Wednesday, 7 December 2016

WASU DAGA CIKIN MUHIMMAN KALAMAI DA AKA GABATAR A TARON ZAMAN LAFIYA (PEACE AND UNITY CONFERECE) A ABUJA

WASU DAGA CIKIN MUHIMMAN KALAMAI DA AKA GABATAR A TARON ZAMAN LAFIYA (PEACE AND UNITY CONFERECE) A ABUJA

"Musulunchi ba Yana Nufin Ka dauki Wuka ko Adda ba kayi kabbara ka kashe wani. A'a musulunchi na nufin zaman lafiya da kyakykyawar mu'amula."___ Cewar, Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III.

"Ga Wani gwaji da yakamata muyi domin samun Kyakkyawar dangantaka da mu'amula."

"Mazaje Ku taimaki matayenku a aikace-aikacen gida, Sannan Idan zakuci abinci (misali da dare) ku dauka da hannunku ku ciyar dasu. Idan ka ciyar da ita to ita ma ta sanya hannunta ta ciyar da kai."___Cewa, Mufti Menk.

"Rayuwarka Kamar Photo Ce, Shi kuma Musulunchi Kamar Gidan sanya photo ne. Idan har kai musulmin kirkine, to ka dauko gidan photon nan ka sanya shi ciki. Kayi amfani da ilmin da kaji. Ka tafiyar da maganganu a aikace musulunchi ya zamo a cikin kirjinka. Kayi maganar gaskiya kada ka karkatarda magana. Kuma kada kayi da'awar abinda baka da shi sannan ka aiwatar da musulunchi a dukkanin rayuwarka."

"Babu wata kasa ko Al'umma da zasu ci gaba makawar basu bi dokokin Allah ba Sannan basu girmama Shuwagabanninsu ba, kuma basu bi koyarwar malamansu ba. Ka mu'amulancin malamai tsawon kwanakki bakwai dake cikin sati. Ka roki Allah tsayuwa akan Ibada ba saudaya ba domin ita ke bunkasa kasa" ___ Cewar, Sheik Assim Al-Hakeem.

"Allah yana Son Masu son Junansu ba don komai ba sai domin Allah. Makasudin samun nasara a wannan rayuwa shine dukkannin mu mu zama abu guda saboda Allah"

"Kada mu bari Zuciyoyinmu su jamu zuwaga ganin kyashin juna ko kuma Yawaita ganin laifin juna idan muka hadu wuri daya hakika zamu kai ga dacewa. Mu rika yiwa junanmu godiya. Sannan mu so makwaftan mu kamar yadda muke son kawunan mu. Hakika murmushi abincin ruhine mu zama masu gaskiya game da rubutun mu. Ina rokon Allah ya taimake mu duka. Mu rika rokon hadin kai ba rarrabara kawuna ba."__ Cewar, Sheik Muiz Bukhari

"Nawane ake Sayarda Manyan Gidaje a Abuja da Lagos? Hakika farashin da zaka biya ka shiga Aljanna Shine, ka yafewa dan uwanka duk laifin da yayi maka. Hakika hakkine akan kowanen mu akan ya yada zaman lafiya kuma umurnine akan mu rika yafewa juna. Ya ku mutane! Ku yada zaman lafiya tsakanin ku. Sannan ku ciyarda matalauta da masu jin yunwa. Ku sowa dan Uwanka/'yar uwarka abinda kake sowa kanka. Hakika ba zaka zama mai Imani ba har sai ka sowa dan uwanka abinda kake sowa kanka. Allah yana son masu gaskiya."___ Cewar, Sheik Muiz Bukhari

"Idan har da gaske kana Son Manzon Allah (SAW) to kabi Allah sannan ka zama mai yafiya ka zama mai son Juna, Ka ajiye duk wani rudani gefe kada ka nuna kafi kowa iyawa domin yana kai mutum zuwa ga dolanci. Ka zama mai taka tsan-tsan ga lamurranka kada ka bari zuciyarka ta rufe ga gaskiya. Musulunchi ba addini ne kawai ba, A'a musulunchi hanyar Rayuwa ce. Nemi ilmin gaskiya. Allah ya Albarkacemu da kyakkyawar fahimta ka tsare mu da Ilmi mai yawa saboda ilmi mai yawa Wani lokaci cuta ne."___ Cewar, Sheik Muiz Bukhari

"Kayi hankali da yawan ganin laifin mutane da yawan ganin Laifin Shuwagabanni. Ka yarda da kanka ka gyara halayenka wannan shi zai cenja gidajenmu, da 'yan uwanmu da Al'ummar mu dama Duniya gaba ki daya ka yarda da kanka ka kauracewa miyagun halaye ka tuna cewa Adanannar dukiyarka na Aljanna. Ka yarda da Allah kada ka taba debe tsammani kayi kaffa kaffa kada ka taba debe tsammani daga rahamar Allah. Allah Yace; "KA GAYAWA BAYINA WAYANDA SUKA CUCI KAWUNANSU KADA SU TABA DEBE TSAMMANI DAGA RAHAMAR ALLAH"..Ya Allah ka hada mu a lambun Aljanna."____ Cewar, Sheik Muiz Bukhari

"Kada ka shagaltu da ilmin da ka samu na Wannan taro (na wa'azi) na kwana biyu kace ya isheka kawai. Kayi godiya ga malaman kasarku da suka dade suna karantarda ku tare da tarbiyantar da ku."___ Cewar, Sheik Muiz Bukhari

"Allah ya kara mana Imani. Hakika addinin Musulunchi addini ne na Zaman lafiya ba na rikici ko tashin Hankali ba. Mu tashi tsaye kada mu sanya gajiyawa. Mu zama masu Alfahari ba masu girman kai ba."____Cewar, Ustaz Abubakr Sadiq

Ni da na fassara Ina fatan Wayannan Gwala-gwalan Kalamai zasu samu wurin zama a cikin Zukatan mu.

Anyi Wannan Wa'azin ne a  dakin taro da ke Abuja a Ranar 3 da Ranar 4  ga watan 12. 2016.

Fassarawa, Jamilu Sani Rarah Sakwkwato.

No comments:

Post a Comment