Sunday, 8 January 2017

MEKE KAWO KARUWANCI A CIKIN AL'UMMAH

MEKE KAWO KARUWANCI A CIKIN AL'UMMAH? 01
**********
Daga Cikin Manyan Abubuwanda Ke Kawo Karuwanci a Cikin Al'ummah akwai wata hanya da Kamfunna ko Bankuna ke bi domin Samun abokan Ciniki (wato Costomer).

Sai Su d'auki Macce Kyakkyawa Su bata Matsayi na Marketing Manager (Ma'ana Shugaba ta masu Nemo Abokan Ciniki), babu Shakka Irin Wannan Shike jefa Wasu da yawa daga cikin Mata Yin Karuwanci.

Huraira Kyakkyawar Macce ce Son Kowa Qin Wanda Bai samu ba (ma'ana k'in wanda ya rasa), Huraira ta Kammala karatunta game da Abinda ya Shafi Kasuwanci (Business Admin), kuma Cikin taimakon Allah ta Samu sakamakon Jarabawa Mai Kyau. Taje tayi Hidima ga K'asa (Ma'ana NYSC) ta kammala.

Huraira na da kyawo matuk'a kuma a lokacin da take karatunta akwai wanda suka yi yarjejeniya akan Idan ta kammala karatu zasuyi Aure kuma zai barta taci gaba da Aikin a duk Inda ta samu aiki.

Bayan kammala Hidima ga k'asa (NYSC) Sai Huraira ta Samu Aiki a d'aya daga cikin Manyan Bankuna da ake ji dasu a K'asarnan kuma ta Samu matsayi na Shugabar Masu nemo Abokan Huld'a ko Ciniki (Marketing Manager).

A kwana a tashi Auren Huraira da Musa (Wanda shine Sukayi Alk'awarin Aure) ya tashi, Aka sanya Ranar aure cikin Iyawar Allah har Ranar aure tayi Aka D'aura Aure Ango da Amarya Suka tare cikin Jin dadi da kwanciyar Hankali.

Bayan Wata Hudu da Auren Su wata Rana Huraira ta je wajen Aiki Sai ta tarar Cewa, Babban Manaja yana Jiranta a Sama (zasuyi Meeting Ita da Shi).

Huraira ta Hau Saman Bene domin Jin Zaman da zasuyi. Huraira ta Same shi yana Jiranta.

Tayi Sallama ta Samu Waje ta Zauna, bayan Sun gaisa da manaja ya yi mata barka da Shigowa Sai Ya soma yi mata bayanin dalilin Zaman nasu ya fara da Cewa, "Wato Malama Huraira We are Under Problematic." (Ma'ana Muna Cikin matsala babba).

Huraira ta tambaya ko me ke faruwane? Sai manaja ya ci gaba da Cewa, "Jiya Misalin K'arfe Goma na Dare Babban Sashe (wato Branch) daga Lagos suka turo mana da Wannan takarda." Ya mik'a mata takarda.

Yaci gaba da Cewa, "Takarda Ce d'auke da Sa Hannun General Manager akan Cewa, Ni da ke Za'a kore mu makawar Sashin (Branch) din mu bai samo wani wanda zai sanya Hannun Jari har Naira Miliya d'ari biyar ba a Cikin Wannan Bankin ba." "Kuma Sati Guda muke da shi."

"Miliyan d'ari biyar...?" Huraira tace tare da Zaro Ido. "Eh miliyan tari Biyar" "to Ina Zamo samo wanda zai iya sanya wayannan ma kuddan kudade haka Manaja?"

Manaja Yace, Kada Huraira ta damu Zaije ya Nemo wanda Zai sanya Miliyan D'ari 3 don haka ita taje ta samo wanda zai sanya Miliyan D'ari 2.

A haka Huraira taje tayi ta neman Wanda zai saka Miliyan d'ari 2 a Bankinsu domin kada a koreta.

Kwatsam wajen Neman Wayanan kuddi Har Huraira taje Wajen wani Alh. A Unguwarsu domin Neman wayannan kud'aden.

Wannan Alh. Kuwa mugun tataccen Mazinaci Ne. Lokacin da Huraira taje Tayi masa bayanin Abinda ke tafe da Ita da kuma matsalar da take fuskanta na kora (wanda saura kuma Kwana biyu wa'adi ya cika).

Wannan Alhajin kai tsaye ya nuna maitarsa a fili game da Huraira tare da bayyana mata zai iya ma sanya d'ari biyar din duka da sharadi in har zata bashi had'in kai.

Huraira Cikin Firgici da tsoro ta bar wurin Alh. ta koma gida a cikin takaicin abinda taji daga bak'in Alh.

Bayan Mai Gidanta ya dawo ta gaya masa abinda Alh. ya gaya mata tare da Nemansa Shawara akan yanda zata fitowa wannan matsala Tunda kwana biyu ne Suka rage musu.

Jin Haka Shiya sanya Mai Gidan nata Hana ta aikin Gaba d'aya domin Tseratar mata da mutumcinta tare da k'are mutuncin Iyalinsa.

Babu Shakka Wannan Na daga Cikin Abubuwa da Ke Kawo Karuwanci a Cikin Wannan K'asa, a tunanina Da ace Wannan Baiwar Allah ta amince wa Wannan Alhajin da ya riga Ya Bud'a mata hanyar B'arna.

Da Yawa Daga Cikin Matan da Kamfunna da Bankuna Ke Sanyawa  Marketing bayarda jikinsu Suke yi Sannan Su samu Masu sanya hannun Jari a Kamfani ko Bankunansu.

A lura da Kyau Karuwanci Ya Kasu Kashi Ko kuma Ince Gida Biyu.

Wallahul Musta'In

Jamilu Sani Rarah Sokoto.
03-01-2017

No comments:

Post a Comment