Sunday, 7 April 2019

SUWA KE BADA KWANGILA DOMIN TABA DARAJAR SARKIN MUSULMI

Masu iya Magana sunce, Kowace Magana da lokacinta, haka kuma Kowane Lokaci da maganar da ta dace dashi, akan haka naga dacewar inyi irin wannan rubutu a wannan lokaci domin kowama (wanda ya sani da wanda bai sani ba duka) su san cewa, Jemage Ba Tsuntsu bane, Domin da yawa zaka samu wasu daga cikin mutane na kallon jemage a matsayin tsuntsu Alhali kuwa ba tsuntsu bane.
Wannan Rubutu zanyi shine zuwa ga kalar mutane guda biyu, Na farko sune, Wayanda ke karbar kwangila domin shiga kafafen yada labarai domin wargaza hadinkan Al’ummar musulmi. Mutane na biyu kuma masu bayarda kwangilar (daga baya kuma su fito suce ba su sukace ayi ba). To duk muna sane da ku da kulle kullenku na wargaza hadin kan musulmi da Allah (Swt) ya umurcemu da yi, domin hadin kai Allah ne ya kwadaitarda yinsa a tsakanin Al’umma. Haka kuma zagin Shugaban Musulmi (Wanda ke da Ikon fadar anga wata ko ba’a gani ba shima wargaje zaman lafiya ne), Idan zaka dubi Alqur’ani gaba daya zaka tarar yana karantarda hadin kai tare da biyayya ga shuwagabanni.

Misali, a cikin suratul Fatiha Allah (Swt) Yana cewa, “Ihdinas-Siraat-Al-Mustaqeem” (Ma’ana, Ya Allah ka shiryar damu ga hanya madaidaiciya), To meyasa Idan zakazo wajen karanta wannan ayar ta Ihdinas-Siraat-Al-Mustaqeem meyasa baka ce, Ihdinis-Siraat-Al-Mustaqeem ba (Ma’ana Ya Allah ka shiryarda ni ga hanya madaidaiciya) Saboda a nuna mana muhimmacin hadin kai.

Haka kuma a wajen fadin “Iyyaka na'aboudou wa iyyaka nasta'in” (Kai muke bauta kuma kai muke neman taimakonka) Meyasa bakace, ” Iyyaka a'aboudou wa iyyaka asta'in” (Kai nake bauta kuma kai nake neman taimakonka) ba? Ubangiji (SWT) Ya sanya wannan ne domin ya kara nuna mana muhimmanchin hadin kai. Babu shakka Idan kaje yin sallah ko kai kadaine (kuma ko a ina ne dole lamirin mutane na biye da kai) domin a nuna maka muhimmanchin hadin kai.

Bayan wannan ma Saboda Ubangiji ya kara nuna mana muhimmancin zaman lafiya ya sanya mana Sallah biyar a wuni, Sallar ma ba’a amince ka rufe daki kai kadai kayi ba in banda Uzuri, dole sai ka fito a masallachin Unguwa kayi sallar, Wannan kai tsaye kowa ma yana iya fahimtar karatun cewa, ana so a nuna mana hadin kai ne.

Haka a duk sati zamu hadu kusan yan Unguwanni da yawa muyi sallar jumu’ah wannan ma hadin kai ne ake nuna mana, Kai k ace wannan bai Isa ba Ubangiji ya sake sanya mana Wasu salloli biyu a shekara domin kawai a Kara nuna mana muhimmanchin hadin kai.

Duk dai domin Ubangiji ya nuna mana Muhimmanchi tare da Soyuwarsa akan mu hada kai, Ubangiji ya sanya mana Haduwa a saman dutse guda kwaya daya tal (Dutsin Arfa) tare da sanya Lada mai tsoka ga duk wanda ya samu damar halartar wannan tsayuwa a wannan dutse (na Arfa), Da zaka je ka samu Tsauni a garinku ko kasarku kaje a wannan rana kayi tsaye da zummar kayi tsayuwar arfa to wannan tsayuwar batayi ba, ba saboda komai ba sai don Allah (SWT) Ya nuna mana muhimmanchin hadin kai (Musamman na Musulmi).

Akan haka ne ma Allah (SWT) Yayi shuwagabanni (Annabawa) kuma yace a bi bayansu kuma yayi shuwagabanni na Al’umma ya kuma bada umurnin abisu a wurare daban-daban,

Misali, Idan Kuka zo zakuyi Sallah Dole ne ku sanya dayanku a matsayin liman kuma dole ne duk abinda yayi shi zakuyi a matsayinsa na shugaba a wajenku a wajen sallah. Bayan ya fara karatun fatiha duk zakuyi shiru kuna saurarensa, Bayan y agama yace, Amin Sannan kuma kuce. Wannan kai tsaye yana nuni da yin biyayya ga Shugaba (Akan abinda yake halat).

Amma yau Saboda lalaci na neman duniya wasu bata gari wayanda basu son ganin musulunchi yaci gaba suna so su kawo suka ga wayannan shuwagabanni. (Ya Allah ka shiryesu), Bazan Manta ba a Shekarar da ta gabata Shiekh Ahmad Gummi Yaje wajen Shirya Atiku da Obasanjo Nan da nan gari ya kaurace ana zaginsa tare da tsinuwa wanda kuma sam Abokan zaman mu ba haka suke ba.

Misali a wannan tafiyar da Shiekh Ahmad Gummi yayi yaje wajen wannan shiri a tare da shi akwai shugaban Kiristoci Rev. Hassan Maku Kuka wanda har yaje ya dawo baka ji Kiristan ko daya ba daya gaya masa Magana marar dadi. Wannan kai tsaye zai nuna mana kura kuran da mukeyi. Na yarda da wasu bata garin Mutane suna Amfani damu domin mu rika batanci ga shuwagabannin mu.

Ina wannan rubutun ne Ya’Allah Allah yasa su masu bada kwangilar suji tsoron Allah su daina, domin babu shakka Mun sansu kuma Idan muma muka ari Jahilcinsu muka fara bazasuji dadinmu ba ko kadan, Domin muna nasane da ko suwaye masu bada kwangilar (Akwai Mai Gida Yamma akwai Mai Gida Gabas) don haka Larabawa suna KARIN MAGANA Cewa, “MAN ANZARAKA FAQAD A’A ZARAKA” (Ma’ana Wanda ya Gargadeka Hakika ya gama shiryarda kai).

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mataimaki na Musamman ga Sarkin Musulmi akan Sababbin kafofin yada labarai
Sun 07/04/2019

Monday, 4 March 2019

WANENE SARKIN YAKIN DAULAR USMANIYYA




Daga cikin Malaman Da Shehu Usmanu Danfodiyo ya Tarar a Wannan Kasa Akwai Muhammad Alamin Alkanemi (Wanda yake Zaune a Borno yana Sarauta) Shi wannan Malamin Mahaifinsa Balarabe ne daga gari da ake kira Fazzana (dake cen Cikin Croatia).

Kamar Yadda Tarihi yazo Cewa, Wannan Malamin Kafin Zuwan Shehu yaje Makkah domin yin aikin hajji daga cen kuma sai ya wuce garin Mahaifinsa Fazzana domin ya ziyarci dangin Mahaifinsa daga baya kuma sai ya dawo kasarsa borno.

Kasancewar Tafiya a wancen lokacin tana da wuya, (domin mutum yakan shekara da shekaru bai samu yaje garin da zaije ba), wannan yasa Bayan dawowarsa sai ya tarar da Daawar Shehu ta mamaye ko Ina a fadin wannan kasa ko kuma Daula a wancen lokaci. Inda Shehu da Almajiransa suka yi waazi suka shiryarda mutane zuwa ga hanyar gaskiya, wayanda kuma suka ki jin wa’azi Shehu ya yakesu (A cikin wayanda aka yaka kuwa harda Jama’are da Hadeja) da sauran wasu garuruwa  wayanda suke cikin Rikon Borno.

Wannan dalili shiyasa Muhammad Alamin Alkanemi Ya zargi jihadin Shehu Usmanu Bin Fodio Inda ya nuna Jahdin na Shehu bai dace ba (Ma’ana bai dace ya yaki wasu garuruwa ba), a cikin wayannan garuruwa da bai dace a yaka ba akwai mutanen da Borno ke riko, Dominsu Mutanen Borno da wayanda suke riko Musulmi ne.

Wannan daliline ya sanya Alkanemi ya rubuta wasika Ga Shehu yana zargin Jahadinsa, Bayan Wasikar Alkanemi ta zowa Shehu da Almajiransa, nan take Shehu ya Umurci da Muhammad Bello Dansa da ya mayarwa da Alkanemi amsar wasikarsa.

A haka Alkanemi ya rika turo wasika inda shi kuma Shehu yana sanya Bello yana maida martani. A Wannan yanayine Allah (Swt) ya karbi ran Shehu Usmanu (Allah ya jikansa da Rahama), Har bayan Mutuwar Shehu Aminu Alkanemi bai daina turo wasika bag a Sarakunan Daular Usmaniya, Inda daga karshe dai Alkanemi ya Rubutowa da Muhammad Bello wasika akan Cewa, Zaizo ya yaki Daular Usmaniyya. Kuma zai fara yakar Kano (tunda tana daga rikon Daular Usmaniyya dake da Hedkwata a Sokoto).

Bayan Samun wasikar Alkanemi Sai Sarkin Musulmi Muhammad Bello ya rubutawa da Yakubun Bauchi (Sarkin Bauchi), Akan Cewa, Ya tari Alkanami da yaki (Wanda a lokacin (Kai harma a yanzu ) Sarkin Bauchi yana karbar Umurni ne daga Sarkin Musulmi dake Sokoto).

Inda nan take Yakubun Bauchi ya shirya Rundunar yaki yaje ya tari Aminu Alkanami (Suka gwabza yaki mai yawa a tsakaninsu), daga karshe Yakubun Bauchi ya samu nasara ga Alkanami, Nan take Alkaname ya gudu, Shi kuma Yakubun Bauchi ya bishi har tsawon kwana ukku bai kama shi ba.

Wannan Dalili yasa aka Bawa YAKUBUN BAUCHI (SARKIN YAKIN YAKIN SARKIN MUSULMI MUHAMMADU BELLO), Wanda har yanzu Jikokinsa (Wayanda suke rike da Sarautar Bauchi suke, Rike da Sarautar Sarkin Yaki).

Don haka duk mai tunanin Ayi masa Sarautar Sarkin Yakin Sokoto to yanama daina wahalar da kansa domin Sarauta ce mai tarihi ba Sarauta ce ta Cuwa-cuwa ba.


Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 04-03-3019

Saturday, 24 November 2018

KUSKURE NE YARDA DA ALLURAR POLIO KO TA YELLOW FEVER

GAME DA ALLURAR POLIO KO TA ZAZZABIN SHAWARA MATSAYIN TUNANI NA DAYA DA BERAN BIRNI
********
Wata Rana Beran Birni Yaje Ziyara a wajen Beran Qauye, Sai Yace da Beran Qauyen, "Abokina amma fa kana shan wahala, kazo nan Qauye ka zauna kana cin Rogo da gyada idan ana ruwa kuma ka shige rame, kuma ramen Yazo ya cika da ruwa idan zai yiwu kazo muje Birni kaga Irin gidan da nake rayuwa a cikinsa (kaga yanda nake rayuwa mana)."

Beran Qauye Ya amince, Bayan Kwana biyu suka Kama hanya zuwa Birni. Daga isarsu sai Beran Birni yaja Beran Qauye a wani Katoton gidan bene.

Mai zai faru bayan Shiyarsu, sai Beran Birni ya kutsa kai ya shiga cikin rame, (nan Beran Qauye ya fara tunani, cewa, au yace inzo muje inga gidan da yake rayuwa a ciki amma kuma naga mun shiga rame).

Bayan shigarsu Ramen Da Dan lokaci sai Beran Birni Yace, To kaga zo mu fita mu gani ko Allah zaisa Masu gidan sun ajiye abinci India hannun mu zai kai mu ci. Anan ma Beran Qauye Ya shiga tunani amma kuma yayi shiru ya bishi suka fita daga ramen zuwa Neman abinci a cikin gidan.

Suna tafiya sai sukazo wajen wani plate Wanda aka ci abinci aka rage, sai Beran Birni yace wa Beran Qauye To Bisimillah yanzu kam ga abinci nan ya samu. Cikin mamaki Beran Qauye Ya Kalle shi tare da wasu tunane tunane a zuciyarsa amma dai yayi shiru baice komai ba, ya fara cin abincin.

Cen suna cikin Cin abincin sai suka jiyo takun kafafuwan mutane suna zuwa inda suke, cikin razani da tsoro Beran Birni Yace da Beran Qauye, Kai yi maza mu koma Rami ga masu gidanan sun dawo.

Bayan sun gudu sun buya Cen Sai Kuma Beran Birni Yace da Beran Qauye Zo mu fita ko za'a dace, Fitarsu keda wuya sai Beran Qauye Yaga An ajiye K'afar kaza a bisa wani faranti yaje haka ya dauka sai Beran Birni ya rike shi yace, dashi "Kai, Ai Mutum mugune, Kada ka dauka tarkone, KA SANI NI DUK INDA NAGA ABINCINA INDA BANA TSAMMANI TO BANA AMINCEWA DA SHI". Wannan Maganar ta Beran Birni Itace Maganar da Nake so mu sanya kwakwalenmu muyi nazari akanta.

Shin turawa Zasu Kashe Makuddan Kuddi su had'a Maganin Polio domin kawai Su taimaka mana? Wallahi A'a Sam Ba zasuyi ba.

Kaje ka karanta Qur'ani sura ta 2 (Al-Baqara) tun daga sura ta 38 har zuwa sura ta 138 Bayani take akan cewa su ba masu Qaunarmu bane.

Ni kam BANA (kamar Beran Birni) duk inda naga abincina Inda bana tsammani to Babu shakka ba zan Amince masa ba.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 24-11-2018

Sunday, 12 August 2018

SIHIRIN DA AKAYIWA ANNABI (SAWW)

A madina lokacin da yake Saura Shekaru 4  Annabi (Saww) Ya Kaura ya bar Duniya Al-amarin ya faru.

Sahabban Annabi (Saww) mutum uku suka rawaito Yadda wannan Al'amarin ya faru daga ciki akwai Nana Aisha (RTa) da Abdullahi bn Abbas (RTA) da kuma Zaidu bn Arqam (RTA).

Dukkanin Wayannan sun bada labari cewa, A watan muharram yahudawan madina, (Wato maqiya Annabi (Saww) suka hadu sukayi Wata tattaunawa (meeting) ta sirri sukayi kancewa Annabi Muhammad (Saww) fa addinin shi na karbuwa ko Ina da ko ina, Kuma gashi a baya munyi sihiri kala-kala ya shanye, munyi tsafi don kashi shi bai mutu ba.

Gashi Anyi yaqin badar bai mutu ba, anyi yaqin uhud ma bai mutu ba, Mun shirya makaqarkashiya anyi yaqin kandab amma ya tsira bai mutu ba.

A Duba bayanin Wannan Zama a Cikin Adh-dabaqatul kubra na ibn Sa'ad.

A Wannan Zaman sai sukayi matsaya akan cewa zasu je wajen wani kwararren masihirci a garin madina Mai suna LABIDU BN A'ASAM (Shi wannan Labidu balarabe ne ba yadudu bane), Ya musulunta amma musuluncin Sa na kafircine.

Bayan Sunje Sun Sami Labidu Sai suka ce yayi musu sihirin Da zai kashe Annabi (Saww) zasu bashi dukiya me yawa (dukiya Mai Nishi), suka shirya suka dauki sule uku 3 suka bashi a lokacin sule 3 kudine masu yawan gaske.

Sai Shi wannan masihirci ya nemi akawo Masa Kayan Da zai hada yayi wannan Sihiri dashi da Farko a kawo Masa tokar Zuma (Bayan an tsotse Zuma Akwai Wata tuka tuka), Sannan A Samo Masa tsarkiya kwaya guda (Wani zare Mai Kama da Jijiya Wanda ake yin jita dashi), sannan aje a Samo Masa hudar dabino namiji da Macce, Sannan a Samo Masa Allura guda Goma Sha daya, Abu na karshe Yana so a Samo Masa gashin kan Annabi (Saww).

Duk aka Samo Masa Wayannan Abubuwan Sai Gashin Annabi (Saww) Ne keda Wuya Sai aka samu Wata yarinya ko Yaro wanda yake shiga gidan Annabi (Saww) aka bukaci ta dauko matajin kan Annabi (Saww).

To da aka Sanya wannan yaro ko Yarinya ya dauko matajin Annabi (Saww) wanda yake taje kanshi, Bayan dauko matajin kai na annabi wanda ya tsufa Annabi (Saww) ya dena ma amfani dashi.

Akwai sauran dangashi daya makale jikin matajin, Da wannan gashi masihircin yasamu ya yiwa Annabi (Saww) sihiri dashi. Wannan matsafi Ya tara duk yaranshi mata suka yi ta yin tofi cikin kulli Da tsafe tsafe, daga cikin yayan nashi wata tace lallai indai har Annabin gaskiya ne To Zai bada labarin wannan sihiri Da aka Yi masa, ta fadi haka ne saboda yadda taga karfin sihirin domin sihirine Me hallaka mutum kai tsaye.

Wannan Masihircin yayi mutum mutumin Annabi (Saww) wato yayi gunkinsa Da danko, sai ya sanya gashin da aka samo na Annabi akan kayin gunkin Annabin da yayi. Yayi duk abinda zaiyi ya gama sihiri akaje can bayan gari ya samu wata tsohuwar rijiya wanda aka dena amafani Da ita, yasa aka shiga cikin rijiyar akwai wani duste cikin rijiyar Qato, aka daga wannan dutsen Akasa sihirin kasar aka danne da wannan dutsin.

To Bayan wannan Sai Annabi (Saww) ya fara rashin lafiya gashin kansa Yana zuba Haka kuma baya iya cin abinci sosai, saboda wannan Sihirin har sai da ta kaiga Annabi (Saww) yana ganin ya kwanta Da iyalinshi amma kuma ba haka bane.

Da ciwo yayi tsanani abu na na cigaba yana ramewa, sai Annabi (Saww) yayi ta addu'a yana addu'a yana neman Allah ya ya ye masa wannan ciwo.

Wata Rana Ya kwanta bacci sai yayi mafarkin mala'ika Jibril Da Mika'il su kazo daya ya zauna ta gefen damarsa daya ta gefen hagunsa sai suka Fara hira

mala'ika Mika'il Yace: Me yasamu wannan bawan Allah wato yana tambayar Jibri (AS), Sai Shi Kuma Yace Masa, Ai Anyi masa sihiri ne, sai Mika'il ya Kara tambayawa Cewa, Wayayi Masa sihirin? Sai Mala'ika Jibril Ya fadi Cewa, Labidu ne Dan A'asam, Kuma an binne sihirin ne akarkashin wata riji sunanta BI'IRI ZARWAN ( ﺏﺀﺭ ﺯﺭﻭﺍﻥ ) tana ciki Garin madina.

Wato kamar suna hirane shi kuma Annabi (Saww) yana jinsu. Suka gama suka tafi Sai Annabi (Saww) ya farka yaiwa Allah godiya, yace wa nana Aisha Allah yabani labarin abinda ke damuna kinji kinji wanene yamin sihiri ya binne a rijiya.

Nan take Anabi (Saww) Ya tura sahabbai suje wannan rijiya sukaje suka ya she rijiyar suka shiga suka daga dutsen da ya danne sihirin.

Suka ciro suka bawa Annabi (Saww) da Annabi (Saww) Yaga irin kulle kullen da ke jikin wannan mutum mutumin nashi, yaga ma sihircin ya soka Allurai goma sha dayane 11, a jikin dankon mutum mutumin.

Sai Allah ya saukarwa Annabi Da surori guda biyu wato suratul FALAQI DA NASI.

Idan Annabi (Saww) ya karanta aya daya daga suratul falaqi sai ya zare allura daya daga jikin wannan mutum mutumin nashi, sai yaji kamar ajikinsa aka cire.

Sai da Annabi (Saww) ya karanta surorin nan Masu dauke Da ayoyi goma sha daya ko wace aya in ya karanta sai ya cire allura daya har sai da yaji jikinshi ya warke yasamu lafiya.

A Duba A Cikin Sahihul bukhari Hadisi na 5763-66 har zuwa Da sittin Da shida.

Da sahihu Muslim hadisi na 2189.

Akwai Abubuwan Lura da Yawa a Cikin Wannan Hadisin Wanda ya kamata mu Yi la'akari dasu.

(1) Wannan Yana Nuna Mu'ujizar Annabi (Saww), Ga yadda aka Bayyana Sihirine Mai Girman Gaske Mai saurin Halakarwa. Amma Kuma Bai kashe Annabi (Saww) Ba.

(2) Na biyu Hadin Kai

Duk wani Abu duniya da kuke so ku aiwatar na Alkherine Kona Mugunta Sai Kun hada Kai kamar Yadda wayannan Yahudawa suka hadakansu suka tattauna.

Haka Shima Labid Sai da Taimakon 'Ya'yansa da suka hada Kai Suka You wannan mugun aiki.

(3) Na Ukku da Makusancinka Ake Hadawa Domin Ganin Bayanka.

(4) Tasirin Addu'ah Ga Dukkan wani Lamari da ya tsananta gareka.

Jamilu Sani Rarah Sokoto

Sun 12-08-2018

Saturday, 23 December 2017

AMFANI DA KANYA A MATSAYIN MAGANI BOKANCINE

AMFANI DA KANYA A MATSAYIN MAGANI BOKANCINE
********
Kwanannan Naje Qauye domin ziyara sai na taradda wani al'amari mai ban takaici wanda kusan tun daga wannan rana kullum sai na rika tunani akan wannan al'amari.


Al'amarin shine Wani audio ne ake yawo dashi, wanda wani Mutum ke bayanin Abubuwan da zasu faru a wannan shekara, Inda yace, An aiko shine Daga Saudiya, Kuma duka-duka su Ukku kawai aka aiko a duniya, sannan yace, Wannan shekarar bala’o’I da yawa zasu faru ma’ana shekara ce ta BALA’I, Sannan wannan mutumen yaci gaba da cewa, Duk wanda yasan yana yin bacci tun daga dare har safiya ta waye, to ya daina Idan bai daina ba to kuwa zai mutu matsiyaci a wannan duniya.

Wannan Mutumen ya fadi abubuwa da yawa wanda lokaci ba zai iya barni na kawo suba, Daga karshe dai ya bada magani, Inda yace, A nemi Kanya tana maganin cutukka da yawa a ciki kuwa hard a Ciwon HIV inda yayi rantsuwa cewa, Idan bata maganin HIV Allah Ubangiji yasa HIV ya zama ajalinsa (Iyazan Billahi Iyazah).

Farko dai Wannan Mutumen yayiwa Allah (swt) Qarya, Domin Cewa da yayi wannan shekara ta bala’ice to yana karyata fadin Allah (swt) ne a cikin Alqur’ani Mai girma.

Domin Al-Imamul Bukhaari ya ruwaito hadisi daga Saalim bn Abdullahi, bn Umar, daga Baban Saalim din, wato ( Abdullahi dan Umar(RA)), Yace, Manzon Allah (Saww) yace: “Mabudan Gaibu guda 5 ne, kuma babu wanda yasansu sai Allah (Swt). Sune Allah ya dunqule su a qarshen Suratu Luqman, inda yace: “Lallai ILIMIN TASHIN QIYAAMAH yana wajen Allah ne, kuma shike SAUKAR DA RUWAN SAMA, kuma YASAN ABINDA KE CIKIN MAHAIFA, kuma RAI BATASAN ME ZATA SAMUBA GOBE, KUMA WATA RAI BATASAN A WACE QASACE ZATA MACE BA, lallai Allah masanine mai bada labara” Imamu Bukhari ya ruwaito a hadithi na 4627, a babin tafsiri.

Kenan Cewa, da wannan mutum yayi, Bala’I zai faru a wayannan shekaru kamar yana cewa ne yasan abinda zai faru gobe (Wa’iyazubillahi), Kai tsaye zamuce wannan mutum ya karyata Allah da ManzonSa (Saww). Allah ya kyauta.

Cikin bayanan Wannan mutumen yayi Rantsuwa tafi a Kirya, Wanda wannan Ma fasikancine. Domin a cikin Rantsuwowin da malamai suka karkasa to kuwa yayi babba daga cikinsu.

Wannan rantsuwa itace, Al-Yaminul-Ghamus ((Rantsuwa mai halakarwa),  Wannan Rantsuwa malamai suka ce, ita ce: Rantsuwar da mutum zai yi ta akan karya domin cin hakkin wani. Saboda irin girman da wannan rantsuwar take da shi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabba a gare shi ya ke cewa "Dukkan wanda ya yanki hakkin wani mutum musulmi da rantsuwar shi to hakika Allah ya wajabta mishi wuta kuma ya haramta mishi Aljanna" Muslim ya ruwaito shi, (A’uzubillahi min zalik).

Sannan dukkan wanda ya bi wannan mutumen ya yarda da zancensa shima ya sabawa Allah (SWT) domin  Allah yana cewa "Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, wulakantacce." Suratul-Kalam, aya ta 10).

Abu na gaba ko na karshe da zamfadi da ke nuna wannan mutumen bokane shine, KANYA ba ta daga cikin itacen da aka fada a cikin Al’qur’ani mai girma da Hadisan Ma’aiki (Saww), Ku lura bawai ina cewa tunda bata cikin Alqur’ani da Hadisai ba ba ina nufin bata magani bane A’a bahaka nake nufi ba

Shi wannan mutumen ya fadi cewa, KANYA ita kadaice Itacen da ta dade a duniya domin tun rowan Duhana Ma’ana zamanin Annabin Farkon Annabi Nuhu (Alaihis Salam)  take, Itace kai bata mutu ba.

Kai tsaye Wannan Karyane domin Kuwa, tunda babu shi a Alqur’ani da Hadisi to A ina ya samo haka? Ni dai nasan Jerin Itacen da suka zo a alqur’ani da Hadisai In ganttatu In shaaa Allahu zan samu Lokaci In kawo su kamar yadda Imamu IBN Khathir ya tattarosu a cikin littafinsa.

Abu na biyu da ke nuna wannan Mutum Boka ne shine, Yace, Ba’a dibar wannan Itace sai Ranar LITANIN (monday), to meye matsalar sauran ranakkun? Babu shakka wannan ire-iren sharuddan da Aljannu ke gin da yawa mutane masu huldayya dasu ne don haka muyi hattara.

Idan mutum ya ci gaba da amfani da Ire-iren wayannan Sharudda babu shakka ya Janyo ALJANNU su rika hulta da shine babu kakkautawa. Allah ya tsare mu. Don haka mu kula.

Please A turawa ‘yan Uwa domin Suyi HATTARA Domin Amfani da Ita Aikin Bokayene.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 23/12/2017

Monday, 2 October 2017

SHIN A MALIYA (THE RED SEA) NE FIR’AUNA YA NUSTE? Fitowa ta farko



SHIN A MALIYA (THE RED SEA) NE FIR’AUNA YA NUSTE? Fitowa ta farko
******
Larabawa kan kira wannan teku da Bahar al-Ahmar Idan aka fassara zuwa Hausa kuwa sai a kira shi da (Bahar Maliya), Turawa kuma sukan kira wannan teku da “Red sea” wato jar teku. Kafin Jin shin ko anan ne Fi’auna ya nutse akwai bukatar Sanin Tarihin wannan teku kadan (Da yake wannan Teku na daga cikin tekunan duniya masu ban mamaki da marubuta da Masana Ilimin Kimiyya da yawa sukayi rubutu kan ta).
Turawa sun kira wannan wuri da Jar teku saboda yanayin jaja-jaja na tsaunukan da suke wannan wuri da ake kira Bahar-maliya.

Wani shahararren marubuci da ake kira da suna Mr E.M.Foster,ya bayyana cewa,tun tale-tale matafiya da yan safara wadanda suke ratsawa ta wannan teku, suka sa mata wannan suna “Red sea” ko kuma “Bahar-ahmar’’.

Wannan ruwa sune marraraba tsakanin yankin Afrika da kuma yankin Asiya. Ruwan wannan teku suna da tsawon kilomita 2000 sannan fadinsu ya kai kimanin kilomita 300. Zurfin su kuwa ya kai mita 2.500.

wayannan Ruwan suna iyaka da kasashe Takwas, wanda suka hada da kasashe hudu na Afrika, Masar, Eritrea,Jibuti, da Sudan,sai kuma ksashe hudu na yankin, Asiya Saudiya, Yamen, Israila da kuma Jordan.
Anyi ta muhawara akan wai me yasa ake kiran wannan teku da “Jar teku” Inda Wasu daga cikin marubutan kasar Birtaniya, da sukayi rubuce rubuce kan wannan Tekun sun tafi akan cewa, wannan suna na “Red sea’’ da Turawa suke kiran tekun Bahar maliya da shi, ba saboda yanayin jaja-jaja na tsaunuka bane, a’a, sakamakon yawan gamsakuka da take kewaye da gabar tekun wanda idan rana ta haska sai ta mai da tekun ta rinka daukar launin jaja-jaja ruwan dorawa-dorawa, da wasu kaloli daban wannan shine dalilin dayasa ake kiran ta da suna “Red sea’’ wato Jar-teku a hausance.

Masana ilimin kimiyya kuwa, sakamakon nazarin da wasu likitoci da kuma masana ilimin tarihi da halittun cikin ruwa suka gudanar,a shekarar 1646. Wani shahararren likita kuma marubucin litattafan turanci da ake kira da suna Sir Thomas Brown ne ya bayyana a cikin littafinsa cewa, wani masani akan halittun Ruwan-teku da ake kira da suna Sir Walter Raleigh, ya na kan ra’ayin cewa, Bahar maliya dai teku ce da take da launuka daban-daban, ya danganta da bangaren da mutum ya ke kallonta.

Sir Raleigh ya ci gabada bayyana cewa nazarin da yayi game da tekun baharmaliya ya tabbatar masa da cewar wannan teku tana da launuka daban-daban. Wani bangaren kore ne fatau,wani bangaren kuma zaka ganshi fari ne da ruwan dorawa-dorawa, wani gurimma ka gan shi shudi-shudi. Saboda haka kalar kowanne bangare na tekun ta dangantane da yanayin yashi ko kuma lakar da take acan kar kashin kasa.

Sai dai kuma har wa yau daya daga cikin malaman kimiyya kuma shahararren marubuci Carl Drews dan kasar Amerika shi ya musanta wancen zancen na Sir Thomas Brown Inda ya bayyana a cikin littafensa mai suna “Between Migdol and the Sea: Crossing the Red Sea with Faith and Science”, cewa, “ A’a, ruwan tekun maliya ba ja ba ne”. haka kuma ya musanya zance da wasu masana Ilmin Teku da Malaman Tarihi suka bayyana na cewa, A nan ne Allah (SWT) Ya halakar da Fir’auna da Jama’arsa lokacin da suka biyo Annabi Musa (AS).

In shaa Allahu Zan Dakata anan Sai mun hadu a Rubutu na Gaba da Iznin Allah.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
02/10/2017


Monday, 3 July 2017

TARIHIN IMAMU ABU HANIFAH

TARIHIN IMAMU ABU HANIFAH
******

"Idan Karya Nakeyi To bayani na ya tabbata taya zaka dauki Matsayi na Alkalin Alkalai Ka bawa makaryaci?" Inji IMAMU ABU HANIFAH.

An Haifi Imamu Abu Hanifa a Cikin Birnin Kufa dake kasar Iraq a lokacin mulkin Kaliphancin Umayyad wato Abd al-Malik ibn Marwan. Mahaifinsa Dan kasuwane daga Kabul dake Afghanistan, mahaifin Imamu Abu Hanifa nada Shekara 40 a duniya aka haifeshi.

Asalin sunan sa An-Nu’uman bin Thabit, At-Taimi,  Abu Hanifa Na daga Cikin Manyam Malamai na farko farko da suka yiwa Musulunchi Hikima Bayan Sahabban Manzon Allah (Sallalahu ALaihi Wa'alihi Wasallam), Imamu Abu Hanifa ya rayayi rayuwa  kamar da Sahabbain Annabi (Sallalahu ALaihi Wa'alihi Wasallam), guda 4 daga cikinsu Akwai Anas Bin Malik, Jabir ibn Abd-Allah da kuma Sahl ibn Sa'd (RA).

An haifi Abu Hanifa Shekara 67 bayan Wafatin Annabi (Sallalahu ALaihi Wa'alihi Wasallam). Kuma Allah ya bashi basira tun yana yaro karami. Har an ruwaito Cewa, Watarana acikin garin Baghdad akwai wani babban kafiri wanda bai yarda da tauheedi ba, kuma bai yarda da cewa akwai Allah ba.
Har ma ya kirkiri wasu tambayoyi yana ta neman wanda zai amsa masa su. Duk Malaman garin sun kyaleshi basu daukeshi da muhimmanci ba.

Alokacin nan Imam Abu Hanifah (rah) yana yaro karami kwata-kwata bai fi shekara goma ba. Watarana yazo wucewa sai yaji mutumin nan yana da Ikirarin cewa wai Musulmai sun kasa amsa tambayoyinsa. Sai Imam Abu Hanifah ya matsa kusa dashi yace masa “In sha Allahu ni zan amsa tambayoyin naka komai wahalarsu”. Mutumin ya amsa gayyatar, Kuma Jama’a suka cika da mamaki. Ta yaya wannan ‘dan Qaramin yaro zai iya jayayya da Kafirin nan wanda manyan Maluma suka kasa ja dashi!

Da ranar Mukabalar tazo sai Jama’ar garin gaba daya suka taru a wani fili a tsakiyar garin Baghdad wanda dama anan ake gabatar da duk wani Muhimmin taro. Sai shi wannan kafirin ya hau kan tudun dake tsakiyar taro. Sannan ya bude muryarsa ya jefo tambayarsa ta farko zuwa ga Abu Hanifah; “Shin menene Allahn naku yake yi dai-dai yanzu? Abu Hanifah ya tsaya yayi tunani na ‘yan mintuna kadan, sai yace ma mutumin “To ina so kai ka sauko kasa, ni kuma in hau sama sannan in baka amsarka”. 

Wannan yaro karamin yaro ‘dan shekara goma (wato Imam Abu Hanifah) ya hau saman kan tudun sannan yace “Ya Allah kaine shaida gareni agaban duk wadannan Mutanen cewar na shaida lallai yanzun nan kai ka Qaddara saukowar wannan kafiri zuwa Qasa, kuma ka Qaddara cewar Mumini zai hau sama (wato zai daukaka akansa)”.

Da Mutane (‘yan kallo) suka ji wannan amsar ta fito cikin fasaha daga bakin Abu Hanifah, sai suka fara kabbara “Allahu Akbar!” Allahu Akbar!” Tun daga nan kafirin nan ya fara ganin kaskanci.
Amma sai ya sake jefowa tambayarsa ta biyu “Shin meke raye kafin Allahn naku?” (Subhanallah). Imam Abu Hanifah (rah) yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace ma kafirin ya Qidaya masa lambobi daga goma zuwa Qasa Sai kafirin ya fara “Goma, tara, takwas, bakwai, shida, biyar, hudu, uku, biyu, daya, sufiri” Sai Imamu Abu Hanifa yace masa “Shin me ka gani bayan sufiri (wato zero)?”

Mutumin yace “Babu komai kafinsa, ni ban sani ba”. Da jin haka sai Imam yayi murmushi yace masa “To gashi nan ka riga ka bawa kanka amsa...Hakika Allah shine rayayye kuma dawwamamme. Babu kowa kuma babu komai kafinsa”. Daga wannan sai waje ya rude da kabbara, suna Qara jinjina ma Imam Abu Hanifah (rah). Kafirin nan zuciyarsa ta harzuka, ransa ya baci. Sai ya jefo tambayarsa ta Qarshe “SHIN YANZU WAJEN INA (WACCE KUSURWA) ALLAHN NAKU YAKE KALLO?” (Shin gabas yake kallo ko yamma ko kudu ko Arewa?). Imam Abu Hanifah bayan yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace a kawo masa Fitila (Aci-balbal ko kuma kyandir). Da aka kawo masa sai ya damka wa kafirin nan. Yace masa ya kunna masa, Bayan kafirin ya kunna kyandir din sai ya tambayi Imam Abu Hanifa , to menene dalikin haka? Sai Imam Abu Hanifah yace masa “Shin wanne waje ne wutar hasken kyandir din nan take kallo?” Sai kafirin yace, “Tana kallon dukkan kuskuwoyi ne. (wato gabas, yamma, kudu, arewa, sama da Qasa) Babu inda bata kallo” Sai Imamu Abu Hanifa yace masa “Ai ka riga ka amsa tambayarka. Hakika Hasken Allah ya mamaye ko ina. Yana nan ako ina, babu wajen da babu shi”.

Daga nan sai mutane suka rude da kabbarori “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!”. Shi kansa wannan kafirin yayi mamakin ilimi da basirar Imamu Abu Hanifa (RA). Don haka anan wajen ya furta kalmar Shahada, ya zama Musulmi kuma ya zama Almajirin Imam Abu Hanifah (ra).

Imam Abu Hanifah yana daga cikin mutane mafiya kaifin hankali da basira daga cikin Maluman wannan al'ummar ta Musulunci. Watarana barayi sun shiga gidan wani mutum suka yashe masa dukiyarsa baki 'daya, sannan suka sanyashi ya rantse akan cewa ba zai tona musu asiri ba. Idan kuma ya tona asirinsu to Matarsa ta saku, Saki uku!! Wannan mutum ya wayi gari cikin tsananin bakin ciki. yana kallon mutanen nan suna ta sayar da kayansa da suka sato, amma bashi da damar yace komai, tunda ya riga ya rantse idan ya fallashesu to matarsa ta saku saki uku!! Saboda haka sai yaje ya gaya ma Imam Abu Hanifah halin da yake ciki. Sai yayi Murmushi yace masa "Na san hanyar da zamu bi, kayanka zai dawo ba tare da kace komai ba". Sai Imam Abu Hanifah yasa aka tara masa dukkan Limamai da ladanai na garin, sannan yace musu "Wannan mutumin anyi masa sata ne. amma shin kuna so dukkan kayansa ya dawo gareshi?". Suka ce "Eh". Sai yace to ina so ku tattaro min duk mutanen da aka ta'ba tuhumarsu da sata a unguwanninku.

Da aka tattarosu sai yasa aka kira masa Jami'an tsaro, yace musu ga wasu mutane nan zan rika tambayar wannan mutumin game dasu. Duk wanda kuka ji wannan mutumin yayi shuru bai ce komai akansa ba, to 'barawo ne. ku kamashi. Sai Imam Abu Hanifah yasa aka rika fitowa da mutanen nan 'daya bayan 'daya. Yana tambayar mutumin nan "SHIN WANNAN NE BARAWONKA?". Sai mutumin yace "A'a ba shi bane". Sai ace wannan ya wuce. Amma idan aka tambayeshi "SHIN WANNAN NE BARAWONKA? " in aka ji yayi shuru bai ce komai ba, sai Imam Abu yace "KU KAMA WANNAN SHIMA BARAWO NE".

Da haka sai da aka kama dukkan barayin nan ba tare da mai dukiyar ya ambaci sunayensu ba.
Allah Mai kyauta da karawa kamar Yadda Imamu Abu Hanifa Yake da kaifin basira haka Allah ya Azzurtashi da 'ya mai kaifin Basira. Abu Hanifa ya kasance yana karba tambayoyi tare da bada fatawowi hadi da karantarda dalibban Ilmi.

Wata Rana Sai aka yi masa wata tambaya wacce ta daure masa kai, tambayar kuwa itace; "ME YASA A MUSULUNCE SU MATA BA'A BASU DA DAMAR AUREN MAZA FIYE DA DAYA BA, ALHALI SU MAZA NA AUREN MACCE HAR UKKU?" Wannan tambayar ta daurewa Imam Abu Hanifa kai sosai da Sosai, Cen 'yarsa da ke Zaune Kusansa (wato Hanifa), Sai tace, "Ya Babana ai zan iya karba wannan tambaya Idan har ka amincemin."

Abu Hanifa Ya amince mata akan ta bada amsar wannan tambaya in har ta san amsa. Hanifa ta sa aka tara mata 4 ta bukaci a kawo katon masaki cike da nono, bayan an kawo wannan masaki, Sai tabawa kowace macce kofi daya tace kowacce ta debo wannan Nono dake cikin wannan Masaki. Bayan kowacen su ta debo (Wannan Nonon), Sai tace, dukansu su mayarda nonon a ciki. Dukansu suka sake mayarda nonon da suka diba. Sai Hanifa tace, "To kowaccen ku ta debo Nonon da ta zuba a cikin Wannan masaki, ba tare da ta debo wanda bata zuba ba."

Dukansu sai suka ce, "Taya zamu iya debo nonon da muka zuba kuwa? Alhali nonon ya hade?"
Sai Hanifa Tace, "To kamar hakane, Idan macce ta auri maza biyu ko ukku ko hudu, aka haihu ba za'a iya gano waye mahaifin jarinrin ba." Wannan Amsa ta Sanya Numan bin Thabit (Abu Hanifa) farin Ciki, daga nan sai aka rika kiransa da sunan (Baban Hanifa).

A shekarar 763, Imamu Abu Hanifa ya samu takardar Bukatar yayi Jagorancin alkalin Alkallai daga Al-Mansur a zamanin Kaliph Harun al-Rashid. Lokacin da Wannan takarda ta sami Abu Hanifa sai ya Rubutawa Al-Mansur Cewa, "Hakika ni Ban cencancan ci Zama kan wannan Mukamin ba abawa wani." Lokacin da Sako ya Zowa Sarki Al-Mansur sai ta yasa aka kira masa Imamu Abu Hanifa Yace Masa Me yasa ba zaka Amsa ba? Abu Hanifa Yace, Ban Cen-centa bane kawai.

Al-mansur Ransa ya bace Yace, "Hakika Karya Kake yi domin ka cen-centa." Sai Imamu Abu Hanifa Ya buda baki yace, "Babu Shakka bayani na ya tabbata (ban Cen-centa ba), taya zaka dauki Matsayi na Alkalin Alkalai Ka bawa makaryaci?" Wannan amsar ta Abu Hanifa Ita ta harzuka wannan Sarkin nan take ya sa aka kama Imamu Abu Hanifa aka Rufeshi a Gidan kaso (Prison) aka Rika azabantar dashi azaba kala-kala a gidan yarin. 

Duk da Irin Azabar da Imamu Abu Hanifah yake sha masana tarihi sun tabbatarda ci gaba kawai yayi da karantarwa da yin Kira zuwa a kadaita Allah a Cikin Wannan Gidan kaso. A karshe dai wasu malaman tarihi sun bayyana a gidan yarin Allah ya karbi ransa.
Masana tarihi suka ce kusan mutum dubu hamshin (50,000), ne suka halarci zana'Izarsa a lokacin da Allah Yayi Masa Cikawa.

Daga cikin littafan da ya wallafa akwai, Fiqh al-Akbar; Fiqh al-Abasat Kitaab-ul-Aathaar, Kitabul Aathaar, Musnad Imaam ul A'zam, da kuma Kitaabul Rad alal Qaadiriyah. Imam Abu Hanifa ya hardace hadisai masu yawan gaske har an ruwaito wani daga cikin magabata na cewa, Imamu Abu Hanifah ba ya rawaito hadisi sai wanda ya haddace, ba ya rawaito hadisin da be haddace ba. Imam Abu Hanifa ya rasu a shekarata (150A.H).

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Mon 17-04-2017