Wednesday, 30 November 2016

LABARIN YAJUJ WAMA JUJ

LABARIN YAJUJU DA MAJUJU.
*********

 
Allah (Swt) a Cikin Al-Qur'ani mai Girma Yana Cewa;

ﺣَﺘَّﻰ ﺇِﺫَﺍ ﻓُﺘِﺤَﺖْ ﻳَﺄْﺟُﻮﺝُ ﻭَﻣَﺄْﺟُﻮﺝُ ﻭَﻫُﻢ ﻣِّﻦ ﻛُﻞِّ ﺣَﺪَﺏٍ ﻳَﻨﺴِﻠُﻮﻥ


Ma'ana "Har sa'ad da aka bude Yajuju da Majuju alhali kuwa suna gaggawa daga kowane tudun kasa." (Suratul Anbiya aya ta 96(

Yajuju da Majuju, tsatso ne, na daya daga cikin ‘ya'yan Annabi Nuhu (Alaihis Salam).

A zamanin Annabi Ibrahim (Alaihis Salam) da akwai wani sarki da ake kira da Zulkarnaini, shi wannan sarki, Allah ya bashi iko da kuma Mulki tun daga Bangon Gabas har zuwa yamma.

Shine mutumen da ya zagaye duniya tun daga farkon Inda rana take fitowa har Inda take faduwa.
Wasu ma suna ganin Zurkarnaini Annabine, amma dai maganar gaskiya zurkarnaini Sarki ne kuma mutumin kirki ne da ya shimfida Adalci, shine ya gina wannan Katanga da ta raba wannan duniya da Yajuju da Majuju. Haka kuma, wannan Katanga an gina tane da narkakken karfe da
duwatsu da kwalta da ruwan dalma.

A zamanin Zulkarnain wadannan al’umma (Yajuju da Majuju) sun addabi mutane, shine al’ummar da
Zulkarnaini yake mulka suka rokeshi da ya gina musu katangar da zata rabasu da Yajuju da Majuju.
Yajuju da Majuju sunyi ta kokarin fasa wannan Katanga su fito amma kuma sun kasa.
Sunyi dukkan irin dabarunsu su yi tsalle su fito amma Allah bai basu iko ba, shine tun daga wancan lokaci har kawo yau suna nan suna kwakwule wannan Katanga domin su samu su fito, amma Allah ba zai basu iko ba, sai a karshen duniya.

Ibn Mas’ud (Rta) ya ruwaito daga Manzon Allah (Saww) cewa. A daren da Manzon Allah (Saww) yayi Isra’I ya hadu da Babansa Annabi Ibrahim da Annabi Musa da kuma Annabi Isah, dukkansu sun tattauna akan shin yaushe ne Alkiyama zata tsaya, sun fara tambayar Annabi Ibrahim yace bai
sani ba.

Daga nan Annabi Musa yace shima bai sani ba, daga nan sai Annabi Isah yace babu wanda ya san wannan ranar sai Ubangiji shi kadai.

Sai Annabi Isa (Alaihis Salam) ya cigaba da cewa, abinda Ubangijina ya gayamin shine a karshen duniya, Dajjal zai bayyana, ya zama fitina daga karshe sai a sauko dani, idan ya hadu da ni zai dinga narkewa yana zagwanyewa, Haka nan Allah zai halakar da shi (Dajjal).

Sannan Musulmi zasu yaki kafurai, har sai takai matsayin da Idan kafiri ya buya a bayan wani dutse ko bishiya, zasu yi Magana su kirawo musulmi suce masa zo ga kafiri ka kashi shi.
Daga nan kuma, adalci zai yadu a ban kasa tsakanin Musulmi, can kuma sai Allah ya fito da Yajuju da Majuju. Zasu barko cikin wannan duniya ta gabas da yamma kudu da Arewa, suna shanye ruwa, suna cinye dukkan wani abu da suka yi arba das hi. A lokacin ne al’umma zasu je ga Annabi Isah suna mai rokonsa da ya roki Ubangiji Allah ya kade musu wannan Masifa da Bala’I na Yajuju da Majuju.

Sai Annabi Isah ya daga hannu ya roki Ubangiji, Allah mai girma da daukaka ya amsa, sannan ya dinga saukar musu da tsutsotsi daga sama, suna halakar da su, bayan sun mutu duniya gabaki daya zata cika da warin gawarwakinsu da jinanansu.

Daga nan kuma Sai Allah ya saukar da Ruwan Sama wanda zai wanke duniya gabaki daya ya wanke dukkan dattin gawarwakin Yajuju da Majuju.

Annabi Isah (Alaihis Salam), ya cigaba da cewa, daga zarar Allah ya saukar da wannan ruwa, to babu wani abu da yake gab da zuwa face Alkiyama.

Haka kuma An karbo hadisi daga Abu-Huraira (Rta), Cewa, Manzon Allah (Saww), ya ce “A kowacce rana wasu al’umma (Yajuju da Majuju) suna nan suna hake wata Katanga, da zasu shigo cikin wannan duniya.

Sai sun yi haka har sun gaji, sannan zasu fara hango harsken rana, abinda yake nuna hakarsu ta kusa cimma ruwa (ma'ana sun kusa bige ginin), sai kawai shugabansu, ya umarce su da su koma su kwanta su huta gobe zasu dawo su cigaba.

Cikin hukuncin Ubangiji washe gari suna zuwa, sai su tarar Allah (Swt) ya shafe wannan Katanga ta kara karfi da kwari, sama da yadda suka sameta a jiya. Haka zasu sake cigaba da tone wannan Katanga, su sake komawa, washe gari su sake ganinta kamar basu taba haketa ba.

Haka nan zasu yi ta yi, har sai lokacin da Allah ya hukunta fitowarsu. Idan sunyi aiki har sun bula katangar sun fara hango hasken rana, anan ne shugabansu zai umarce su da su koma su
kwanta, gobe idan sun dawo zasu cigaba, amma a wannan Ranat zai ce IN SHAA ALLAHU.
Bisa fadin IN SHAA ALLAHUN da shugabansu ya yi sai Allah ya amsa, washe gari idan sun komo zasu sami wannan Katanga yadda suka barta jiya! Bayan dawowarsu ne, washe gari, zasu ci gaba da yin aikinsu na bugun wannan Katanga.

Kuma cikin nufin Allah, zasu buge wannan gini su shigo cikin duniya daga katangesu da Allah yayi da al’umma, idan suka fito zasu shanye dukkan wani ruwa da sukayi ido hudu dashi, sannan zasu cinye dukkan wani abinci da suka gani, kai kusan dukkan wani abu da suka gani sai sun cinye shi.

kama daga Bishiya tsirrai da dabbobi, sannan zasu shiga kisan mutane babu ji babu gani!
A wannan lokacin Yajuju da Majuju zasu dinga harba kibau sararin samaniya. Suna harba kibiyoyi da masuna, sannan suna fadowa kasa suna masu digar da jini a jikinsu, anan ne Yajuju da Majuju zasu ce, mun gama da al’ummar da take a ban-kasa sannan kuma wadan da suke sama suma mun gama da su!
A lokacin da suka yi wannan ikirari ne kuma, Allah zai yi musu ruwan wasu irin tsutsotsi wadan da zasu dinga makalemusu a wuya suna cizonsu, haka nan, wannan tsutsa zata hakalasu gabaki dayansu a
cikin dare daya!

A duba a Cikin kitaab al-fitan, (hadisi 4080), 2/1364.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Tues 30/08/2016

SANARWA MAI MUHIMMANCHI GAME DA MADIGO DA LUWADI

SANARWA MAI MUHIMMANCI
********
Ka karanta tabbas Zai amfaneka idan ma bai amfaneka ba zai amfani 'danka, 'yarka ko kuma qanenka ko 'dan uwanka. Tun kusan Watan January nayi Rubutu akan 'yan Mata masu 'dabi'ar yin Madigo (Lesbian), tun kusan wancen lokaci na samu kira daga wata baiwar Allah Wadda ta bayyanamin Dalilin shigarta harkar madigo da kuma halin da take ciki.

Yarinyar wacce mun dau kusan Mintuna arba'In mun waya ta shaida min dalilin shigarta Harkar madigo, In da ta bayyana min a makarantar gaba da Secondry aka koyar da Ita wannan muguwar 'dabi'ah.
"Bayan kaini makaranta mu hudu ne a dakin da nake, kuma nice karama a duk cikin wayanda muke daki 'daya da su, ranar da nazo na fara fahimtar 'yan Iska ne, domin kuwa a gado 'daya naga suna yin bacci duk da kowace nada nata gado."

"A haka har na fahimci me suke yi domin kuwa wani lokacin a gabana suke sheke ayarsu."
Yarinyar taci gaba da gayamin cewa, a hankali idan suna yi sai taji sha'awa ta taso mata, kwatsam rannan sai suka bukaci ta shiga cikinsu domin jin dadi. Da farko sai ta nuna musu ai ita bata sha'awar wannan mu'amula kuma tana ma son ta chanja 'daki ne domin kada ta takura musu.

Anan ne suka nuna mata ai babu damuwa tayi zamanta a dakin nasu domin halayenta na burgesu.
Kwatsam sai ranan suka nuna mata ai ta shigo cikinsu yafi tunda Allah bai fadi azabar da za'ayiwa mata 'yan madigo ba sai 'yan Luwadi. Sannan kuma tayi wannan shi ya fiye mata da taje tayi zini ko ta aikata Mistabution (ISTIMINA'I).

Ta shaida min da irin wayannan kalamai aka sanya ta a madigo kuma wallahi yanzu bata sha'awar kowane namiji, haka kuma bata sha'awar aure.

Ta kara shaidamin Cewa, Ita kadai ta lalata yara bata san adadiba, kuma yanzu tana son ta tuba amma ba ta san yanda zatayi ba.

Anan na bata wasu shawarwari tare da nuna mata muddin ta mutu bata tuba ba to kuwa akwai matsala domin Allah zai mata Ukuba fiye da yanda take tunani.

Wannan yarinyar tayi godiya ta kuma bukaci duk ranar da na samu lokaci don Allah Inyi fadakarwa game da Irin Wannan 'yan madigon Masu nunawa mutane madigo bai da wata azaba da aka tanadarwa masu yinsa, haka kuma macce zata ji dadi ba tare da ta rasa budurcin ta ba. Bayan Wannan Jiya14 ga watan October Jaridar Aminiya ta fitarda wani rubutuna game da Maza 'yan Luwadi.

Kusan karfe 10 na dare wani bawan Allah ya kirani, daga daukan wayan na san hankalinsa a tashe yake muryarsa na karkarwa. Ya shaidamin yana 'daya daga cikin masu neman Maza kuma kusan Shekarar sai 15 yana wannan lalata yanzu kuma kusan shekarar sa 10 da aure amma har yanzu ya kasa dainawa.
Yace min hakika babu yanda baiyi ba domin ganin ya bar wannan muguwar 'dabi'ah amma ya kasa.
Bayan gama wayar da shi tare da gama bashi shawarori akan ya tuba ya kuma kauracewa wayanda suke wannan ta'adi.

Cen kusan karfe 12 na dare wani ya kirani ya shaidamin daga wata jami'ah (dake arewa ) yake kira na, ya shaidamin yanda aka sanya shi wannan muguwar 'dabi'ah ta luwadi (Wa'Iyazubillah).
Ya gaya min Cewa, wani ne ya sanya shi wannan muguwar 'dabi'ah ta hanyar nuna masa ya zo su rika yin Romace ba tare da sun sadu ba. Wannan yafi yaje yayi zina.

Ya gayamin a hakan ya amince domin a tunaninsa Romac ba komai ba ne, ya gayamin a cikin Romace din ne kawai wata rana ya afka masa yayi masa luwadi.

Ya shaidamin hakika yanzu baya sha'awar macce, Sai dai maza, yace min wani lokaci har kashisa yake dauka ya shafa a al'aurarsa idan wannan sha'awar ta taso masa (Wa'Iyazubillahi).
Yan da kyau 'Yan Uwa mu rika Kula da Suwa Qannenmu da 'ya'yanmu da Abokananmu ke mu'amula domin gudun yin dana sanin a gaba.

Duk wanda yace maka kazo kuyi romace yafi kaje kayi Zina Wallahi karya yake maka Yana so ne kawai ya halaka maka rayuwa.

Sanan yana da kyau 'yan mata su san cewa, da madigo da Luwadi duka daya ne babu banbanci a wajen Azaba a gobe Qiyama. Sannan yana da kyau su san anya mafi sauri ta kamuwa da cutar Infection Itace ta hanyar yin madigo (lesbian). Su kuma samari su sani daga ranar da aka yi maka luwadi daga ranar Kashi ba zai taba tsayama ba. Daga kaji kashi da yazo.

Sannan masu yi yana da kyau su sani daga ranar da kayi sanadiyar wani fadawa cikin Muguwar 'dabi'ah to kuwa duk lokacin da akayi dashi ko yaje yayi sai an rubuta maka zunubi koda kana Cikin kabari ne.
Wannan Muhimmiyar Sanarwa Ce, Idan ka taimaka wajen Yada ta to ka taimaka wajen ya'da Alheri. Idan kuma ka qi yadawa to ka yi hasarar tarin Ladar da Za'a samu.

Jamilu Sani Rarah Sokoto
Sat 15/10/2015

Tuesday, 29 November 2016

NAZARI AKAN YAWAITAR ZAZZABI (MALERIYA)

HUJEWAR OZONE LAYER YA FARA KAWO ANNOBA A CIKIN AL'UMMA.

Tun Kusan Lokacin da Na samu Labari akan k'aruwar Hujewar OZONE LAYER ( Bargon da ke matsayin kariya tsakanin duniya da kuma cutukkan rana), nake ta tunani akan wannan lamari.
A bangare daya kuma Yawaitar Mace-macen hadi da rashin lafiya da Suke Faruwa a Jahar mu ta Sokoto sai na tsaya nayi nazari tare da Bincike mai zurfi game da Wannan Lamari. Sai naga gaba days an dau wannan matsala kacokan an daurata ga zazzabin Cizon Sauro. Wanda kuwa ga dukkan alamu ba haka lamarin yake ba.

Shi dai Wannan OZONE LAYER masana suka ce abu ne tamkar bargo a sararin saman duniya kuma kariya ne ga (Sama) da kuma Mutane.

Suka kara da Cewa, shi wannan Bargon da ake kira ozone layer, yana shinfide ne a Sararin Samaniya domin ya zama kariya ga halittun kasa daga sinadaran da suke zubowa daga zafin rana wanda zasu cutar da 'dan Adam ta hanyar sanyawa mutane cututtuka (masu wuyar Sha'ani). To idan sinadirai masu cutarwa suka zubo sai su makale a jikin wannan Bargon na Ozone layer.

Babu Shakka Wannan Zance na Masana Ilmin Kimiya ba karya bane game da Wannan Bargon.
Domin tun Kusan Shekaru 1400 da suka Gabata Al-qur'ani Mai Girma ya gaya mana labarin wannan Bargon da ke Sama.A Cikin Al-qur'ani Mai Girma Allah (Swt) Yana Cewa, 

ﻭَﺟَﻌَﻠْﻨَﺎ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﺀَ ﺳَﻘْﻔًﺎ ﻣَّﺤْﻔُﻮﻇًﺎ ۖ ﻭَﻫُﻢْ ﻋَﻦْ ﺁﻳَﺎﺗِﻬَﺎ ﻣُﻌْﺮِﺿُﻮﻥَ

MA'ANA, "Kuma Mun sanya sama rufi tsararre, alhali kuwa su daga ayoyinta masu bijirewa ne" (Suratul Anbiya aya ta 31). Sannan a Wata Ayar kuma Allah (Swt) Yana Cewa,

ﻭَﺍﻟﺴَّﻘْﻒِ ﺍﻟْﻤَﺮْﻓُﻮﻉِ


MA'ANA, "Da rufin nan da aka ɗaukaka." (Suratu At-Tur aya ta)
.
A Wani Wuri Kuma Allah (Swt) ya gaya mana Cewa, Wannan bargo kariya ne ga Mazauna kasa.

ﻗَﺪْ ﻣَﻜَﺮَ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦ ﻗَﺒْﻠِﻬِﻢْ ﻓَﺄَﺗَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺑُﻨْﻴَﺎﻧَﻬُﻢ ﻣِّﻦَ ﺍﻟْﻘَﻮَﺍﻋِﺪِ ﻓَﺨَﺮَّ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢُ ﺍﻟﺴَّﻘْﻒُ ﻣِﻦ ﻓَﻮْﻗِﻬِﻢْ ﻭَﺃَﺗَﺎﻫُﻢُ ﺍﻟْﻌَﺬَﺍﺏُ ﻣِﻦْ ﺣَﻴْﺚُ ﻟَﺎ ﻳَﺸْﻌُﺮُﻭﻥَ

MA'ANA "Lalle ne waɗanda suke a gabaninsu sun yi makirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsa-shensa, sai rufi ya faɗa a kansu daga bisansu, kuma azaba ta je musu daga inda ba su sani ba." (Suratul An-Nahl aya ta 26).

Friedrich Schonbein Shine mutunen da ya gano Ozone a shekarar 1839, In da a Shekarar 1840 Gordon Miller ya gano amfanin wannan bargo na Ozone layer. Shi dai wannan bargon ya fara hujewa tun kusan shekarun 1980 inda wannan hujewar ta rika fadada tun daga wancan lokaci har zuwa yanzu, in da a wannan shekarar ta 2016 aka gano wannan bargon yayi qatuwar hujewa.

Masana dai sun riga sun fadi Cewa, Wannan hujewar ta kan iya haifar da kafewar manya da kananan koguna, da kuma karuwar yawan ruwan da ke cikin manyan kogunan
wannan duniya.

Haka Kuma Sun fadi Cewa, Wannan hujewar barazana ce ga lafiyar 'yan Adam din dake rayuwa a wannan duniya musamman sassan duniyar dake fama da yanayin zafin rana. Domin ana samun karin sabbin cututtukan da suke da alaka da fata masu Wuyar magani.

Wannan abu hakika ya fara tabbatuwa domin kuwa a watan juli din wannan shekara ta 2016 (Wato July 2006), a North America an samu mutuwar a kalla mutane 225. Wanda kuma duka bincike ya tabbatar da cewa, dukansu sun samu cutukkane ta dalilin yawan zafin rana.

Haka Wannan Annoba ta mace-mace da rashin lafiya ta yawaita a Wani kauye dake Cikin Erteria In da kusan Sai da 'yan kauyen Suka yanke kauna da rayuwa. Kwatsam kuma Sai gashi Wannan Annoba ta Rashin Lafiya da Mace-mace Sun yawaita a Cikin Tsakiyar Garin Sokoto In da a Rana 'daya zakaji an Rasa fiye da Mutum 50. Babu Shakka Annoba Jarabawa Ce Da Allah Ke yiwa Bayinsa Ko dai don Ya Jarabesu ko Kuma don Gargadesu akan Su tuba daga miyagun laifuka.

....Subhanallah!!!
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Wed 26/10/2016