GUDUMMUWAR MAWAKAN HAUSA A CIKIN AL-UMMA
******
Sau tari Wasun mu sukan Rik'ajin haushi tare da Sukar mawaka musamman namu na Hausa tare da yi musu kallo a matsayin 'yan Iska ko kuma masu b'ata tarbiyar Al-ummah. Hak'ik'a kafin In kawo gudummuwar da suke bayarwa yana da kyau in yi bayanin wata aya a cikin al-qur'ani wacce wasu da yawa basu san dalilin Saukar taba, amma daga zarar Sunji anyi maganar mawaki sai su kawo ayar a matsayin Hujjar Qin wak'a. Ayar da take Cikin Suratush-Shu'ara'I aya ta 224 In da Allah (Swt) Yake Cewa; "WASH-SHU'ARA'U YATBA'UHUMUL-GH AAWUUN" Ma'ana "Kuma mawaƙa halakakku ne ke bin su." (Sura shu'ara'i aya ta 224).
******
Sau tari Wasun mu sukan Rik'ajin haushi tare da Sukar mawaka musamman namu na Hausa tare da yi musu kallo a matsayin 'yan Iska ko kuma masu b'ata tarbiyar Al-ummah. Hak'ik'a kafin In kawo gudummuwar da suke bayarwa yana da kyau in yi bayanin wata aya a cikin al-qur'ani wacce wasu da yawa basu san dalilin Saukar taba, amma daga zarar Sunji anyi maganar mawaki sai su kawo ayar a matsayin Hujjar Qin wak'a. Ayar da take Cikin Suratush-Shu'ara'I aya ta 224 In da Allah (Swt) Yake Cewa; "WASH-SHU'ARA'U YATBA'UHUMUL-GH AAWUUN" Ma'ana "Kuma mawaƙa halakakku ne ke bin su." (Sura shu'ara'i aya ta 224).
Ibn Jareer da Ibnu Abi-Haatim sun fitar da hadisin daga
Babban Malami Masani tafsirin al-qur'ani wato Ibnu Abbas cewar; Wasu
mutane (mawaqa) su biyu sunyi ma juna habaici (alokacin Manzon Allah
(Saww), Daya daga cikinsu mutumin madina ne. Dayan kuma ba d'an madina
bane. Sun kasance a koda yaushe sukan soki junansu da munanan
kalamai a waken da suke, kuma kowannensu yana da masu binsa suna zuga
shi daga cikin danginsa.
Sai Allah (Swt) Ya Saukar da fadinSa Cewa, "Kuma mawaƙa halakakku ne ke bin su." To wayancen dangin nasu sune Allah yake nufi da "Halakakku" (su da ke zugi domin ayi zage-zage).
Har wayau Imamul-hakim da Ibnu Jareer sun karbo hadisi daga
Abu Hasan Albarrad cewar: "bayan da wannan ayar ta sauka
wash-shu'ara'u. Sai Wasu daga cikin mawakan Annabi (Saww), Irinsu
Abdullahi Ibn Rawaha da Ka'abu Ibn Malik da kuma Hassanu Ibn Thabit
(rta) suka je wajen Manzon Allah (saww) suka ce: "Ya Rasulil Lahi Gashi
Wannan aya ta Sauka, Kuma Allah yasan Cewar, Mu mawaka ne. Shikenan mun
halaka." Nan da nan sai Allah (Swt) ya sake Saukarda wata ayar
Inda Allah (swt) yayi istisna'i garesu cewar. "ILLAL-LADHEENA AMANU"
ma'ana "Sai dai wadanda sukayi imani kuma suka aikata ayyuka na kwarai
kuma suka yi zikirin Allah da yawa" (Shura'I aya ta 227). Sai Manzon
Allah (Saww) ya kirawo su ya gaya musu tare da karanta musu Ayar domin
hankalinsu ya kwanta.
Mai Neman karin bayani ya duba, Usudul-ghaabah- Juzu'i
na 3 shafi na 235. Tirmidhy ma ya fitar da hadisin ta isnadi mai Qarfi, a
duba a Sunanut-Tirmiziy hadisi mai lamba 2851 da kuma SIYARU
A'ALAMIN-NUBALA 'I juzu'i na 1 shafi 236 domin karin bayani. Nasan wani zaice to ai Wakokin Hausawa babu komai a cikin
su in ban da sakarci da sharholiya da kuma son a kwaikwayi Indiyawa,
Babu shakka duk mai irin wannan tunani zan iya kiran shi wanda bai waye
ba ko kuma ma bai da zurfin tunani domin wakokin Hausa suna taka
muhimmiyar gudummawa ga addinin musulunchi da ma al'umma a kebe.
Muna sane da cewa kafin finafinan Hausa su samu babu finafinan da suka fi na Indiyawa karbuwa a kasar Hausa, kuma idan an duba za a ga akwai
wakokinsu wadanda babu komai a ciki face yabon gumakansu da sauran
abubuwan bautarsu, to ire-iren wadannan wakoki ne mutanenmu suke yi da bakinsu, ba su san mene ne ma’anar abubuwan da suke fada ba, amma
wakokin da ake yi a finafinan Hausa kowa ya san abin da ake fada, sannan
ana ambaton Ubangiji da Annabinsa da kuma yabo gare su, kafin a shiga
gundarin wakar ko a tsakiyarta ko kuma a karshenta (Wanda ake kira
Introduction and Conclusion a turance). Wannan ba karamar gudumuwa bace
domin da yanzu Allah kadai ya san wanda ya hardace wakokin bautar gunka. Mu Janye maganar Gudumuwa wak'a na da tasiri a wajen jan hankalin
al'umma daga cikin mawakan a zamanin Annabi (Saww) akwai Hassanu bin
Thabit (rta) kamar yanda na ambata a baya, Babu shakka Annabi (Saww) da
kansa ya tab'a umurtarsa da ya tashi ya mayarwa da wasu mawaka da suka
ci mutunchin Annabi (Saww) da martani.
Bayan wancen
K'arnin Bincike ya nuna cewa, mutum na farko wanda ya fara rubuta
littafi a kan ilimin ma'aunin waka wanda da Larabci ake kira Arudhi shi ne Khalil Ibn Ahmad Alfarahidi Albasari, a karni na
biyu. Marubucin ya rasu a shekara ta 174 bayan hijira Annabi Mahamadu (Saww) wacce ta zo daidai da shekarar ta 791 Shekarar alak'ak'ai Miladiya. To, amma kuma tarihi ya nuna cewa, kafin shi wannan bawan Allah ya rubuta wannan littafi akwai mawaka da suke rubuta wakoki, ko da ya zo ya
rubuta wannan littafi sai ya dace da ma'aunin ire-iren wakokin da suke
yi tun dauri. Dalilin da ya sa ya rubuta wannan littafi shi ne, Khalil
ya yi kwadayin ilmi irin na Sibawaihi wani malamin Nahawu ko kuma
marubucin Nahawu, sai ya fita yana kewaya Ka'aba yana rokon Allah ya ba
shi baiwa ta ilmi, sai Allah ya yi masa baiwa ta wallafa littafin ilmin
ma'aunin waka, Arudhi. A cikin littafin ne ya takaita waka a kan ma'auni
goma sha shida. To, amma da yake rubutun nawa ba yana magana a kan
ilimin wakar ba ne, bari na mayar da alkalami na a saman hanya, wato kar
ya yi ratse.
Amma ya yakamata a yi wakar? Kasancewa a
al'adar bahaushe tana tafiyane tare da addinin musulunce, to kamata yayi
idan za'a yi wakar ta kasance namiji ne kadai ke rairata banda macce,
haka idan macce za'a nuna tana wakar to kada a hada ta da namiji. Misali, akwai wani fim mai suna Wani Gari. A fim din ai
ba'a hada mata da maza suna rawa ba, kawai an nuna jarumin ne shi kadai
yana karanta wakar. Haka a fim din Salma shima jarumin ne kawai ke waka
banda macce, haka fim din Jiddah shima macce ce kadai ke wakar ba tare
da namiji ba. haka ya kamata wakokin finafinan Hausa su kasance domin
kare mutuncin al'adar mu da kuma addinin mu.
Babu shakka ina goyon bayan Wakoki da finafinan Hausa sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba nuna saurayi da budurwa suna waka da rawa a tare wannan sam ba al'adar Hausawa ba ce sam domin duk wanda ya kalli irin wa dannan wakoki a finafinan Hausa zai ga abin sam ba tsari. sai da me kuma? masu kallo ne ke sanya ana sanya saurayi da budurwa a tare domin su a ganinsu idan ba haka akayi ba sam ba'a burgesu ba. saura Gudumuwar fina-finan Hausa.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 22-04-2017