HUJEWAR OZONE LAYER YA FARA KAWO ANNOBA A CIKIN AL'UMMA.
Tun Kusan Lokacin da Na samu Labari akan k'aruwar Hujewar OZONE LAYER ( Bargon da ke matsayin kariya tsakanin duniya da kuma cutukkan rana), nake ta tunani akan wannan lamari.
Tun Kusan Lokacin da Na samu Labari akan k'aruwar Hujewar OZONE LAYER ( Bargon da ke matsayin kariya tsakanin duniya da kuma cutukkan rana), nake ta tunani akan wannan lamari.
A bangare daya kuma Yawaitar Mace-macen hadi da rashin
lafiya da Suke Faruwa a Jahar mu ta Sokoto sai na tsaya nayi nazari tare
da Bincike mai zurfi game da Wannan Lamari. Sai naga gaba days an dau
wannan matsala kacokan an daurata ga zazzabin Cizon Sauro. Wanda kuwa ga
dukkan alamu ba haka lamarin yake ba.
Shi dai Wannan OZONE LAYER masana suka ce abu ne tamkar bargo a sararin saman duniya kuma kariya ne ga (Sama) da kuma Mutane.
Suka kara da Cewa, shi wannan Bargon da ake kira ozone
layer, yana shinfide ne a Sararin Samaniya domin ya zama kariya ga
halittun kasa daga sinadaran da suke zubowa daga zafin rana wanda zasu
cutar da 'dan Adam ta hanyar sanyawa mutane cututtuka (masu wuyar
Sha'ani). To idan sinadirai masu cutarwa suka zubo sai su makale a jikin
wannan Bargon na Ozone layer.
Babu Shakka Wannan Zance na Masana Ilmin Kimiya ba karya bane game da Wannan Bargon.
Domin tun Kusan Shekaru 1400 da suka Gabata Al-qur'ani Mai Girma ya gaya mana labarin wannan Bargon da ke Sama.A Cikin Al-qur'ani Mai Girma Allah (Swt) Yana Cewa,
ﻭَﺟَﻌَﻠْﻨَﺎ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀَ ﺳَﻘْﻔًﺎ ﻣَّﺤْﻔُﻮﻇًﺎ ۖ ﻭَﻫُﻢْ ﻋَﻦْ ﺁﻳَﺎﺗِﻬَﺎ ﻣُﻌْﺮِﺿُﻮﻥَ
ﻭَﺍﻟﺴَّﻘْﻒِ ﺍﻟْﻤَﺮْﻓُﻮﻉِ
.
A Wani Wuri Kuma Allah (Swt) ya gaya mana Cewa, Wannan bargo kariya ne ga Mazauna kasa.
ﻗَﺪْ ﻣَﻜَﺮَ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦ ﻗَﺒْﻠِﻬِﻢْ ﻓَﺄَﺗَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ
ﺑُﻨْﻴَﺎﻧَﻬُﻢ ﻣِّﻦَ ﺍﻟْﻘَﻮَﺍﻋِﺪِ ﻓَﺨَﺮَّ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢُ ﺍﻟﺴَّﻘْﻒُ ﻣِﻦ
ﻓَﻮْﻗِﻬِﻢْ ﻭَﺃَﺗَﺎﻫُﻢُ ﺍﻟْﻌَﺬَﺍﺏُ ﻣِﻦْ ﺣَﻴْﺚُ ﻟَﺎ ﻳَﺸْﻌُﺮُﻭﻥَ
MA'ANA "Lalle ne waɗanda suke a gabaninsu sun yi makirci,
sai Allah Ya je wa gininsu daga harsa-shensa, sai rufi ya faɗa a kansu
daga bisansu, kuma azaba ta je musu daga inda ba su sani ba." (Suratul
An-Nahl aya ta 26).
Friedrich Schonbein Shine mutunen da ya gano Ozone a
shekarar 1839, In da a Shekarar 1840 Gordon Miller ya gano amfanin
wannan bargo na Ozone layer. Shi dai wannan bargon ya fara hujewa tun kusan shekarun
1980 inda wannan hujewar ta rika fadada tun daga wancan lokaci har zuwa
yanzu, in da a wannan shekarar ta 2016 aka gano wannan bargon yayi
qatuwar hujewa.
Masana dai sun riga sun fadi Cewa, Wannan hujewar ta kan
iya haifar da kafewar manya da kananan koguna, da kuma karuwar yawan
ruwan da ke cikin manyan kogunan
wannan duniya.
wannan duniya.
Haka Kuma Sun fadi Cewa, Wannan hujewar barazana ce ga
lafiyar 'yan Adam din dake rayuwa a wannan duniya musamman sassan
duniyar dake fama da yanayin zafin rana. Domin ana samun karin sabbin
cututtukan da suke da alaka da fata masu Wuyar magani.
Wannan abu hakika ya fara tabbatuwa domin kuwa a watan juli
din wannan shekara ta 2016 (Wato July 2006), a North America an samu
mutuwar a kalla mutane 225. Wanda kuma duka bincike ya tabbatar da cewa, dukansu sun samu cutukkane ta dalilin yawan zafin rana.
Haka Wannan Annoba ta mace-mace da rashin lafiya ta yawaita
a Wani kauye dake Cikin Erteria In da kusan Sai da 'yan kauyen Suka
yanke kauna da rayuwa. Kwatsam kuma Sai gashi Wannan Annoba ta Rashin Lafiya da
Mace-mace Sun yawaita a Cikin Tsakiyar Garin Sokoto In da a Rana 'daya
zakaji an Rasa fiye da Mutum 50. Babu Shakka Annoba Jarabawa Ce Da Allah Ke yiwa Bayinsa Ko
dai don Ya Jarabesu ko Kuma don Gargadesu akan Su tuba daga miyagun
laifuka.
....Subhanallah!!!
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Wed 26/10/2016
Wed 26/10/2016
No comments:
Post a Comment