MEYE LAIFIN SHUGABA BUHARI A CIKIN SADAKIN ZARAH?
*******
Tunkusan Lokacin da Akayi Sadakin Zarah 'yar Gidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ke samun Sak'onni akan ba'aji nayi sharhi ba game da wannan Sadakin.
Alhamduli Lahi bayan 'yan Uzurukka da suka sha gabada Sai yau Allah ya kaddare ni da Cewa wani abu game da wannan Sadaki.
Har yau har gobe Ina Kara kira ga 'yan Arewar mu akan Don Allah su daina Sanya Kansu cikin Kwano ko k'ok'o suna tunani su rika bude kawunansu suna tunani.
Da farko ina son mutane su san Wanene Ahmad Indimi sannan suyi tunani mai kyau game da shi Kafin Su rika yanke Hukunci game da duk wannan Sadaki na shi.
Kafin Nayi bayani akan Ahmad Indimi bari na fara bayani akan Jahar Borno (In da Cen ne Garin Su Ahmad da Mahaifansa).
Wani daga cikin Masu son jin ra'ayina game da wannan Sadakin ya min tambaya game da wannan sadaki na Zarah Buhari.
Amma mai makon In bashi amsa sai na kyale shi Na kira wata baiwar Allah Wacce 'yar asalin maiduguri ce.
Bayan na kira ta dauka sai na saka Speaker domin yaji me zamu tattauna ana akai. Bayan mun gaisa sai na tambayeta Cewa, "Shin har yanzu A maiduguri Miliyan daya ake Sadaki?"
Sai tayi dariya tace dani, "Humm yanzu wannan Recession da ake ciki wa zaiyi wani sadaki milion 1"
Sai nace, "To nawa ake yin Sadaki Maiduguri a yanzu?" Sai tace dani, "Dubu d'ari bakwai, d'ari biyar Ida kuma mutum bai da shi sosai Cikin Anyi hankuri an matse sai ya biya Naira dubu dari biyu da hamsin ko kuma dubu d'ari da Ashirin."
Bayan mun gama magana mukayi Sallama na kashe waya ta. Tare da tambayar wannan mai tambaya ta ko kaji wayar da nayi? Sai yace da Ni "Eh yaji ashe haka maiduguri suke."
Sai nace dashi to Wanda yayi wa Zarah Buhari Sadaki 'dan Maiduguri ne, kuma a maidugurin ma su ne manyan masu kuddi.
Baban Ahmad Wato Muhammad Indimi Surukine ga Tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Badamasi Babangida IBB.
Sannan Muhammad Indinmi Shike da kamfanin nan na Oriental Energy Resources Limited, kamfanin da ke da rijiyoyin mai har guda uku da suka hada da: OML 115 da ta Oldwok da kuma ta Ebok.
Sannan Shi Ahmad Indimi yana daga Cikin Manyan Daretoci na Kamfanin domin Shine daracta na Ukku a kamfanin.
Sannan Ahmad Indimi din da kake ji yana daga Cikin Matasan Samari da ke da taimako domin IDPs INTERNAL DISPLACE PERSONS (Wato mutanen da rikici yasa suka bar mazauninsu) ya taimakesu kusan da Naira Miliyan d'ari biyu har da wani abu.
Sannan Idan ka koma B'angaren Ita kanta Zarah Duk kusan Cikin 'ya'yan Manyan Kasarnan Kaf (ban cire ma kowa ba daga cikinsu), ta fisu taimako tare da Neman Dukiya. Domin har Ophanage (gidan marayu) take da shi.
To mene A Ciki don Shi Wannan matashin Mai kuddi ya bi Al'adar Garinsu ta yin Sadaki da Tsada? Tun da dai ba'a kaiyade kuddin Sadakin ba a musulunce.
A musulunce Kuddin Sadakin Bana yanda malamai suka yi kiyasi shine naira 8400, Shin don Allah akwai wanda yaga In da akayi Sadaki 10,000 a bana? In kuwa babu inda akayi to me yasa don shi yayi al'adar garinsu (na yin sadaki da tsada) abu zai zama abin Ganin Laifi.
Ni banga laifin Wannan Ba Gaskiya sai dai abinda muke cewa da Su Wayannan Samarin Sunyi kwaikwayo da Sunnar Manzon Allah (Saww) na Takaita Sadaki da Sun kyauta. Domin Manzon Allah (saww) yake cewa, Aure Mafi albarka shine wanda sadakinsa ya zamo mafi sauki".Kuma da Sun bar tarihi a kasarnan.
Da kuma sun kwaikwayi auren Nana Fatima da Sayyidina Aliyu da Sun burge duk wani ma'abocin Sunnah.
Lokacin da Sayyidina Aliyu (Rta) ya nemi Auren Nana Fatima (rta) bayan Annabi (Saww) ya tambayeta kuma ta amince sai Manzon Allah (Saww) ya cewa Sayyidina Aliyu (RA): "Ya Aliyu, shin kana da wani abu da zan daura maka aure da shi (sadaki)?".
Sai Sayyidina Aliyu (RA) ya ce: "Sai takobina da garkuwata, sai kuma rakumina na ban ruwa ", (a wata ruwayar an ce doki ne maimakon rakumin)
Sai Manzon Allah (Saww) ya ce: "Amma takobinka kana da bukatarsa, za ka yi yaki da shi a tafarkin Allah kuma ka kashe makiya Allah da shi.
Rakuminka kuma kana shayar da (gonar) dabinonka da shi, haka kana daukar kaya da shi, kuma yana daukarka a tafiye-tafiyenka.
Don haka je ka yi yadda za ka yi da
garkuwarka". Sai Sayyidina Aliyu (RA) ya je ya sayarwa Sayyidina Usman bin Affan (RA) da garkuwarsa a kan farashin dirhami 480, sai ya kawo wa Manzon Allah (saww).
Daga nan Manzon Allah (Saww) ya sanar da Musulmi zancen auren.
Haka kuma na So ace Zarah Buhari ta kwaikwayi Ummu Sulman An Ruwaito Cewa Sahabbai (RA) suna
Cewa, "FIYAYYEN AURE SHINE AUREN UMMU SULMAN (RA), DOMIN ITA SADAKINTA MUSULUNCI NE."
Ummu Sulman Itace Mahaifiyar Anas Bin Malik (Hadimin Manzon Allah (Saww)), lokacin da mahaifinsa ya rasu, taqi yin aure har Saida Abu Talha ya fito yana Sonta sannan ta amince zata aure shi amma da sharadi zaya Musulunta (Musuluntarsa Shine Sadakinta).
Bayan manyan attajirai da Masu mulki da Sadaukai sunyi ta fito mata amma taki amincewa dasu. To da ace Zarah Buhari ta Bukaci kada sadakinta Yayi tsada haka to babu shakka da ta kyauta.
Kuma ba zanga Laifinta ba ko na wanda zata aura ko mahaifanta don anyi mata sadaki naira miliyan 44, sai dai muna cewa a kamanta Sunnah ga dukkanin Abubuwa yafi.
Subhanallah...!
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 5/12/2016
No comments:
Post a Comment