Wednesday, 30 November 2016

LABARIN YAJUJ WAMA JUJ

LABARIN YAJUJU DA MAJUJU.
*********

 
Allah (Swt) a Cikin Al-Qur'ani mai Girma Yana Cewa;

ﺣَﺘَّﻰ ﺇِﺫَﺍ ﻓُﺘِﺤَﺖْ ﻳَﺄْﺟُﻮﺝُ ﻭَﻣَﺄْﺟُﻮﺝُ ﻭَﻫُﻢ ﻣِّﻦ ﻛُﻞِّ ﺣَﺪَﺏٍ ﻳَﻨﺴِﻠُﻮﻥ


Ma'ana "Har sa'ad da aka bude Yajuju da Majuju alhali kuwa suna gaggawa daga kowane tudun kasa." (Suratul Anbiya aya ta 96(

Yajuju da Majuju, tsatso ne, na daya daga cikin ‘ya'yan Annabi Nuhu (Alaihis Salam).

A zamanin Annabi Ibrahim (Alaihis Salam) da akwai wani sarki da ake kira da Zulkarnaini, shi wannan sarki, Allah ya bashi iko da kuma Mulki tun daga Bangon Gabas har zuwa yamma.

Shine mutumen da ya zagaye duniya tun daga farkon Inda rana take fitowa har Inda take faduwa.
Wasu ma suna ganin Zurkarnaini Annabine, amma dai maganar gaskiya zurkarnaini Sarki ne kuma mutumin kirki ne da ya shimfida Adalci, shine ya gina wannan Katanga da ta raba wannan duniya da Yajuju da Majuju. Haka kuma, wannan Katanga an gina tane da narkakken karfe da
duwatsu da kwalta da ruwan dalma.

A zamanin Zulkarnain wadannan al’umma (Yajuju da Majuju) sun addabi mutane, shine al’ummar da
Zulkarnaini yake mulka suka rokeshi da ya gina musu katangar da zata rabasu da Yajuju da Majuju.
Yajuju da Majuju sunyi ta kokarin fasa wannan Katanga su fito amma kuma sun kasa.
Sunyi dukkan irin dabarunsu su yi tsalle su fito amma Allah bai basu iko ba, shine tun daga wancan lokaci har kawo yau suna nan suna kwakwule wannan Katanga domin su samu su fito, amma Allah ba zai basu iko ba, sai a karshen duniya.

Ibn Mas’ud (Rta) ya ruwaito daga Manzon Allah (Saww) cewa. A daren da Manzon Allah (Saww) yayi Isra’I ya hadu da Babansa Annabi Ibrahim da Annabi Musa da kuma Annabi Isah, dukkansu sun tattauna akan shin yaushe ne Alkiyama zata tsaya, sun fara tambayar Annabi Ibrahim yace bai
sani ba.

Daga nan Annabi Musa yace shima bai sani ba, daga nan sai Annabi Isah yace babu wanda ya san wannan ranar sai Ubangiji shi kadai.

Sai Annabi Isa (Alaihis Salam) ya cigaba da cewa, abinda Ubangijina ya gayamin shine a karshen duniya, Dajjal zai bayyana, ya zama fitina daga karshe sai a sauko dani, idan ya hadu da ni zai dinga narkewa yana zagwanyewa, Haka nan Allah zai halakar da shi (Dajjal).

Sannan Musulmi zasu yaki kafurai, har sai takai matsayin da Idan kafiri ya buya a bayan wani dutse ko bishiya, zasu yi Magana su kirawo musulmi suce masa zo ga kafiri ka kashi shi.
Daga nan kuma, adalci zai yadu a ban kasa tsakanin Musulmi, can kuma sai Allah ya fito da Yajuju da Majuju. Zasu barko cikin wannan duniya ta gabas da yamma kudu da Arewa, suna shanye ruwa, suna cinye dukkan wani abu da suka yi arba das hi. A lokacin ne al’umma zasu je ga Annabi Isah suna mai rokonsa da ya roki Ubangiji Allah ya kade musu wannan Masifa da Bala’I na Yajuju da Majuju.

Sai Annabi Isah ya daga hannu ya roki Ubangiji, Allah mai girma da daukaka ya amsa, sannan ya dinga saukar musu da tsutsotsi daga sama, suna halakar da su, bayan sun mutu duniya gabaki daya zata cika da warin gawarwakinsu da jinanansu.

Daga nan kuma Sai Allah ya saukar da Ruwan Sama wanda zai wanke duniya gabaki daya ya wanke dukkan dattin gawarwakin Yajuju da Majuju.

Annabi Isah (Alaihis Salam), ya cigaba da cewa, daga zarar Allah ya saukar da wannan ruwa, to babu wani abu da yake gab da zuwa face Alkiyama.

Haka kuma An karbo hadisi daga Abu-Huraira (Rta), Cewa, Manzon Allah (Saww), ya ce “A kowacce rana wasu al’umma (Yajuju da Majuju) suna nan suna hake wata Katanga, da zasu shigo cikin wannan duniya.

Sai sun yi haka har sun gaji, sannan zasu fara hango harsken rana, abinda yake nuna hakarsu ta kusa cimma ruwa (ma'ana sun kusa bige ginin), sai kawai shugabansu, ya umarce su da su koma su kwanta su huta gobe zasu dawo su cigaba.

Cikin hukuncin Ubangiji washe gari suna zuwa, sai su tarar Allah (Swt) ya shafe wannan Katanga ta kara karfi da kwari, sama da yadda suka sameta a jiya. Haka zasu sake cigaba da tone wannan Katanga, su sake komawa, washe gari su sake ganinta kamar basu taba haketa ba.

Haka nan zasu yi ta yi, har sai lokacin da Allah ya hukunta fitowarsu. Idan sunyi aiki har sun bula katangar sun fara hango hasken rana, anan ne shugabansu zai umarce su da su koma su
kwanta, gobe idan sun dawo zasu cigaba, amma a wannan Ranat zai ce IN SHAA ALLAHU.
Bisa fadin IN SHAA ALLAHUN da shugabansu ya yi sai Allah ya amsa, washe gari idan sun komo zasu sami wannan Katanga yadda suka barta jiya! Bayan dawowarsu ne, washe gari, zasu ci gaba da yin aikinsu na bugun wannan Katanga.

Kuma cikin nufin Allah, zasu buge wannan gini su shigo cikin duniya daga katangesu da Allah yayi da al’umma, idan suka fito zasu shanye dukkan wani ruwa da sukayi ido hudu dashi, sannan zasu cinye dukkan wani abinci da suka gani, kai kusan dukkan wani abu da suka gani sai sun cinye shi.

kama daga Bishiya tsirrai da dabbobi, sannan zasu shiga kisan mutane babu ji babu gani!
A wannan lokacin Yajuju da Majuju zasu dinga harba kibau sararin samaniya. Suna harba kibiyoyi da masuna, sannan suna fadowa kasa suna masu digar da jini a jikinsu, anan ne Yajuju da Majuju zasu ce, mun gama da al’ummar da take a ban-kasa sannan kuma wadan da suke sama suma mun gama da su!
A lokacin da suka yi wannan ikirari ne kuma, Allah zai yi musu ruwan wasu irin tsutsotsi wadan da zasu dinga makalemusu a wuya suna cizonsu, haka nan, wannan tsutsa zata hakalasu gabaki dayansu a
cikin dare daya!

A duba a Cikin kitaab al-fitan, (hadisi 4080), 2/1364.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tues 30/08/2016

No comments:

Post a Comment