Saturday, 23 December 2017

AMFANI DA KANYA A MATSAYIN MAGANI BOKANCINE

AMFANI DA KANYA A MATSAYIN MAGANI BOKANCINE
********
Kwanannan Naje Qauye domin ziyara sai na taradda wani al'amari mai ban takaici wanda kusan tun daga wannan rana kullum sai na rika tunani akan wannan al'amari.


Al'amarin shine Wani audio ne ake yawo dashi, wanda wani Mutum ke bayanin Abubuwan da zasu faru a wannan shekara, Inda yace, An aiko shine Daga Saudiya, Kuma duka-duka su Ukku kawai aka aiko a duniya, sannan yace, Wannan shekarar bala’o’I da yawa zasu faru ma’ana shekara ce ta BALA’I, Sannan wannan mutumen yaci gaba da cewa, Duk wanda yasan yana yin bacci tun daga dare har safiya ta waye, to ya daina Idan bai daina ba to kuwa zai mutu matsiyaci a wannan duniya.

Wannan Mutumen ya fadi abubuwa da yawa wanda lokaci ba zai iya barni na kawo suba, Daga karshe dai ya bada magani, Inda yace, A nemi Kanya tana maganin cutukka da yawa a ciki kuwa hard a Ciwon HIV inda yayi rantsuwa cewa, Idan bata maganin HIV Allah Ubangiji yasa HIV ya zama ajalinsa (Iyazan Billahi Iyazah).

Farko dai Wannan Mutumen yayiwa Allah (swt) Qarya, Domin Cewa da yayi wannan shekara ta bala’ice to yana karyata fadin Allah (swt) ne a cikin Alqur’ani Mai girma.

Domin Al-Imamul Bukhaari ya ruwaito hadisi daga Saalim bn Abdullahi, bn Umar, daga Baban Saalim din, wato ( Abdullahi dan Umar(RA)), Yace, Manzon Allah (Saww) yace: “Mabudan Gaibu guda 5 ne, kuma babu wanda yasansu sai Allah (Swt). Sune Allah ya dunqule su a qarshen Suratu Luqman, inda yace: “Lallai ILIMIN TASHIN QIYAAMAH yana wajen Allah ne, kuma shike SAUKAR DA RUWAN SAMA, kuma YASAN ABINDA KE CIKIN MAHAIFA, kuma RAI BATASAN ME ZATA SAMUBA GOBE, KUMA WATA RAI BATASAN A WACE QASACE ZATA MACE BA, lallai Allah masanine mai bada labara” Imamu Bukhari ya ruwaito a hadithi na 4627, a babin tafsiri.

Kenan Cewa, da wannan mutum yayi, Bala’I zai faru a wayannan shekaru kamar yana cewa ne yasan abinda zai faru gobe (Wa’iyazubillahi), Kai tsaye zamuce wannan mutum ya karyata Allah da ManzonSa (Saww). Allah ya kyauta.

Cikin bayanan Wannan mutumen yayi Rantsuwa tafi a Kirya, Wanda wannan Ma fasikancine. Domin a cikin Rantsuwowin da malamai suka karkasa to kuwa yayi babba daga cikinsu.

Wannan rantsuwa itace, Al-Yaminul-Ghamus ((Rantsuwa mai halakarwa),  Wannan Rantsuwa malamai suka ce, ita ce: Rantsuwar da mutum zai yi ta akan karya domin cin hakkin wani. Saboda irin girman da wannan rantsuwar take da shi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabba a gare shi ya ke cewa "Dukkan wanda ya yanki hakkin wani mutum musulmi da rantsuwar shi to hakika Allah ya wajabta mishi wuta kuma ya haramta mishi Aljanna" Muslim ya ruwaito shi, (A’uzubillahi min zalik).

Sannan dukkan wanda ya bi wannan mutumen ya yarda da zancensa shima ya sabawa Allah (SWT) domin  Allah yana cewa "Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, wulakantacce." Suratul-Kalam, aya ta 10).

Abu na gaba ko na karshe da zamfadi da ke nuna wannan mutumen bokane shine, KANYA ba ta daga cikin itacen da aka fada a cikin Al’qur’ani mai girma da Hadisan Ma’aiki (Saww), Ku lura bawai ina cewa tunda bata cikin Alqur’ani da Hadisai ba ba ina nufin bata magani bane A’a bahaka nake nufi ba

Shi wannan mutumen ya fadi cewa, KANYA ita kadaice Itacen da ta dade a duniya domin tun rowan Duhana Ma’ana zamanin Annabin Farkon Annabi Nuhu (Alaihis Salam)  take, Itace kai bata mutu ba.

Kai tsaye Wannan Karyane domin Kuwa, tunda babu shi a Alqur’ani da Hadisi to A ina ya samo haka? Ni dai nasan Jerin Itacen da suka zo a alqur’ani da Hadisai In ganttatu In shaaa Allahu zan samu Lokaci In kawo su kamar yadda Imamu IBN Khathir ya tattarosu a cikin littafinsa.

Abu na biyu da ke nuna wannan Mutum Boka ne shine, Yace, Ba’a dibar wannan Itace sai Ranar LITANIN (monday), to meye matsalar sauran ranakkun? Babu shakka wannan ire-iren sharuddan da Aljannu ke gin da yawa mutane masu huldayya dasu ne don haka muyi hattara.

Idan mutum ya ci gaba da amfani da Ire-iren wayannan Sharudda babu shakka ya Janyo ALJANNU su rika hulta da shine babu kakkautawa. Allah ya tsare mu. Don haka mu kula.

Please A turawa ‘yan Uwa domin Suyi HATTARA Domin Amfani da Ita Aikin Bokayene.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 23/12/2017

9 comments:

  1. Allah yasaka da alheri yakara shiryamu

    ReplyDelete
  2. Shidai ilimi fadi gareshi kowa akwai gwargwadon abinda ALLAH ya bashi ikon sani ko addinance akwai lokutan da aka ware da ranaku don neman biyan bukata. Haka kuma masu ilimin taurari sukan fadi abinda zai kasance a wasu lokutan damina da yanayin zafi ko sanyi ko lokacin da za'ayi ruwa ko zazzabin wata ko rana. Haka kuma likitoci suna ware lokacin da za'a sha magani. Shi tsaida rana ko lokaci don gabatar da wani al'amari na rayuwa ko magani ko addu'a don neman biyan bukata ba laifi bane kuma ba nuna sanin gaibu bane kuma ba bokanci bane.

    ReplyDelete
  3. Shin nufin bugaruwa nkas shi ne kanta?

    ReplyDelete
  4. Masha Allah wannan it a ce fahimta madaidaiciya gaskiyar lamari
    Nafiu Rabiu kano

    ReplyDelete
  5. malam ka tambayi mlamin yayi maka bayani tun da kai iliminka bai zoba amma kana karyata mutun kuma kai baka sani ba bakayi bayani ba to meka kake mudai amfani da sauran itatuwan da abaa ambacesu a alqur ani ba kuma kayi amfani da kanyar bata yi makabane kake hassada kai baka fasda kuma amfada ka ce kar ayi Allah ya rabamu da hassada mu muna amfani da ita kuma muna ganin maganin to meye bokanci a ciki shan ko turaran .

    ReplyDelete