MURNAR SABUWAR SHEKARA BAYA DA ALAQA DA KIRISTOCI BALLE MUSULMI.
**********
Ada na dauka Cewa, Genegoria kalanda Kalanda ce da Ya kamata Inyi farin ciki da samuwarta. Har ina ganin duk wanda baya bikin wannan Sabuwar shekarar a matsayin wanda bai waye ba (bagidaje).
Haka ma na san Cewa, Da dama mutane suna d'aukar cewa an fara amfani da wannan kalanda ne bayan haihuwar Annabi Isa (alaihis Salam) amma tarihi ya nuna cewa
Romawa sun fara amfani da wannan tarihi tun kafin a haifi Annabi Isa da shekaru (750).
Amma lokacin ba sunanta kenan ba, kuma a lokacin ba da juyawar rana ake lissafa ta ba, da juyawar wata ne (kamar yadda na Hijirah yake a yanzu) sai dai a lokacin watanni goma ne a cikin shekara guda mai makon yanzu da suke goma sha biyu.
A cen da Watanni suna farawa ne daga d'aya ga watan Maris, March su k'are da k'arewar watan Disamba (kenan babu febuary babu January).
A shekara ta 700 kafin haihuwar Annabi Isa, sarkin Roma Numa Pontilius wanda ya rayu tsakanin (673-716) kafin haihuwar Annabi Isa, ya k'ara wayannan watanni guda biyu; January , da kuma February daga nan watannin kalandar suka koma goma shabiyu maimakon goma.
An ci gaba da amfani da d'aya ga watan Maris (March) a matsayin farkon shekarar Romawa, sai dai kuma a shekara ta 153 kafin haihuwar Annabi Isa, sai aka musanya shi da Janairu (January).
Sai dai hakan bai hana a yi bikin sabuwar shekarar a watan Maris d'in ba a wasu lokuta.
Ana kiran shekara ta 46 kafin haihuwar Annabi Isa da “Shekarar rud'ani” saboda sarkin Roma na wannan lokaci Julius Caesar ya kara kwanaki har casa’in a kalandarsu to Roma wai don ya
saisaita hargitsewar da ta yi gameda abin da ya shafi yanayai (hunturu, bazara, damuna, kaka
dss) to sai abubuwa suka k'ara dagulewa, haka ta sa ya nemi shawara da gudunmawar wani
Bamasare masanin ilimin taurari wai shi Sosigenes d'an garin Iskandariyya, wanda shi kuma ya k'irk'irar masa sabuwar kalanda da ta ginu akan juyawar rana.
Tun daga lokacin sai Romawaa suka koma amfani da wannan kalanda da aka gina ta akan juywar rana, maimakon tasu ta da ta ginu akan ganin wata. Harila yau, a wannan shekarar ne aka tabbatar cewa kowace sabuwar shekara a garuruwan Romawa baki d'aya za ta rik'a farawa ne daga d'aya ga watan Janairu, ba wani sab'ani.
An rad'awa wannan sabuwar kalanda suna da kalanda ko tarihin Julian calendar , kenan an jingina ta zuwa ga sarkin da ya nemi a samar da ita, sarkin Roma Julius An ci gaba da amfani da wannan kalanda a k'asashen turai, da kuma wasu yankuna na duniya, kafin, da bayan haihuwar Annabi Isa.
Daga shekara ta (470-544) bayan haihuwar Annabi Isa, an yi wani babban Fasto a can yankin Romaniya mai suna Dionysius Exiguus ana yi masa lak'abi da (Dennis the Small).
A shekara ta 525 wannan Fasto ya rubuta jadawalin bukuwan Easter (Bikin da kiristoci suke yi a duk shekara saboda tashin Isa Almasihu daga matattu kamar yadda suke cewa)
To a cikin wannan jadawali, maimakon ya yi amfani da shekarar da aka saba amfani da ita kafin shi wato Diocletian era sai ya canza ya yi amfani da “A.D” bisa dalilin cewa shi Diocletian shi ne
sarkin Roma wanda ya rura wutar wurtuma da azabtarwa mafi girma ta k'arshe da aka yi wa kiristoci a daular Romawa, don haka amfani da alamar shekarar dake d'auke da sunansa za ta rik'a motsowa kiristoci bakin cikin wannan halin
ni-‘yasu da kakaninsu suka samu kansu a ciki.
“A.D” ko “AD” tak'aitawa ce ta jumlar Latin: “Anno Domini ” ma’anarta da ingilishi: “In the year of the Lord” Ko “In the year of our Lord” ma’ana “A shekarar ubangiji”
Ko kuma “A shekarar ubangijinmu”
Wannan ubangijin nasu shi ne Annabi Isa kamar yadda yake b'aro b'aro a wata sigar daban a yaren Latin; “Anno Domini Nostri Iesu (Jesu) Christi ” ma’anarsa ta ingilishi (“In the Year of Our Lord
Jesus Christ”). Ma’ana: (“A shekarar ubangijimu Yesu Almasihu”)
Duba da cewa bukukuwan da ake yi na sabuwar shekara da ake fara su daga d'aya ga watan Janairu bukukuwa ne na maguzanci da ba su da alak'a da kiristanci har a wurin kiristocin, majalisar masu kula da harkokon ziyara na kiristoci a shekara ta 567 bayan haihuwar Annabi Isa, suka hukunta cewa sabuwar shekara ba za ta rik'a
farawa daga daya ga watan Janairu ba.
Maimakon haka za ta rik'a farawa daga 25 ga watan Disimba wato ranar Kirsimeti (ranar da aka haifi Annabi Isa a fad'insu).
Tun daga wannan lokacin wasu yankuna na k'asashen turai suke yin bikin sabuwar shekara ranar 25 ga Disamba d'in, wasu kuma ranar d'aya ga watan Maris, wasu kuma ranar ashirin da biyar gareshi Kowane d'aya daga ciki wad'annan ranaku yana da alak'a da wani biki nasu.
A ranar 24 ga watan Fabrairu February na shekarar 1582 shugaban kiristocin duniya mabiya Katolika Catholics na wannan lokaci wato Pope Gregory XIII ya gabatar da wasu gyare gyare a kalandar genegoria shi a ganinsa za su magance wad'annan kurakurai, sai dai kuma kash!, tsugune ba ta k'are ba.
Domin kuwa manya masana lissafi da malaman taurari na duniya, ba na musulmi kawai ba, har da na kirista tuni sun gano cewa ita kanta “Gregorian Calendar” cike take da kurakurai na lissafi da ya wajaba a gyara, har wasu ma suka yi kira zuwa babban taron duniya na masana da kwararru da gaggawa don gyara wad'annan kurakurai.
Daga cikin canje canjen da Pope Gregory ya yi a sabuwar kalandar da ya gabatar akwai dawo da d'aya ga watan Janairu January ya zama shi ne mafarin shekarar tasu.
Duk da cewa kusan dukkanin cocinan da suke bin tafarikin Katolika nan take suka rungumi aiki da wannan sabuwar kalanda da Pope Gregory ya kawo, sai dai ba ta samu karbuwa a wurin mabiya Protestant ba sai sannu a hankali.
Misali k'asar Burtaniya tana daga cikin k'asar da ba ta rungumi aiki da kalandar ba sai a shekara 1752, kafin lokacin, masarautar Burtaniyan, da k'asashen America da take yi wa milkin mallaka a lokacin a watan Maris March
suke bikin sabuwar shekarsu.
Bsbban dalilin da yasa Pope Gregory ya mayarda d'aya ga watsn January a matsayin ranar Sabuwar Shekara, Shine domin a da cen shi babban maiyin bautane ga Gunti mai Suna Junus, domin ya ribanci kafirai sai ya koma mabiyin addinin Kirista domin ya dawo da wasu gyare gyare da sukayi dai-dai da bukukuwansu.
Janus wanda a cikin sunansa ne aka juyar a ka mayar January: Suna kiran Janus da Ubangijin kofofi, mai kula da shige da fuce a wurin Romawa. Yana dauke da Fuska biyu don lura da ko’ina b'angare.
A watan Janairu ake bikin tunawa da shi ba don komai ba sai domin sunansa ne aka dauka aka juyar ya zuwa January d'in.
Ga dai Photon Wannan Gunka nan. Duk lokacin da musulmi yayi murna da wannan Shekara to babu Shakka yana murna ne da tunawa da Wannan Gunka.
Karmu manta da Maganar Annabi (Saww) da ya Fa'da a cikin hadisi Ingantacce Cewa, "MAN TASHABBAH BI KAUMIN FA HUWA MINHUM" ma'ana "Duk Wanda yayi kama da wasu mutane to yana daga cikinsu."
Wallahul Musta'an
Jamilu Sani Rarah Sokoto
1-12-2017 (kalandar Ala k'ak'ai).