DALILAN DA KE NUNA SAMUWAR ALLAH (SWT), ZUWA GA ATHEIST.
*****
Zuwa ga Masu da'awar Cewa, Babu UBANGIJI (Swt), Atheist a turance ku sani Duniyar nan gaba d'ayanta tana mai tabbatarwa da shaidawa da fad'in cewa, akwai Allah Mai girma da buwaya.
*****
Zuwa ga Masu da'awar Cewa, Babu UBANGIJI (Swt), Atheist a turance ku sani Duniyar nan gaba d'ayanta tana mai tabbatarwa da shaidawa da fad'in cewa, akwai Allah Mai girma da buwaya.
A cikin Al-qur'ani Mai Girma Allah Madaukakin Sarki yana
cewa,“Manzanninsu suka ce, yanzu akwai shakka a cikin samuwar Allah,
wanda ya halicci sammai da qassai, yana kiranku don ya gafarta muku zunubanku ya jinkirta musu
zuwa wani lokaci sananne. Sai suka ce, kufa ba kowa ba face
mutane kamar mu, kuna so ne ku kange mu daga abin da iyayenmu suke bautawa, ku zo mana da wata hujja mabayyaniya” (Suratul Ibarahim aya ta 10).
mutane kamar mu, kuna so ne ku kange mu daga abin da iyayenmu suke bautawa, ku zo mana da wata hujja mabayyaniya” (Suratul Ibarahim aya ta 10).
Hakika Mumini shi ke da yaqinin cewa, Allah Madaukakin
Sarki shi ne Ubangiji, mai iko, ya kuma tabbatar da cewa shi ne abin
bautawa shi kadai. Ta yaya zaku tsaya akan neman dalili akan samuwar abin da shi ne dalilin samuwar komai da kowa? Idan muka haura zuwa ga dalilan da suke nuna samuwar Allah, za mu samu dalilai masu yawa kamar haka:
DALILIN SAMUWAR ALLAH NA FIQRA: Babu wani abu da za ka yabi
Allah da shi face da falalarsa da ni’imominsa, a kowane hali kana
buqatar Allah mai girma da buwaya. Asalin halitta an yi ta ne a kan imani da Allah mahalicci. Babu wanda yake barin wannan abin da aka halicce shi a kai na imani da Allah mahalicci sai wanda Allah ya rufewa zuciya da hankali.
Daga cikin manya-manyan dalilai da suke nuna an halicci
mutum a kan imani da samuwar Allah Mad'aukakin Sarki Shine, fad'in
Manzon Allah (Saww) cewa, “Dukkan wanda ake haihuwa ana
haihuwarsa akan asalin halitta, iyayensa ne suka mayar da shi bayahude ko banasare ko ba majuse, kamar irin yadda dabba take haihuwa, shin kuna ganin ana haihuwar dabba mai yankakken kunne?” (Imamu Bukhari ne ya rawaito sh).

Dukkan wani abin halitta ya yarda da kadaita Allah a
yanayin halittarsa Allah (Swt) ya ce, “Ka tsayar da fuskarka a kan
addini, kana mai karkata ga barin qarya.Halittar Allah ce da ya halicci
mutane a kanta, babu canji ga halittar Allah. Wannan shi ne addini
miqaqqe sai dai da yawan mutane ba su sani ba” (Suratur rum aya ta 30).
Wad'annan dalilai na hankali suna nuna samuwar Allah mad'aukakin Sarki.
Sai tabbatuwar da samuwar Allah a hankalce ya fi kowane
dalili qarfi ga duk wani wanda shaidanu ba su janye shi ba, a cikin
Al-qur'ani mai girma Allah Mad'aukakin Sarki yana cewa, “Halittar Allah
ta asali da ya halicci mutane a kanta” (Suratur rum aya ta 30). Bayan ya
ce “Ka tsayar da fuskarka ga addini kana kaucewa barna”. (rum : 30).
Sunan Allah suna ne da aka zana shi a cikin halittar kowa, ba ya buqatar wani dalili fiye da wannan.
Lafiyayyen hankali yana shaida wa da samuwar Allah, amma wanda shaidanu suka janye shi zai iya qin wannan dalili ya ji ba ya buqatarsa. Amma idan ya fada cikin wata matsala babba, sai ka ga hannayensa da idanuwansa da zuciyarsa sun nufi sama kai tsaya suna neman taimako da agaji daga Ubangijinsa. Domin ya koma halittarsa ta asali madaidaiciya.

DALILIN SAMUWAR ALLAH NA HANKALI: Daga cikin manya-manyan
dalilai masu qarfi, wadanda ba wanda zai yi musu akansu sai mai jayayyar
runto kadai, akan tabbatar da samuwar Allah mahalicci, daga cikinsu akwai
1-Dukkan halitta akwai wanda ya halicceta: dukkan wad'annan
ababen halitta gaba d'ayansu akwai wanda ya samar da su, domin ba zai
yi wu su samar da kansu da kansu ba, saboda babu
abin da ya halicci kansa, don kuwa babu shi kafin samuwarsa, to kuma ta yaya zai samar da kansa, don dukkan wani abu samamme akwai wanda ya samar da shi.
abin da ya halicci kansa, don kuwa babu shi kafin samuwarsa, to kuma ta yaya zai samar da kansa, don dukkan wani abu samamme akwai wanda ya samar da shi.
Sannan kuma samuwar wadannan abubuwa akan wannan tsari mai kyau, hadadde, mai tafiya tare da sababi, a
hade da juna, ba zai yiwu ba a ce haka kurum abun ya faru kwatsam, a’a
dukkan wani mahaluki ba makawa yana da wanda ya halicce shi. To idan kuwa abin haka yake, to lallai Allah ne Ubangijin
talikai ya samar da su, Allah Mad'aukakin Sarki ya fad'i wannan dalili
inda yake cewa “Shin an halicce su ne daga babu, ko kuwa su ne masu yin
halittar?” (Suratud Dur aya ta 35).
Allah yana nufin su ba haka kurum akan halicce su ba, ba
tare da wani wanda ya halicce su ba, kuma ba su suka halicci kawunansu
ba, to dole suna da wanda ya halicce su, wanda shi ne Allah Madaukakin
Sarki.
Don haka ma a lokacin da Sayyidina Jubairu d'an Mud’im (RA)
ya ji Manzon Allah (Saww) yana karanta suratud Duri, ya zo kan wadannan
ayoyi, inda Allah yake cewa, “Shin an halicce su ne daga babu, ko kuwa
su ne masu yin halittar. Ko su ne suka halicci Sammai da Qasa, a’a ba su
yi yaqini ba. Ko a wajensu akwai taskokin Ubangijinka, kai ko su ne
wadanda suka mamaye komai” (Suratud Dur aya 35 zuwa 37).
A lokacin Jubairu yana mushiriki bai musulunta ba, amma duk
da haka sai ya ce, “Zuciyata ta kusa ta tsinke na musulunta” (Bukhari
ne ya rawaito shi).
Dan adam tare da dimbin ilimin sanin duniya da Allah ya ba
shi, har yanzu ya kasa gano wasu abubuwa na boye wadanda babu abin zai
kawo qarshen cece-kuce a kansu sai kawai imani da akwai Allah shi kadai.
2-Bayyanannu ayoyin Allah a cikin duniya da halittarsa.
Allah Madaukakin Sarki ya ce, “Ku duba (ku yi tunani) mene ne a cikin
Sammai da Qasa” (Yunus : 101).
Saboda a cikin duba sammai da qasa zai bayyana Allah ne mai halitta, kuma ya qara tabbatar da
kadaituwar Allah da ayyukansa. An cewa wani mutumin qauye, dame ka gane Ubangijinka? Sai
kadaituwar Allah da ayyukansa. An cewa wani mutumin qauye, dame ka gane Ubangijinka? Sai
ya ce, “Alamar sawu tana nuna tafiya, kashin raqumi yana nuna akwai raqumin. To yanzu sama
mai matakalai, da qasa mai hanyoyi, da teku mai igiyar ruwa da yawa, yanzu wadannan ba za su
nuna akwai Allah mai ji mai gani ba?”.
mai matakalai, da qasa mai hanyoyi, da teku mai igiyar ruwa da yawa, yanzu wadannan ba za su
nuna akwai Allah mai ji mai gani ba?”.
3-Tsaruwa lamarin duniya da kyautatuwarsa, dalili ne akan wanda yake tsara shi, shi ne abin
bauta shi kadai, kuma mamallakinsa shi kadai, Ubangiji shi kadai, babu wani abin bauta sai shi, kamar yadda ba zai yi wu ba a samu Ubangiji biyu, masu halitta kuma wadanda suka yi daidai da juna, to haka ma ba zai yiwu a samu ababen bauta guda biyu ba, waxanda suka yi daidai da juna.

Kuma ba zai yi wu a samu wadanda suka yi duniya su biyu ba,
abu ne tabbatacce a hankali, to haka ma ba za a samu abbaben bautawa
guda biyu ba.
DALILIN SAMUWAR ALLA NA SHARI'A: Dukkan Shari’u suna nuna samuwar wanda ya yi halitta, kuma suna nuna cikar iliminsa da hikimarsa da jinqansa, saboda dukkan shari’u ba makawa da wanda ya
shar’anta su, wanda shi ne Allah Mai girma da buwaya, Allah (Swt) yana
cewa, “Ya ku mutane ku bautawa Ubangijinku wanda ya halicce ku, da
wadanda suke gabaninku ko kwa samu taqawa. Wanda ya sanya muku qasa ta
zama shimfida gareku, ya sanya kuma sama ta zama gini gareku, ya saukar
daruwa daga
girgije, ya fitar da ‘ya’yan itace arziqi gareku, to kada ku sanya wa Allah abokan tarayya alhali kuna sane” (baqra aya ta 21 zuwa 22).
girgije, ya fitar da ‘ya’yan itace arziqi gareku, to kada ku sanya wa Allah abokan tarayya alhali kuna sane” (baqra aya ta 21 zuwa 22).
DALILIN SAMUWAR ALLAH NA JI DA GANI: Daga bayanannun
dalilai da suke nuna samuwar Allah Mahalicci akwai dalilin da duk mai
hankali yake gani kuma yake jinsa, kamar:
1-Amsa addu’o’i: Mutum yana roqon Allah, ya ce, “Ya
Ubangiji” ya roqi wani abu, sai kuma ya ga an amsa masa, to wannan
dalili ne da ake gani dake nuna samuwar Allah Ubangiji, saboda Allah ya
amsa masa, kuma mutum ya ga hakan quru-quru.
Haka ma muma sau da yawa mun ji misalai a da, da yanzu na cewa Allah ya amsa musu abin da suka roqa. To wannan wani lamari ne da yake nuna samuwar Allah Mahalicci, a cikin Alqur’ani akwai dalilai
irin wadannan da yawa, daga cikinsu akwai fad'in Allah, “Ka tuna
(Annabi) Ayyuba lokacin da ya kira Ubangijinsa cewa cuta ta shafe ni,
Allah kuma kai ne mafi jinqai masu jinqai. Sai muka amsa masa”
(Al’anbiya aya ta 83 zuwa 84). Da ayoyi da yawa irin wad'annan. Kore samuwar Allah cuta ce a cikin hankali, kuma matsala ce a cikin tunani.
2-Shiryar da halittu zuwa ga abin da yake shi ne sirrin
rayuwarta. Wanene ya shiryar da mutum zuwa ga kama mama yayi da aka
haife shi? Wanene ya shiryar da Al-Hudu-Hudu har yake gane wurin ruwa a
qarqashin qasa, wanda ba wanda yake ganin hakan sai shi? Haqiqa Wannan aikin Allah ne, yana cewa: “Ubangijinmu wanda ya halicci dukkan komai kuma ya shiryar da shi” (Daha aya ta 50).
3-Ayoyin da Allah ya aiko Annabawa da Manzanni da su, su ne
Mu’ujizozin da Allah ya qarfafa su da su, ya zabe su, daga cikin mutane
ya fifita su. Dukkan wani Annabi Allah ya aiko shi da wata mu’ujiza zuwa
ga mutanensa, tana tabbatar da cewa abin da aka aiko shi da shi daga
wajen Allah ne, mahalicci abin bauta shi kadai, babu wani abin bauta
wanda ba shi ba.
Sannan har wayau daga Cikin dalilai na hankali da ke nuna Samuwar Allah (Swt), akwai yin Arziki ko talauci, babu shakka duk wanda zai ce babu Allah to yana Fadar son ransa ne. Domin idan ka duba a kusa da kai a kwai mai kuddi ko Ilmi wanda kake burin Inama ace kai ne, makawar kuwa kai ka halicci kanka to zaka Mayarda kanka kamar wancen da kake muradin zama kamarsa.
Abinda Zan Cewa, Masu da'awar Babu Allah d'aya ne Zuwa Biyu, Na farko Ina yi musu murna da Suka Shaidi Cewa, Babu Allah. Dalili kuwa Yana daga Cikin Sharuddan Karbar Addinin
Musulunchi wato La'Ilaha (ma'ana "Babu Wani abin Bauta") don haka ina
jan hankalinsu tun lokaci bai kire ba Su karbi ragowar ILLALLAH (ma'ana
"Sai Allah").
Ina Fatan Duk wanda Ya Samu Karanta wannan Rubutun Zai
taimaka da Share domin Wayannan mutanen suna nan Suna ta Jan yan Uwanmu a
cikin wannan muguwar Ak'ida ta BABU ALLAH.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Thu 20-04-2017
Thu 20-04-2017
No comments:
Post a Comment