MATSAFI YA FA'DA HANNUN 'YAR MADIGO
********
Na hadu da wani daga Cikin Abokanai da na dau kusan Shekara 3 zuwa 4 bamu hadu ba, Sai dai a waya ko kuma A kafar sadarwa ta Facebook.
Ya bani Wani Labari da ya Girgizani tare da tunanin Anya kuwa irin wannan labari zan barshi a dunkule ba tare da na 'dan fincina wa mutane na shi ba. Ko ba komai wasu zasu fadaku tare da sanya Ido ga 'ya'yansu da Qannensu da matansu.
Shi Wannan abokin nawa yana da wani aboki wanda kusan baya jin shawararsu duk yanda suka bashi shawara (kuma zama dashi ya zamar musu dole ne.
Ablinda ke faruwa shine wannan abokin nasu ya kasance yana son wata kyakykyawar yarinya Qin wanda ya rasa Son wanda ya samu.
Yayi juyin duniyar nan akan ta so shi amma kuma ba ta ko sauraren shi balle har ya samu ta amince masa (ta yarda da soyayyarsa).
Kwatsam sai Zuciyarsa ta bashi shawara akan cewa, ai yaje ya kai ta wajen Wani wanda duk mai hankali ba zai so a kirashi da malami ba. Saboda yana amfani da malantaka ne yana bokanci.
Ya je ya sami bokan ya gaya masa shakkuwarsa. Nan take wannan bokan Sai ya je yayi tsibbace-tsibbacensa tare da kulle-kullensa da siddabaru akan yarinya ta so wannan yaron.
Ai kuwa cikin kan kanen lokaci sai wannan yarinya ta fada tarkon Aljannun da wannan yaron ya sa aka turo mata domin su rika nuna mata shi a matsayin masoyi.
Kwana tashi Sai ya zamo wannan yarinyar duk duniya bata ganin kowa face, wannan yaron. Shi kuma sai ya fara Jin dadi akan aikin boka yayi kyau.
To meya faru? Kwatsam sai Wata babbar macce ta kirayi wannan abokin nawa mai bani labari tare da gargadarsa akan ya yi maza ya umurci abokinsa ya rabu da wannan yarinyar saboda kayan su ne. Ina fatan wannan hausar ta fito da kyau.
Ma'ana Budurwarsu ce da suke yin madigo da ita (wa'iyazu billahi). Ya amince akan zai bashi shawara akan ya rabu da ita. Haka kuwa akayi ya kira abokinsu ya bashi shawara amma yaqi ji.
Bayan da wannan labari ya zowa saurayin sai kawai ya fara tunani a zuciyarsa cewa, dama wance tana madigo? Ai nan take ya shiga bincike akan ya gano gaskiya.
Ai kuwa sai ya gano Cewa, ashe tana Madigo kuma tafi kusan Shekara biyar tana wannan muguwar 'dabi'a (kenan wannan shibe dalilin da yasa taki amincewa da soyayyarsa tun farko, Sai da yaje wajen boka).
Nan ya fara nadama marar amfani. Eh nadama marar amfani kuwa saobda a duniya ya tsani yar madigo ko 'dan luwadi. Amma kash yau gashi ammasa Baiko da 'yar madigo.
Nan yaje wajen Bokansa akan a raba wannan magani da akayi domin ta soshi. Ai kuwa boka ya aiwatar da abinda ya umurce shi da yi (ya raba wannan magani).
Nan take taji bata sonsa kuma gashi an musu baiko. To meya faru ashe Ita ma tana da nata boka sai taje ta koka masa matsalarta.
Wannan boka yayi na shi tsafi ya gano cewa, tun daga farko magani yaron yayi mata. Ai kuwa da aka gaya mata sai tace ita ma ayi masa magani yaji duk duniya kowa baya so sai ita.
Nan take Wannan bokan ya aiwatar shi kuma wannan yaro sai gashi ya fada tarkon so da kaunar yarinyar baji ba gani.
Ganin irin yanda yake binta take wulaqantashi (kuma aurensu ya kusa), shi ya sanya wannan abokina mai bani labari ya shirya zama da yarinyar don yaji meye matsalar take yiwa abokinsa wulaqanci.
Ai kuwa sai ta fafe masa biri har wutsiya tare da gaya masa cewa, babu shakka ita 'yar madigo ce. Kuma ta lalata yara babu adadi kuma zata ci gaba da lalatawa.
Kuma auren abokinsa babu mahani domin tunda yayi mata magani ita kuma sai ta gwada masa ko wacece. Domin sai ta aure shi kuma bayan auren sai ta mayar da gidansa Kasuwa ta Safarar mata domin yin madigo (Wa'iyazubillahi).
Yanzu dai kam An kusa Aure.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Thus08-12-2016
No comments:
Post a Comment