BOKO HARAM BASU DA ALAQA DA ADDININ MUSULUNCHI KO KADAN
**********
Duk Wani Mai Hankali Kuma Wanda Ya San Hakikanin Abinda ake Kira da Addinin Musulunchi, kuma ya Fahimtace shi hak'ik'anin fahimta. To zai tabbatar maka da cewa, aqidar Boko haram ta sha banban da Addinin Musulunchi.
Boko Haram Suna d'aukar duk wanda Baya tare dasu a matsayin Maqiyansu. Alhali Qur'anin Allah Ba haka Yazo dashi ba,
Allah (Swt) Yana Cewa, "YA KU MUTANE, LALLE NE MU, MUN HALITTA KU DAGA NAMIJI DA MACCE, KUMA MUKA SANYA KU DANGOGI DA K'ABILU, DOMIN KU SAN JUNA. LALLE MAFIFICINKU DARAJA A WURIN ALLAH (SHINE) WANDA YA FIKU TAQAWA. LALLE NE ALLAH MASANI NE MAI KIDIDDIGAWA." (Suratul Hujurat aya ta sha 13).
Boko Haram Sun Kashe Musulmi Kuma Sun Kashe Wayanda Ba Musulmi ba. Alhali Qur'ani Mai Girma Bai Yi Umurni da haka ba,
Allah (Swt) yana Cewa, "LALLE NE WANDA YA KASHE RAI BADA WANI RAI BA, KO B'ARNA A CIKIN KASA, TO KAMAR YA KASHE MUTANE DUKA NE, KUMA WANDA YA RAYA RAI, TO KAMAR YA RAYAR DA MUTANE GABA D'AYA NE" (Suratul Ma'Ida aya ta 32).
Kusan Shekara Biyu zuwa Ukku da Boko Haram suka Sace 'Yan Mata (Budare) da sunan wai dole sai sun shiga Aqidarsu, Alhali Allah (Swt) yayi baice haka ba.
Allah (Swt) Yana Cewa, "BABU TILASTAWA A CIKIN ADDINI" (Suratul Baqara aya ta 256).
Bayan Sace Wayannan Yara Boko Haram Suka Aurar dasu da K'arfin Tsiya, Alhali Allah (Swt) baice Haka ba,
Allah (Swt) Yana Cewa, "YA KU WAYANDA KUKA YI IMANI, BAYA HALATTA A GAREKU KU GAJI MATA AKAN TILAS." (Suratul Nisa'I aya ta 19).
Boko Haram Sun Kasance Suna So su Tilastawa Al'umma bin Aqidarsu (har suna kallon kowa a matsayin kafiri in ba a tare dasu kake ba), Alhali Allah bai ce haka ba
Allah (Swt) Yana Cewa, "KUMA DA UBANGIJINKA YA SO, DA WAYANDA SUKE A CIKIN K'ASA SUNYI IMANI DUKANSU GABA D'AYA. SHIN KAI KANA TILASTA MUTANE NE HAR SU KASANCE MASU IMANI?" (Suratul Yunus Aya ta 99).
Boko Haram Suna Yin Zalunchi Tare da Rarraba Kawonan Jama'a (Kafirai da Musulmi), Alhali Allah bai ce haka ba.
Allah (Swt) yana Cewa, "LALLE ALLAH NA YIN UMURNI DA ADALCI DA KYAUTATAWA, DA BAIWA MA'ABOCI ZUMUNTA, KUMA YANA HANI GA ALFASHA DA ABINDA AKA QI NA RARRABE JAMA'AH. YANA YI MUKU GARGADI , TSAMMANIN KU, KUNA TUNAWA. (Suratul Nahl aya ta 90).
Abinda Zance A Qarshe dai Shine, Boko Haram Suna Yin Ta'addanci Suna Jingina Shi ga Yin Aikin Allah, Alhali Allah (Swt) Baice haka ba,
Allah (Swt) Yana Cewa, "KUMA KADA KUYI TSOKANA, LALLE ALLAH BAYA SON TSOKANA." (Suratul Bakara aya ta 2)
Babu Shakka Boko Haram Ba Addinin Musulunchi bane kum Ya sab'a koyarwar Addinin Musulunchi. Ko gobe Idan ka tashi Lissafo Musulmi Masu banbancin Aqida kada ka Sanya Boko haram a Ciki domin Ba Addinin Musulunchi bane.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
30-12-2016
No comments:
Post a Comment