Sunday, 8 January 2017

TARIHIN ICCEN FIR (X MAS TREE)

TARIHIN ICCEN FIR (X-Mas tree)
*******
Yazo a tarihi Cewa, Yahudawa da Nasara Sun kasance suna Boyewa Sauran Musulmai Hak'ik'anin ma'anonin wasu daga Cikin abubuwan su (Musamman na Addini).

Tun kusan Shekara biyu nake bibiya tare da binciken hakikanin Ma'anar Wannan Iccen da Nasara ke amfani da shi a wajen shagul-gulan da suke na murnar X-Mas.

Sai dai kuma duk labarun da nake samu sai in ga basu wadatar dani ba, (ma'ana hankalina bai kwanta da ingancinsu ba).

Amma yanzu Alhamdulil Lahi bincike yakai makula kuma amsa ta samu dai-dai kamar yadda dama nake tunani boyewa suke.

Kafin kawo hakikanin gaskiyar Al'amarin zan fara yin bayanin Qaryayyakin dasuke game da wannan Iccen.

Mutane na Farko sun tafi akan cewa, Mutum na farko da ya fara kirkiro da Sanya wannan Iccen a Gidansa Shine, wani mutum (mai wa'azin arna) d'an asalin Jamus (Germany) mai suna Martin Luther.

A karni na 16 ne Wata rana da dare yana tafiya a farkon dare (ana saura kwana d'aya ayi Bikin Christmas). Yana tafiya a wani gandu daji sai ya cira kayinsa sama ya dubi sama, sai ya hangi taurari suna haskawa gwanin sha'awa karkashin wasu itace.

Lokacin da ya koma gida sai ya shaidawa 'ya'yansa Wayannan taurari da ya hanga da suka burge shi tare da shaida musu cewa hakika wannan ya tuna masa da cewa, Annabi (Alaihis Salam), Jesus yakan sauko daga sama duk ranar wannanin biki domin shima ya gudanar da nashi farin ciki.

Saboda haka suka d'auke shi a matsayin Bauta mai zaman kanta a duk irin wannan lokaci sukan yi tafiya daga wani kogi da ake kira Baltic sea, wanda ke cikin Latvia zuwa Kasar Jamus (Germany).

Wasu daga cikinsu kuma suka ce, an fara amfani da wannan Iccen ne lokacinda St. Boniface ( 'dan asalin kauyen Devon, dake Ingila) ya bar Ingila zuwa kasar Jamus (Germany) domin yayi wa wasu daga cikin arna daga Jamus 'din wa'azi domin ya mayar dasu zuwa Addinin Nasara (Christianity).

Sai Yace, ya samu kansa a tsakiyar wasu arna (wayanda basu da addini), sai ya tarar dasu suna bauta zasu yanka wani yaro (domin su bayarda jininsa ga wani Icce da suke bauta).

Cikin fushi sai ya dakatar dasu yayi musu wa'azi ya umurcesu da daina bawa wannan itacen jini (Wani iccen oak). Sannan ya umurce su da su sare wannan Iccen.

Bayan sun sare shi cikin mamaki sai wani icce (mai suna Fir), ya fito ta inda aka sare wannan Iccen (na Oak).

Sai shi St. Boniface ya dauki wannan itace a matsayin Iccen da ke nuna gaskiya ga Addinin Kiristanci daga nan sai wayannan arnan suka kunna fitillu sai yayi wa wayannan arna wa'azi (saboda wannan fitila ne da arnan suka kunna aka yi musu wa'azi shiyasa ake k'awata wannan itacen da haske duk lokacin wannan biki).

Wasu daga cikinsu (Nasara), Sukace, wata Rana ne a daren Christmas. Wani manomi (mai yawan bauta) tare da Iyalinsa sun kunna wutar Itace domin su dumama Jikinsu.

Suna haka sai suka Jiyo an kwankwasa kofa, lokacin da wannan manomin ya isa a kofar ya bude sai ya tarar da wani yaro karami ne ke kwankwasawa.

Yaron ya gabatar da kansa a matsayin wanda yayi b'atan hanya. Sai wannan manomin ya yi maraba da shi tare da bashi abinci.

Tare da bashi wurin kwanan d'ansu domin ya kwana. Wayewar safiya shine ranar Christmas, sai waken Mala'ikku ne ya tashe su (Wa'Iyazubillahi). Lokacin da suka duba sai suka tarar wannan b'ataccen yaron ya koma Annabi Isah (Alaihis Salam).

Sai ya kama hanya zuwa Lambun wannan manoni dake cikin gida ya tsinko musu ganyen wani Icce (Fir tree), ya basu tare da yi musu godiya akan hidimar da suka yi masa.

To tun daga wannan lokacin, Nasara daga ko Ina a fadin duniyar nan sukan sayo wannan itace su kai gidajensu domin tunawa da wannan rana. Wannan shine Ra'ayin da Nasara suke Bayarwa game da wannan Iccen.

Sai dai kuma wasu daga Cikin Musulumi (har da Ni Jamilu Sani Rarah) mun tafi akan Cewa, Wannan Itacen suna Tuni ne game da abinda yake Cikin al'qur'ani Mai Girma Sura-Maryam.

A cikin wannan Sura Allah ya fa'ada a cikin aya ta 19 Cewa, An haifi Annabi Isah (Alaihis Salam) a Karkashin Iccen Dabino.

Wannan shiyasa suka Kawata Gidajensu da Masana'antunsu da Wuraren shakatawarsu da Wayannn Itace domin tunawa da Ranar Haihuwarsa.

Abin duba da Fahimta anan Shine, Baya Halatta daga Cikin Mu (musulmai) muyi murna ko taya su murnan Wannan Shagali.

Domin Annabi (Saww) Ya Fa'da a cikin hadisi Ingantacce Cewa, "MAN TASHABBAH BI KAUMIN FA HUWA MINHUM" ma'ana "Duk Wanda yayi kama da wasu mutane to yana daga cikinsu."

In shaa Allahu Zuwa Gobe Zan gabatar Muku da wasu Sunaye da na Bautar Shaidan LA da suke Sanyawa tare da Ma'ana ta musamman akan Christmas din.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Thu 22-12-2016

No comments:

Post a Comment