Tuesday, 13 August 2019

KA TABA SALLAR GAWA?

Mutane da Yawa Sukanyi Sallar Janaiza (Sallar Gawa), Amma Kuma Basu San ya ake yin wannan Sallah ba (Ma'ana Basu San me ake fada a Sallar ba), ko Kuma Basu San hukunce hukuncen ta ba.

Da farko Ya Halatta Idan Liman yayi Niyar yin Sallar Gawa yayi Kabbara Hudu, Biyar, Shidda, Bakwai ko Kuma Tara, a Lokacin Sallar Gawa, Sannan ya sallame, domin duka An samu wannan dalilai daga Sahabban Annabi (Saww) Sunyi hakan.

Kabbara Hudu, Sayyidina Abu Huraira (RTA) Yace, " Lokacinda labarin rasuwar Najashi (Sarkin Habasha) ya zowa Annabi (Saww), A wannan Rana sai Annabi (Saww) Ya fita da mu a Wani wuri da ake yin sallah, mukayi sahu Annabi (Saww) yayi Mana Sallar Janaiza Yana Mai yin Kabbara hudu.
(Sahih Al-Bukhari, littafe na 2, shafi na 227, Hadith na 404; ko Kuma Sahih Muslim, littafe ba 2, shafi na 452, Hadith na 2077).
Kabbara Biyar, Abdurrahman Ibn Abi Laylah (RTA) yace, Zayd Dan Arqam ya kasance Yana Yana yin kabbarori Hudu Idan Dayan mu ya rasu, wata Rana sai ya yi raka'a Biyar sai muka tambayeshi Dalilin yin Haka, sai Yace, Ma'aikin Allah (tsira da amincin Allah Su tabbata a gareshi) ya kanyi Haka.[
(Sahih Muslim, littafe na. 2, shafina 453 Zuwa 454, Hadith na 2089).
Kabbara Shidda, Abdul Khayr Yace, Ali Ibn Abi Talib Ya kasance Yana yin Kabbarori Shidda (Idan Yana Bada Sallar Gawa), ga wayanda suka halarci yakin Badar, Kabbarori Biyar ga sauran Sahabban Annabi (Saww) da Basu halarci yakin ba, Sannan Yana yin Kabbarori Hudu ga gama GARIN Al'umma.
(Imamu Al-Bayhaqi da Ad-Daraqutni suka fitar dashi hadisi ne Mai kyau a duba a Cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi na 113).
Kabbarori Bakwai, Musa Dan Abdullahi Dan Yazid yace, Sayyidina Aliyu ya yi Kabbarori guda Bakwai a lokacin da Yake sallatar gawar Qatadah, (Kuma Qatadah ya kasance daga Cikin wayanda suka halarci yakin Badar).
( Imamu Bayhaqi ya fitar dashi Kuma hadisi ne Mai kyau a duba a Cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi na 113 Zuwa 4).
Kabbarori Tara, Abdullahi Ibn Az Zubar ya ruwaito Cewa, Annabi (Saww), ya sallaci gawar Sayyidina Hamza Yana mai yin Kabbarori guda Tara.
(At-Tahawi da kuma At-Tabarani suka fitarda shi hadisi ne Mai kyau a duba a cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi na 114).
Ya Halatta Mutum ya daga hannayensa Biyu idan zaiyi Kabbara a kowace Kabbara ko Kuma Mutum ya daga hannayen a kabbarar farko kawai kowane Mutum yayi daidai ne.
(A duba a Sahih Al-Bukhari, littafe na 2, shafi na 228, 55).
Ana son Mutum ya karanta suratul fatiha da sauri a kabbarar farko.
(Sahih Bukhari, littafe na 2,  shafi na 236, Hadith na 419;  ko Kuma Sahih Al-Bukhari, littafe na 1, shafi na 397, Hadith na 710; Sahih Muslim, littafe na 1, shafi na 219, Hadith na 786).
A Kabbara ta Biyu Ana so ayi sauri ayiwa Annabi (Saww) Salati, duk salatin da Mutum yayi Amma salatin Ibrahimiyya Shine Wanda aka fiso a Yi domin shine salatin da ya zo a ingantattun hadisai.
A Kabbara ta ukku Ana so ne ayiwa Mamaci Addu'ar Samun Rahama, Tunda sallat anayinta ne ga Mamaci Ana so ayi Masa Addu'ah a Kabbara ta ukku, zuwa ta Hudu ko ta Biyar Zuwa Tara domin nema Masa rahamar Allah. (Abu Dawud, 2, shafi na 616-7, 2740).
Sallamewa, Akwai hanyoyi Biyu da Sunna ta amince A sallame Sallar kamar yadda Baihaqi da Tabaranj suka ruwaito a Cikin Ahkam al-Jana'iz, shafi ba 127, #83).
1. Ko dai Mutum yayi sallama daya kawai ta hanyar sallamewa a Bangaren Dama. Kamar yanda Hadisin Abu Huraira (RTA) ya nuna.
2. Ko Kuma Mutum ya sallame a duka bangarori Biyu (Dama da hagu) kamar yanda yazo a Hadisin Ibn Mas'ud.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tue 13-08-219

UNGUZOMA (MIDWIVES)

UNGOZOMA (MIDWIFE) BAIWAR ALLAH

Wasu suna ganin kalmar Ungozoma ta samo asali ne daga "ungo-tsoma ".Wai don Idan mace ta yanke cibin jariri, kuma mabiyya (mahaifa) ta fado, to sai a dauko ta fito da ita waje ta mika wa masu taimaka mata, ta ce da su "Ungo-tsoma " A cikin masaki mai cike da ruwa. Wai ta haka ne sabida yawan fadar kalmar "Ungo-tsoma ". Sai ta koma Ungotsoma. "Ungozoma ".

A Al'adar Hausawa Ungozoma ta na da muhimmanci kwarai da gaske, domin kuwa kusan kowanne Kauye ko Gari ko Unguwa Inda jama'a su ke zaune akwai Ungozoma, kamar dai yadda ake samun Ruwa don bukatar rayuwa.

Saboda sanin muhimmancin Ungozoma a al'umar Hausawa har kirari su ke mata da cewa " Ungozoma kin fi mai da son da ". Haka har cikin Karin magana an ambaci Ungozoma, misali : "Komai saurin Ungozoma ta jira a haihu ".da kuma "Ai ba a Kare haihuwa ba wai an baiwa Ungozoma tuwan suna a hannu". Dasauransu. wannan shi zai Kara tabbatarma da muhimmamchin Wannan Mata a Cikin al'umma.

Akwai ire-iren Ungozoma guda biyar. (5times) a kasar Hausa kamar haka :

1-Ungozomar Gado, Wasu Gidajen Attajirai Sukan Ajiye Ungozoma wacce duk matarda zata haihu Gidan itace zata Kula da wannan matar tun daga rainon Cikin har Zuwa Haihuwa Itace zata Rika Kula da matar.

2-Ungozomar Sana'a, Akan Samu Wasu Masu Aikin Karbar Nakuda (Ungozoma), wacce Ita Zaman Kuddi take, 'yan Unguwa sun San da zamanta, Duk Gidan da za'a haihu akan Kira Irin wannan matar a sanyata ta karbi bikin Idan an haihu sai a biyata ladan aikinta.

3-Ungozomar Dangi, Kamar Gidan Attajirai Haka A Dangi Idan an samu Macce wacce ta iya Karbar haihuwar to Tana iya Zama ta Dangi, duk wani wata 'yar uwa ko matar Dan uwa da zata haihu akan je anemo ta ta karbi haihuwar.

4-Ungozomar Masarauta, Duk Gidan sarauta akan samu Mai Karbar biki na matar Sarki ko Kuma 'ya'yan Sarki ko Kuma Matan 'ya'yan Sarki Dasauransu.

Ayyukan Ungozoma suna da yawa ga kadan daga ciki:

Akwai aikace -aikace da dama da Ungozoma ke gudanarwa kafin haihuwa, da kuma lokacin haihuwa, da bayan an haihuwa.

Sanin Lafiyar Abin da ke Ciki Tun kafin lokacin haihuwa Ungozoma takan je ta duba lafiyar jariri ,misali kwanciyarsa a ciki, motsinsa Dasauransu. Ta hanyar sunkuyawa ta kara kunnwanta kan cibiyar mai ciki, ta yadda Idan ta ji matsala ta gyara mata ta hanyar mulmula cikin a hankali da kuma yin amfani da wani dan karamin Koko wajan gyara Shi ta yadda lokacin haihuwa zai fito cikin sauki salamun -salamun.

Kula da mai Ciki Wani muhimmin aikin Ungozoma za taita kula da mai ciki wajan hanata yin wasu abubuwa ko sata ko hanata shan abu mai daci, da kuma bata magungunan rage Zaki, da kuma samun Karin karfin jiki a lokacin Nakuda.

Gyaran dakin Mai Ciki
Yanayin gyaran dakin mai ciki iri biyu ne kafin haihuwa da kuma bayan haihuwar. Ungozoma takan kawar da kayan dakin mai haihuwa gefe guda dan ta sami sararin da za ta haihu.

Gyaran daki na biyu Shi ne bayan an haihuwa Ungozoma zata gyara dakin tsaf ta maida Shi yadda yake.

Karbar Haihuwa  Dazarar anga Nakuda ta kankama, haihuwa ta doso gadan -gadan sai Ungozoma da dangi masu taimaka wa mai haihuwa su shiga shiri Karbar haihuwar.

Ayyukan Ungozoma suna da yawa kamar bata taimako na abinda za ta sha lokacin Nakuda yankan cibi dss. Amma konan muka tsaya Ina ga za mu iya fahimtar Wacece Ungozoma da kuma Ire-irenta da Irin gudunmawar ta ga mai ciki da kuma abin haihuwa (Jariri).

Babu Shakka Babu Wani mutum a Duniyar Nan da Ungozoma Bata Yi Masa Rana ba.

Jinjina Ga Ungozoma (Midwives).

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tue 06-08-2019