqeem” (Ma’ana, Ya Allah ka shiryar damu ga hanya madaidaiciya), To meyasa Idan zakazo wajen karanta wannan ayar ta Ihdinas-Siraat-Al-Mustaqeem meyasa baka ce, Ihdinis-Siraat-Al-Mustaqeem ba (Ma’ana Ya Allah ka shiryarda ni ga hanya madaidaiciya) Saboda a nuna mana muhimmacin hadin kai.

Haka kuma a wajen fadin “Iyyaka na'aboudou wa iyyaka nasta'in” (Kai muke bauta kuma kai muke neman taimakonka) Meyasa bakace, ” Iyyaka a'aboudou wa iyyaka asta'in” (Kai nake bauta kuma kai nake neman taimakonka) ba? Ubangiji (SWT) Ya sanya wannan ne domin ya kara nuna mana muhimmanchin hadin kai. Babu shakka Idan kaje yin sallah ko kai kadaine (kuma ko a ina ne dole lamirin mutane na biye da kai) domin a nuna maka muhimmanchin hadin kai.

Bayan wannan ma Saboda Ubangiji ya kara nuna mana muhimmancin zaman lafiya ya sanya mana Sallah biyar a wuni, Sallar ma ba’a amince ka rufe daki kai kadai kayi ba in banda Uzuri, dole sai ka fito a masallachin Unguwa kayi sallar, Wannan kai tsaye kowa ma yana iya fahimtar karatun cewa, ana so a nuna mana hadin kai ne.

Haka a duk sati zamu hadu kusan yan Unguwanni da yawa muyi sallar jumu’ah wannan ma hadin kai ne ake nuna mana, Kai k ace wannan bai Isa ba Ubangiji ya sake sanya mana Wasu salloli biyu a shekara domin kawai a Kara nuna mana muhimmanchin hadin kai.

Duk dai domin Ubangiji ya nuna mana Muhimmanchi tare da Soyuwarsa akan mu hada kai, Ubangiji ya sanya mana Haduwa a saman dutse guda kwaya daya tal (Dutsin Arfa) tare da sanya Lada mai tsoka ga duk wanda ya samu damar halartar wannan tsayuwa a wannan dutse (na Arfa), Da zaka je ka samu Tsauni a garinku ko kasarku kaje a wannan rana kayi tsaye da zummar kayi tsayuwar arfa to wannan tsayuwar batayi ba, ba saboda komai ba sai don Allah (SWT) Ya nuna mana muhimmanchin hadin kai (Musamman na Musulmi).

Akan haka ne ma Allah (SWT) Yayi shuwagabanni (Annabawa) kuma yace a bi bayansu kuma yayi shuwagabanni na Al’umma ya kuma bada umurnin abisu a wurare daban-daban,

Misali, Idan Kuka zo zakuyi Sallah Dole ne ku sanya dayanku a matsayin liman kuma dole ne duk abinda yayi shi zakuyi a matsayinsa na shugaba a wajenku a wajen sallah. Bayan ya fara karatun fatiha duk zakuyi shiru kuna saurarensa, Bayan y agama yace, Amin Sannan kuma kuce. Wannan kai tsaye yana nuni da yin biyayya ga Shugaba (Akan abinda yake halat).

Amma yau Saboda lalaci na neman duniya wasu bata gari wayanda basu son ganin musulunchi yaci gaba suna so su kawo suka ga wayannan shuwagabanni. (Ya Allah ka shiryesu), Bazan Manta ba a Shekarar da ta gabata Shiekh Ahmad Gummi Yaje wajen Shirya Atiku da Obasanjo Nan da nan gari ya kaurace ana zaginsa tare da tsinuwa wanda kuma sam Abokan zaman mu ba haka suke ba.

Misali a wannan tafiyar da Shiekh Ahmad Gummi yayi yaje wajen wannan shiri a tare da shi akwai shugaban Kiristoci Rev. Hassan Maku Kuka wanda har yaje ya dawo baka ji Kiristan ko daya ba daya gaya masa Magana marar dadi. Wannan kai tsaye zai nuna mana kura kuran da mukeyi. Na yarda da wasu bata garin Mutane suna Amfani damu domin mu rika batanci ga shuwagabannin mu.

Ina wannan rubutun ne Ya’Allah Allah yasa su masu bada kwangilar suji tsoron Allah su daina, domin babu shakka Mun sansu kuma Idan muma muka ari Jahilcinsu muka fara bazasuji dadinmu ba ko kadan, Domin muna nasane da ko suwaye masu bada kwangilar (Akwai Mai Gida Yamma akwai Mai Gida Gabas) don haka Larabawa suna KARIN MAGANA Cewa, “MAN ANZARAKA FAQAD A’A ZARAKA” (Ma’ana Wanda ya Gargadeka Hakika ya gama shiryarda kai).

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mataimaki na Musamman ga Sarkin Musulmi akan Sababbin kafofin yada labarai
Sun 07/04/2019

Monday, 4 March 2019

WANENE SARKIN YAKIN DAULAR USMANIYYA




Daga cikin Malaman Da Shehu Usmanu Danfodiyo ya Tarar a Wannan Kasa Akwai Muhammad Alamin Alkanemi (Wanda yake Zaune a Borno yana Sarauta) Shi wannan Malamin Mahaifinsa Balarabe ne daga gari da ake kira Fazzana (dake cen Cikin Croatia).

Kamar Yadda Tarihi yazo Cewa, Wannan Malamin Kafin Zuwan Shehu yaje Makkah domin yin aikin hajji daga cen kuma sai ya wuce garin Mahaifinsa Fazzana domin ya ziyarci dangin Mahaifinsa daga baya kuma sai ya dawo kasarsa borno.

Kasancewar Tafiya a wancen lokacin tana da wuya, (domin mutum yakan shekara da shekaru bai samu yaje garin da zaije ba), wannan yasa Bayan dawowarsa sai ya tarar da Daawar Shehu ta mamaye ko Ina a fadin wannan kasa ko kuma Daula a wancen lokaci. Inda Shehu da Almajiransa suka yi waazi suka shiryarda mutane zuwa ga hanyar gaskiya, wayanda kuma suka ki jin wa’azi Shehu ya yakesu (A cikin wayanda aka yaka kuwa harda Jama’are da Hadeja) da sauran wasu garuruwa  wayanda suke cikin Rikon Borno.

Wannan dalili shiyasa Muhammad Alamin Alkanemi Ya zargi jihadin Shehu Usmanu Bin Fodio Inda ya nuna Jahdin na Shehu bai dace ba (Ma’ana bai dace ya yaki wasu garuruwa ba), a cikin wayannan garuruwa da bai dace a yaka ba akwai mutanen da Borno ke riko, Dominsu Mutanen Borno da wayanda suke riko Musulmi ne.

Wannan daliline ya sanya Alkanemi ya rubuta wasika Ga Shehu yana zargin Jahadinsa, Bayan Wasikar Alkanemi ta zowa Shehu da Almajiransa, nan take Shehu ya Umurci da Muhammad Bello Dansa da ya mayarwa da Alkanemi amsar wasikarsa.

A haka Alkanemi ya rika turo wasika inda shi kuma Shehu yana sanya Bello yana maida martani. A Wannan yanayine Allah (Swt) ya karbi ran Shehu Usmanu (Allah ya jikansa da Rahama), Har bayan Mutuwar Shehu Aminu Alkanemi bai daina turo wasika bag a Sarakunan Daular Usmaniya, Inda daga karshe dai Alkanemi ya Rubutowa da Muhammad Bello wasika akan Cewa, Zaizo ya yaki Daular Usmaniyya. Kuma zai fara yakar Kano (tunda tana daga rikon Daular Usmaniyya dake da Hedkwata a Sokoto).

Bayan Samun wasikar Alkanemi Sai Sarkin Musulmi Muhammad Bello ya rubutawa da Yakubun Bauchi (Sarkin Bauchi), Akan Cewa, Ya tari Alkanami da yaki (Wanda a lokacin (Kai harma a yanzu ) Sarkin Bauchi yana karbar Umurni ne daga Sarkin Musulmi dake Sokoto).

Inda nan take Yakubun Bauchi ya shirya Rundunar yaki yaje ya tari Aminu Alkanami (Suka gwabza yaki mai yawa a tsakaninsu), daga karshe Yakubun Bauchi ya samu nasara ga Alkanami, Nan take Alkaname ya gudu, Shi kuma Yakubun Bauchi ya bishi har tsawon kwana ukku bai kama shi ba.

Wannan Dalili yasa aka Bawa YAKUBUN BAUCHI (SARKIN YAKIN YAKIN SARKIN MUSULMI MUHAMMADU BELLO), Wanda har yanzu Jikokinsa (Wayanda suke rike da Sarautar Bauchi suke, Rike da Sarautar Sarkin Yaki).

Don haka duk mai tunanin Ayi masa Sarautar Sarkin Yakin Sokoto to yanama daina wahalar da kansa domin Sarauta ce mai tarihi ba Sarauta ce ta Cuwa-cuwa ba.


Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 04-03-3019

Saturday, 24 November 2018

KUSKURE NE YARDA DA ALLURAR POLIO KO TA YELLOW FEVER

GAME DA ALLURAR POLIO KO TA ZAZZABIN SHAWARA MATSAYIN TUNANI NA DAYA DA BERAN BIRNI
********
Wata Rana Beran Birni Yaje Ziyara a wajen Beran Qauye, Sai Yace da Beran Qauyen, "Abokina amma fa kana shan wahala, kazo nan Qauye ka zauna kana cin Rogo da gyada idan ana ruwa kuma ka shige rame, kuma ramen Yazo ya cika da ruwa idan zai yiwu kazo muje Birni kaga Irin gidan da nake rayuwa a cikinsa (kaga yanda nake rayuwa mana)."

Beran Qauye Ya amince, Bayan Kwana biyu suka Kama hanya zuwa Birni. Daga isarsu sai Beran Birni yaja Beran Qauye a wani Katoton gidan bene.

Mai zai faru bayan Shiyarsu, sai Beran Birni ya kutsa kai ya shiga cikin rame, (nan Beran Qauye ya fara tunani, cewa, au yace inzo muje inga gidan da yake rayuwa a ciki amma kuma naga mun shiga rame).

Bayan shigarsu Ramen Da Dan lokaci sai Beran Birni Yace, To kaga zo mu fita mu gani ko Allah zaisa Masu gidan sun ajiye abinci India hannun mu zai kai mu ci. Anan ma Beran Qauye Ya shiga tunani amma kuma yayi shiru ya bishi suka fita daga ramen zuwa Neman abinci a cikin gidan.

Suna tafiya sai sukazo wajen wani plate Wanda aka ci abinci aka rage, sai Beran Birni yace wa Beran Qauye To Bisimillah yanzu kam ga abinci nan ya samu. Cikin mamaki Beran Qauye Ya Kalle shi tare da wasu tunane tunane a zuciyarsa amma dai yayi shiru baice komai ba, ya fara cin abincin.

Cen suna cikin Cin abincin sai suka jiyo takun kafafuwan mutane suna zuwa inda suke, cikin razani da tsoro Beran Birni Yace da Beran Qauye, Kai yi maza mu koma Rami ga masu gidanan sun dawo.

Bayan sun gudu sun buya Cen Sai Kuma Beran Birni Yace da Beran Qauye Zo mu fita ko za'a dace, Fitarsu keda wuya sai Beran Qauye Yaga An ajiye K'afar kaza a bisa wani faranti yaje haka ya dauka sai Beran Birni ya rike shi yace, dashi "Kai, Ai Mutum mugune, Kada ka dauka tarkone, KA SANI NI DUK INDA NAGA ABINCINA INDA BANA TSAMMANI TO BANA AMINCEWA DA SHI". Wannan Maganar ta Beran Birni Itace Maganar da Nake so mu sanya kwakwalenmu muyi nazari akanta.

Shin turawa Zasu Kashe Makuddan Kuddi su had'a Maganin Polio domin kawai Su taimaka mana? Wallahi A'a Sam Ba zasuyi ba.

Kaje ka karanta Qur'ani sura ta 2 (Al-Baqara) tun daga sura ta 38 har zuwa sura ta 138 Bayani take akan cewa su ba masu Qaunarmu bane.

Ni kam BANA (kamar Beran Birni) duk inda naga abincina Inda bana tsammani to Babu shakka ba zan Amince masa ba.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 24-11-2018

Sunday, 12 August 2018

SIHIRIN DA AKAYIWA ANNABI (SAWW)

A madina lokacin da yake Saura Shekaru 4  Annabi (Saww) Ya Kaura ya bar Duniya Al-amarin ya faru.

Sahabban Annabi (Saww) mutum uku suka rawaito Yadda wannan Al'amarin ya faru daga ciki akwai Nana Aisha (RTa) da Abdullahi bn Abbas (RTA) da kuma Zaidu bn Arqam (RTA).

Dukkanin Wayannan sun bada labari cewa, A watan muharram yahudawan madina, (Wato maqiya Annabi (Saww) suka hadu sukayi Wata tattaunawa (meeting) ta sirri sukayi kancewa Annabi Muhammad (Saww) fa addinin shi na karbuwa ko Ina da ko ina, Kuma gashi a baya munyi sihiri kala-kala ya shanye, munyi tsafi don kashi shi bai mutu ba.

Gashi Anyi yaqin badar bai mutu ba, anyi yaqin uhud ma bai mutu ba, Mun shirya makaqarkashiya anyi yaqin kandab amma ya tsira bai mutu ba.

A Duba bayanin Wannan Zama a Cikin Adh-dabaqatul kubra na ibn Sa'ad.

A Wannan Zaman sai sukayi matsaya akan cewa zasu je wajen wani kwararren masihirci a garin madina Mai suna LABIDU BN A'ASAM (Shi wannan Labidu balarabe ne ba yadudu bane), Ya musulunta amma musuluncin Sa na kafircine.

Bayan Sunje Sun Sami Labidu Sai suka ce yayi musu sihirin Da zai kashe Annabi (Saww) zasu bashi dukiya me yawa (dukiya Mai Nishi), suka shirya suka dauki sule uku 3 suka bashi a lokacin sule 3 kudine masu yawan gaske.

Sai Shi wannan masihirci ya nemi akawo Masa Kayan Da zai hada yayi wannan Sihiri dashi da Farko a kawo Masa tokar Zuma (Bayan an tsotse Zuma Akwai Wata tuka tuka), Sannan A Samo Masa tsarkiya kwaya guda (Wani zare Mai Kama da Jijiya Wanda ake yin jita dashi), sannan aje a Samo Masa hudar dabino namiji da Macce, Sannan a Samo Masa Allura guda Goma Sha daya, Abu na karshe Yana so a Samo Masa gashin kan Annabi (Saww).

Duk aka Samo Masa Wayannan Abubuwan Sai Gashin Annabi (Saww) Ne keda Wuya Sai aka samu Wata yarinya ko Yaro wanda yake shiga gidan Annabi (Saww) aka bukaci ta dauko matajin kan Annabi (Saww).

To da aka Sanya wannan yaro ko Yarinya ya dauko matajin Annabi (Saww) wanda yake taje kanshi, Bayan dauko matajin kai na annabi wanda ya tsufa Annabi (Saww) ya dena ma amfani dashi.

Akwai sauran dangashi daya makale jikin matajin, Da wannan gashi masihircin yasamu ya yiwa Annabi (Saww) sihiri dashi. Wannan matsafi Ya tara duk yaranshi mata suka yi ta yin tofi cikin kulli Da tsafe tsafe, daga cikin yayan nashi wata tace lallai indai har Annabin gaskiya ne To Zai bada labarin wannan sihiri Da aka Yi masa, ta fadi haka ne saboda yadda taga karfin sihirin domin sihirine Me hallaka mutum kai tsaye.

Wannan Masihircin yayi mutum mutumin Annabi (Saww) wato yayi gunkinsa Da danko, sai ya sanya gashin da aka samo na Annabi akan kayin gunkin Annabin da yayi. Yayi duk abinda zaiyi ya gama sihiri akaje can bayan gari ya samu wata tsohuwar rijiya wanda aka dena amafani Da ita, yasa aka shiga cikin rijiyar akwai wani duste cikin rijiyar Qato, aka daga wannan dutsen Akasa sihirin kasar aka danne da wannan dutsin.

To Bayan wannan Sai Annabi (Saww) ya fara rashin lafiya gashin kansa Yana zuba Haka kuma baya iya cin abinci sosai, saboda wannan Sihirin har sai da ta kaiga Annabi (Saww) yana ganin ya kwanta Da iyalinshi amma kuma ba haka bane.

Da ciwo yayi tsanani abu na na cigaba yana ramewa, sai Annabi (Saww) yayi ta addu'a yana addu'a yana neman Allah ya ya ye masa wannan ciwo.

Wata Rana Ya kwanta bacci sai yayi mafarkin mala'ika Jibril Da Mika'il su kazo daya ya zauna ta gefen damarsa daya ta gefen hagunsa sai suka Fara hira

mala'ika Mika'il Yace: Me yasamu wannan bawan Allah wato yana tambayar Jibri (AS), Sai Shi Kuma Yace Masa, Ai Anyi masa sihiri ne, sai Mika'il ya Kara tambayawa Cewa, Wayayi Masa sihirin? Sai Mala'ika Jibril Ya fadi Cewa, Labidu ne Dan A'asam, Kuma an binne sihirin ne akarkashin wata riji sunanta BI'IRI ZARWAN ( ﺏﺀﺭ ﺯﺭﻭﺍﻥ ) tana ciki Garin madina.

Wato kamar suna hirane shi kuma Annabi (Saww) yana jinsu. Suka gama suka tafi Sai Annabi (Saww) ya farka yaiwa Allah godiya, yace wa nana Aisha Allah yabani labarin abinda ke damuna kinji kinji wanene yamin sihiri ya binne a rijiya.

Nan take Anabi (Saww) Ya tura sahabbai suje wannan rijiya sukaje suka ya she rijiyar suka shiga suka daga dutsen da ya danne sihirin.

Suka ciro suka bawa Annabi (Saww) da Annabi (Saww) Yaga irin kulle kullen da ke jikin wannan mutum mutumin nashi, yaga ma sihircin ya soka Allurai goma sha dayane 11, a jikin dankon mutum mutumin.

Sai Allah ya saukarwa Annabi Da surori guda biyu wato suratul FALAQI DA NASI.

Idan Annabi (Saww) ya karanta aya daya daga suratul falaqi sai ya zare allura daya daga jikin wannan mutum mutumin nashi, sai yaji kamar ajikinsa aka cire.

Sai da Annabi (Saww) ya karanta surorin nan Masu dauke Da ayoyi goma sha daya ko wace aya in ya karanta sai ya cire allura daya har sai da yaji jikinshi ya warke yasamu lafiya.

A Duba A Cikin Sahihul bukhari Hadisi na 5763-66 har zuwa Da sittin Da shida.

Da sahihu Muslim hadisi na 2189.

Akwai Abubuwan Lura da Yawa a Cikin Wannan Hadisin Wanda ya kamata mu Yi la'akari dasu.

(1) Wannan Yana Nuna Mu'ujizar Annabi (Saww), Ga yadda aka Bayyana Sihirine Mai Girman Gaske Mai saurin Halakarwa. Amma Kuma Bai kashe Annabi (Saww) Ba.

(2) Na biyu Hadin Kai

Duk wani Abu duniya da kuke so ku aiwatar na Alkherine Kona Mugunta Sai Kun hada Kai kamar Yadda wayannan Yahudawa suka hadakansu suka tattauna.

Haka Shima Labid Sai da Taimakon 'Ya'yansa da suka hada Kai Suka You wannan mugun aiki.

(3) Na Ukku da Makusancinka Ake Hadawa Domin Ganin Bayanka.

(4) Tasirin Addu'ah Ga Dukkan wani Lamari da ya tsananta gareka.

Jamilu Sani Rarah Sokoto

Sun 12-08-2018

Saturday, 23 December 2017

AMFANI DA KANYA A MATSAYIN MAGANI BOKANCINE

AMFANI DA KANYA A MATSAYIN MAGANI BOKANCINE
********
Kwanannan Naje Qauye domin ziyara sai na taradda wani al'amari mai ban takaici wanda kusan tun daga wannan rana kullum sai na rika tunani akan wannan al'amari.


Al'amarin shine Wani audio ne ake yawo dashi, wanda wani Mutum ke bayanin Abubuwan da zasu faru a wannan shekara, Inda yace, An aiko shine Daga Saudiya, Kuma duka-duka su Ukku kawai aka aiko a duniya, sannan yace, Wannan shekarar bala’o’I da yawa zasu faru ma’ana shekara ce ta BALA’I, Sannan wannan mutumen yaci gaba da cewa, Duk wanda yasan yana yin bacci tun daga dare har safiya ta waye, to ya daina Idan bai daina ba to kuwa zai mutu matsiyaci a wannan duniya.

Wannan Mutumen ya fadi abubuwa da yawa wanda lokaci ba zai iya barni na kawo suba, Daga karshe dai ya bada magani, Inda yace, A nemi Kanya tana maganin cutukka da yawa a ciki kuwa hard a Ciwon HIV inda yayi rantsuwa cewa, Idan bata maganin HIV Allah Ubangiji yasa HIV ya zama ajalinsa (Iyazan Billahi Iyazah).

Farko dai Wannan Mutumen yayiwa Allah (swt) Qarya, Domin Cewa da yayi wannan shekara ta bala’ice to yana karyata fadin Allah (swt) ne a cikin Alqur’ani Mai girma.

Domin Al-Imamul Bukhaari ya ruwaito hadisi daga Saalim bn Abdullahi, bn Umar, daga Baban Saalim din, wato ( Abdullahi dan Umar(RA)), Yace, Manzon Allah (Saww) yace: “Mabudan Gaibu guda 5 ne, kuma babu wanda yasansu sai Allah (Swt). Sune Allah ya dunqule su a qarshen Suratu Luqman, inda yace: “Lallai ILIMIN TASHIN QIYAAMAH yana wajen Allah ne, kuma shike SAUKAR DA RUWAN SAMA, kuma YASAN ABINDA KE CIKIN MAHAIFA, kuma RAI BATASAN ME ZATA SAMUBA GOBE, KUMA WATA RAI BATASAN A WACE QASACE ZATA MACE BA, lallai Allah masanine mai bada labara” Imamu Bukhari ya ruwaito a hadithi na 4627, a babin tafsiri.

Kenan Cewa, da wannan mutum yayi, Bala’I zai faru a wayannan shekaru kamar yana cewa ne yasan abinda zai faru gobe (Wa’iyazubillahi), Kai tsaye zamuce wannan mutum ya karyata Allah da ManzonSa (Saww). Allah ya kyauta.

Cikin bayanan Wannan mutumen yayi Rantsuwa tafi a Kirya, Wanda wannan Ma fasikancine. Domin a cikin Rantsuwowin da malamai suka karkasa to kuwa yayi babba daga cikinsu.

Wannan rantsuwa itace, Al-Yaminul-Ghamus ((Rantsuwa mai halakarwa),  Wannan Rantsuwa malamai suka ce, ita ce: Rantsuwar da mutum zai yi ta akan karya domin cin hakkin wani. Saboda irin girman da wannan rantsuwar take da shi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabba a gare shi ya ke cewa "Dukkan wanda ya yanki hakkin wani mutum musulmi da rantsuwar shi to hakika Allah ya wajabta mishi wuta kuma ya haramta mishi Aljanna" Muslim ya ruwaito shi, (A’uzubillahi min zalik).

Sannan dukkan wanda ya bi wannan mutumen ya yarda da zancensa shima ya sabawa Allah (SWT) domin  Allah yana cewa "Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, wulakantacce." Suratul-Kalam, aya ta 10).

Abu na gaba ko na karshe da zamfadi da ke nuna wannan mutumen bokane shine, KANYA ba ta daga cikin itacen da aka fada a cikin Al’qur’ani mai girma da Hadisan Ma’aiki (Saww), Ku lura bawai ina cewa tunda bata cikin Alqur’ani da Hadisai ba ba ina nufin bata magani bane A’a bahaka nake nufi ba

Shi wannan mutumen ya fadi cewa, KANYA ita kadaice Itacen da ta dade a duniya domin tun rowan Duhana Ma’ana zamanin Annabin Farkon Annabi Nuhu (Alaihis Salam)  take, Itace kai bata mutu ba.

Kai tsaye Wannan Karyane domin Kuwa, tunda babu shi a Alqur’ani da Hadisi to A ina ya samo haka? Ni dai nasan Jerin Itacen da suka zo a alqur’ani da Hadisai In ganttatu In shaaa Allahu zan samu Lokaci In kawo su kamar yadda Imamu IBN Khathir ya tattarosu a cikin littafinsa.

Abu na biyu da ke nuna wannan Mutum Boka ne shine, Yace, Ba’a dibar wannan Itace sai Ranar LITANIN (monday), to meye matsalar sauran ranakkun? Babu shakka wannan ire-iren sharuddan da Aljannu ke gin da yawa mutane masu huldayya dasu ne don haka muyi hattara.

Idan mutum ya ci gaba da amfani da Ire-iren wayannan Sharudda babu shakka ya Janyo ALJANNU su rika hulta da shine babu kakkautawa. Allah ya tsare mu. Don haka mu kula.

Please A turawa ‘yan Uwa domin Suyi HATTARA Domin Amfani da Ita Aikin Bokayene.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 23/12/2017