KUYI HANKALI DA 'YAN DAMFARA
******
A Ranar 07 ga watan Mayun Shekarar 2014 Jaridar Khaleej Times ta k'asar Dubai ta Ruwaito Labarin Wata Makekiyar damfara da aka yiwa Wata Mata 'yar k'asar Dubai Dirham miliyan hudu, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 160 a kuddin Nageriya.
******
A Ranar 07 ga watan Mayun Shekarar 2014 Jaridar Khaleej Times ta k'asar Dubai ta Ruwaito Labarin Wata Makekiyar damfara da aka yiwa Wata Mata 'yar k'asar Dubai Dirham miliyan hudu, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 160 a kuddin Nageriya.
An damfari wannan matar ne don a cire wa ’yarta aljanin da
ya hana ta aure. Jaridar ta Ruwaito Cewa, Al’amarin ya samo asali ne a
lokacin da matar ta shiga damuwa, ganin cewa tsararrakin ’yarta sun yi
aure, amma ita 'yarta ko labari babu. Da ta shiga tunanin yadda za ta aurar da ’yarta, sai kawar
yarinyar ta nuna mata cewa akwai wata amtsala a cikin al’amarin ’yarta, inda ta nuna mata cewa aljani ne ya aure ta. Ita kuwa jin haka, sai ta
yarda. Daga nan sai aka nuna mata cewa za a samo mata maganin aljanin da
ya hana ’yarta aure.
Bayan kwanaki kadan, sai aka bayyana mata cewa aljanin da
ya auri ’yarta yana da tsananin kishi, don haka ba zai kyale kowa ya
aure ta ba. Kuma shi yake korar duk wanda ya nuna yana son ’yarta.
An dai cusa wa matar ra’ayin ta tuntubi wata bokanya, wadda
ta bukaci ta ba Dirhami miliyan guda wato daidai da Naira miliyan 40.
Wannan bokanya, sai ta kara da cewa abin wuyanta ma aljani ya kama shi.
Don haka aka ce ta bayar da abin wuyan, wanda kimarsa ta kai Dirham dubu
700.
Bayan da ta aikata abubuwan da aka bukaci ta yi, sai kuma
bokanya ta bukaci ta biya wasu dirhami miliyan biyu da dubu 700, don
gudanar da wannan gagarumin aiki na cire aljani. “Wanda Jimlar kudin da
bokanya ta bukaci a biyata sun kai Dirhami miliyan hudu (Naira miliyan
160),”.
Jaridar ta Khaleej Times, ta ruwaito cewa, wannan mata ta
yi yunkurin sayar da gidanta, don haka ta bayar da cikon kudi na tsawon
lokaci, inda za a dauki shekaru har zuwa 20 tana biyan kudin. Sai kawai
aka aiko mata da sammaci, wai ana binta bashi.
Ganin haka, sai ita ’yarta suka kai kara gaban hukuma, aka
kuma bincika, aka gano cewa, matar da ta yi musu wannan kulle-kullen an
sha kama ta da laifin damfara. Hukumar Shari’a ta birnin Abu Dhabi ta bayar da cikakken
rahoton damfarar, inda ta bayyana cewa,tuni matar ta bukaci hukuma ta
dakatar da biyan wannan ciken kudin, a kuma soke amfani da shi kacokam.
Wannan Labarin Ya dade da faruwa, amma dalilin da ya sa na
kawo shi shine, yanzu wasu mayaudara sun fara yawo a cikin wannan k'asa
ta nigeriya da sunan bada magani. Yanda suke yi Shine, Idan suka zo a Unguwa Zasu tambaya
Waye mai kuddi sosai a wannan Unguwar? Idan aka nuna musu sai su tambayi
sunan 'yarsa Ko matarsa. Idan aka gaya musu sai su samu farar Leda su
cika ta da Iska makil suyi Tsibbace-Tsibbacensu Da sunan matar ko 'yar
Mutumen.
Nan take Ita kuma wacce aka yi wa wannan Asiri abin zai
kama ta Sai cikinta ya Cika kamar Zai fashe, tare da Jin Matsanancin
Jiri. Za'ayi ta neman magani amma ba za'a dace Ba, kuma su wayannan macuta sukan Sicce Wannan Cikin yau gobe kuma su Sake Hura shi.
Bayan Sati d'aya ko biyu zasu bayyana a Gidan da sunan Su
masu bada magani ne zasu taimaka, A haka zasu kawo magani su bayar tare
da Sanya miliyoyin kuddin da za'a bayar Idan ta samu sauki. Bayan kwana
biyu sai suje su Sacce wannan ledar marar lafiyar ta dawo kamar bata
tab'a ciwon ba. Wannan fa Shine damfarar da ake yi a yanzu.
Ina Mafita? Idan Irin Wannan Ya Faru a Unguwarku Ga Wata
Mafita Da Ta tabbata daga Sunnar Manzon Allah (Saww). Za'a samu Fitsarin
Rakumi da Nononsa a Rik'a bata tana sha In shaa Allahu Allah zai
Cubutar da mai lalurar daga Makircin Wayannan Masihirta.
An Samo hadisi daga Manzon Allah (Saww) yace, Ku nemi nonon rakumi yana maganin duk wata cuta da ke cikin ciki. Haka Kuma An karbo daga Annabi (Saww) Yace: Nonon rakumi da fitsarin rakumi suna maganin cutar dake cikin ciki wadda ake kira (Dharibah).
Har Wayau Jaridar Emirati mai lamba 11172 wacce ta fito a
shekarar fabairu 2006 ta rubuta wani bincike da tayi akan Rakumi inda ta
kawo cewa abu mafi amfani da yake jikin Rakumi akwai nononsa yana
tasiri wajen maganin ciwon zuciya da narkar da abinci da cututtuka da
suka shafi daji da sauran cutuka.
A wani bincike da Dr Ahlam al-awadi yayi wanda magazine na
al-da'awa suka buga mai lamba 1938 a shekarar 2004 ya ce, akwai amfani
mai yawa a cikin nonon Rakumi daga cikin abinda ya kawo ya tabbatar da
cewa fitsarin Rakumi na yana taimakwa wajen maganin cutar da ta shafi
fata yana gyra ga shi ya sanya shi kyalli da laushi ya kuma fidda
amosarin kai. Haka Kuma Fitsarin Rakumi Yana Maganin Kambun Baka da
Sihiri Da Iznin Allah. Abin Lura Dai wannan ya faru da Wasu 'yan Uwa
kuma Mashaa Allahu an samu waraka.
Note: Dharibah wata cuta ce dake cikin ciki, idan anci
abinci baya narkewa har sai ya rube. To idan an sha nonon rakumi bayan
an gama cin abinci, yana gusar da
wannan matsalar.
wannan matsalar.
Wannan Damfarar Tuni na dade da Sanin ta Sai dai Yanzu abin ya fara Yawaita don Haka a Kula Jama'ah.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Thu 20-04-2017
Thu 20-04-2017
No comments:
Post a Comment