Tuesday, 2 August 2016

TARIHIN DAULAR MUSLINCHI TA ANDALUS 2

TARIHIN DAULAR MUSLUNCI TA ANDALUS (Spain) Fitowa ta 2
*******************************************************


Ga wayanda Basu samu damar karanta Fitowa ta Farko ba Su latsa nan domin karantawa; jamilrara.blogspot.com/…/…/tarihin-kasar-andalus-spain.html…

Ci Gaban Tarihin;

Kasar Andalus Sai da ta Shekara 800 a cikin musulunci kuma daular musulunci. Amma a Ranar da Yahudawa sunka saka Andalus a gaba sai da wannnan kasa ta fita daga hannun Musulmi (ta tashi daga daular musulunci).

kasan cewa duka ka'idodin musulunci da ake bi a kasar da kewaye har sai da ta kai kafirai basa sha'awan shiga kasar, amma randa yahudawa suka bulla a kasar ba'a dauki shekaru 50 ba saida suka juyar da musuluncin. sunka rushe duk wani abu na musulunci akasar suka cenja Sunayen garin (daga na musulunci zuwa nasu na kafirci).

Har sai da ta kai ta kawo Gaba daya kasar ba'a yarda ayi addinin musulunci ba.
Babban abinda ya kawo haka a kasar kuwa rashin hadin kan da yahudawa suka sanya a tsakanin 'yan kasar. Wato babu hadin kai tsakanin kiristoci na asali da musulman da aka tilasta masu shiga adinin kirista. Haka ma tsakanin musulmin su kansu babu hadin kai.

To daga nan Sai tattalin arzikin kasar ya rika fadawa cikin nakaso da samun matsala tare da tabarbarewa.
Sakamakon ganin Tattalin Arzikin na tabarbarewa sai aka yi wani zaman tattaunawa (Metting) a Ingila don idan har aka bari tattalin arzikin kasar yana rushewa to mutanan kasar zasu watsar da kiristiyaniti zasu koma musulmai.

A zaman tattaunawar ne sunka yanke shawarar cewa za'a kirkiro da wani abu wanda zai hada kan 'yan kasar. A cikin tattaunawar akayi ta kawo abubuwan da ake ganin zasu karbu ga musulmi da kafirai amma duk wanda aka kawo aga bayayi. Anan ne wani ya bada shawara akan a kirkiro da gasar kwallon kafa a kasar domin zata karbu (musamman ga matasa musulmi da Kirista).

To anan ne aka kirkiro da kwallon kafa akasar ta spain. Wannan ne yasa aka debi dalibai akaje dasu kasar Ingila aka karantar dasu kwallon kafa da dabarunta tare da yanda zasu sanyawa mutane Sha'awarta.
Bayan sun kware sai aka turosu kasar ta spain don su karantar da matasan kasar kwallon ta kafa.
Anan ne aka kirkiro da wani kulob na kwallon kafa mai suna sevilla (Wanda asalin sunan wani garine na musulunci da ke cikin kasar ta Spain mai suna Ishbiliya).

Sevilla shine kulob na farko da aka kirkiro akasar ta Spain. (Wannan yafaru ne a shekarar 1890 zuwa 1899). daga baya aka kirkiro da spanish king cup. Wato copa del ray, Shi wannan kofin an kirkiroshi ne wajan bikin bada sanda ga sarkin kasar.

Haka a Shekarar 1905 aka samar da kulob din real madrid. sai kum kulob din Barcalona Sai Espenyol da ganan sai visaya. Wayannan kulob kulob din su sunka maye madadin musulunci a kasar. har sai da ya kasance musulmi yafi son kirista dan kulob dinsu da musulmi wanda ba dan kulob dinsu ba.

Haka sarkin spain mai suna king alfanso yace suna da wata kalma ta kiristoci wadda su sunka san sirrin dake cikinta (Wannan kalmar).kalmar tana da wani sirri.wanda sai dan kungiyar yahudawa yasan sirrinta.
Wannan kalmar itace real. wannan kalmar sarkin ya bada ita a shekarar 1927 yace duk kulob din dake son kalmar ya dauki wannan kalmar yabashi aronta.

Nan take kulob fiye da 10 sunka dauketa anan ne anka samu real zaragoza wanda ainihin sunan garin musulunci ne wanda ake kira saraqusda.

Sai Real betis, Real soceida, Real valadolid wanda shima asalin sunan garin musulunci ne mai suna valadu walid, Sai Real murcia, Real union, Real sporting gijon sai Real madrid. (In shaa Allahu zan kawo bayanin ma'anar Real anan gaba).

Haka ma a can baya akwai wani bayahude makiyin musulunci na gaske wanda yana cikin wayanda sunka yaki musulunci akasar ta Spain sunan sa santiago to shine aka sakama stadium din Real Madrid domin Girmamawa gareshi da girmama kwazonsa.

To ta hakane akaci musulunci da yaki akasar. yanzu yawan musulmai akasar ta spain akalla akwai musulmai dubu 500 kacal. Yayin da mutanan kasar kuma yawansu ya kai miliyan 36. wanda tarihi ya nuna kasar ta spain tayi zama kashi 95 cikin 100 musulmai ne kamar yadda na fada a baya
Kuma a cikin yawan musulmin a kasar dubu 500 to dubu 400 ba ainahin 'yan kasar bane bakine (wato ba yan asalin kasar bane).

Daga cikin Musulmi Mutum Dubu 100 kacal sune 'yan kasa. cikin dubu 100 din mutum dubu 20 sabbin musulmai ne dubu 80 ne kawai tsofaffin musulmai. Hakika da kwallo aka Shiga Kasar Spain aka Karya Kashin gadon bayan Musulunci a kasar ta Spain. Kuma dama yahudawa sunce kwallo addini ne mai zaman kanshi. kuma duk wanda ya shiga cikinta yau da gobe sai ya aje addininshi ya rungumeta don zai samu tarin kudin da ba zai iya samun kwatan-kwacinsu a addininsa ba. Haka kuma zai kashe mata kuddin da ba zai iya kashewa a addininsa ba. Kuma Zai bada lokacinsa lokacin da bazai iya ba addininsa ba.
Akwai wata waka da akayi a 2008 mai suna "Football is religion". haka ma shugaban fifa a lokacin Sep Blater yace Football is more than sport is a religing.

Kuma Wannan Gadkiya ne Saboda kiyasin da akayi a akwai masu sha'awar kwallon kafa sama da mutum biliyan 5. Yayin da yawan mutanan duniya gaba daya biliyan 7 ne. yayin da musulmai yawan mu be kai biliyan 2 ba. kunga masu kwallo da sha'awarta sun lunka yawan musulmai aduniya. Haka yanzu yan kwallo sune masu kudi a duniya.

Dan wasan Real madrid duk minti yana amsar sama da naira dubu 9 koda yana baccine. A duniya Bayan Bill gate 'dan Kasar America da yafi kowa Kuddi a duniya Sai Mutumen Spain mai suna Amancio Ortega shine na Biyu da kuddi a duniya wannan mutumen a talaka ya tashi amma ta dalilin yin tufafe wa 'yan kallo yanzu ya zama shine yafi kowa kuddi a kasar ta Spain kuma shine mai kuddi na biyu a duniya. (Shima zuwa gaba zan kawo tarihinsa da kuma yanda ya samu kuddinsa In shaa Allahu).

Mutane da yawa suna tambayar wai ina kulob kulob din nan ke samun wayannan makuddan kudade ne?
Watakila in na samu dama nan gaba zan kawo bayanai game da haka tare da kawo mutu wasu abubuwan da suka Shafi Daular musulunci ta kasar Andalus (Spain a yanzu In shaa Allahu).

Jamilu Sani Rarah Sokoto.
Mon 25/07/2016.

1 comment: